NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 14

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*


*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*


*Wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ki yayata SUMAYYA MUKHTAR RABO (mrs Al-ameen) ina godiya da karfafa min gwiwa Allah ya bar zumunci*

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
               *14*

Yau kusan satina ɗaya a gidan Adda saratu rayuwa nake mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali babu wani abu da ke damun xuciyata, sbd Adda saratu mace ce mai kirki babu wani abu mara daɗi da take min ta ɗauke ni tamkar yar da ta haifa a cikinta, sai dai abu ɗaya da ke damuna shi ne yawan tunanin innata da nake yi a halin yanzu, sbd ban san halin da take ciki ba, tunda Adda saratu da kanta taje gidan namu don shaida mata cewa ina wajenta, sai aka ce mata an koreta daga gidan, ga rashin masoyina da aminiyata wanda ban san halin da suka kasance ba bayan tafiyata, ban san lokacin da zan daina kewarsu ba.

Tsaye nake a kitchen ina mayar da kwanukan da na wanke, Adda saratu ce ta shigo “Sa’adatu anya kina so mu yi tafiyar nan kuwa, ki kalli agogo har ƙarfe ɗaya saura tayi” da sauri na duba agogon da ke nanne a kitchen din “ayya ban kula lokaci ya tafi haka ba bari nayi sauri na ƙarasa abinda nake tunda nayi wanka baxa mu bata lokaci ba” sauri nayi kammala abinda nake yi, har ga xuciyata bana son tafiyar nan saboda kada wani daga cikin ahalin gidanmu ya ganni ya fadawa Babana inda nake, amma tunda ta nuna min muhimmancin tafiyar sai na yarda , saboda xamu je ne mu duba inda inna take da kuma yanayin da take ciki, na san duk inda take hankalin ta na kaina.

Khadija da zainab  muka bari a gidan kasancewar su yara masu nutsuwa, har mu dawo baxa a samu wata matsala ba.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Kai tsaye gidan kanwar mahaifiyar su innah muka nufa gwaggo Balaraba amma da gwaggo suke kiranta, saboda mun san shi kaɗai ne gidan da xata iya zuwa ta xauna, kasancewar ita kadai ta rage musu duk iyayensu sun ƙare, kuma duk wata matsala ita ce take kashe musu ita.
Da ƙarfin gwiwa nake tafiya na san yau xan ga innata farin cikin rayuwata,  da sauri muka faɗa cikin gidan, gidan bangare-bangare ne, kusan duk ƴaƴanta idan sun tashi aure a gidan suke zama kaɗan ne suke fita waje su yi gini. bangaren gwaggo Balaraba muka nufa sai dai kash!!! Kofarta a kulle, don haka muka shiga wajen danta Abbas, tun daga nesa matarsa ta ganmu ta tarbe mu da farin cikinta, daki ta kaimu ta bamu lemo da abinci lemon kadai muka sha saboda mun ci abinci a gida, sai da muka ɗan taɓa hira take faɗa mana cewa gwaggo sun tafi kauye tare da innata, tambayarta Adda saratu tayi dalilin tafiyar tasu, a nan ta shaida mata cewa sun tafi ne a kan abinda yake faruwa da ni, kasancewar kusan kullum sai Babana ya zo yayi xage-xage a kan innah ta fito masa da ni ko kuma ya kaita ƙara, hakan yasa su tafiya don shaidawa magabatanta.

Tunani da tausayin innah ne ya kamani duk wannan abin ana yi mata ne saboda ni, don haka ya dace na nemo hanyar da zata rabu da wannan baƙin cikin na har abada, sbd tunda innah take a gidanmu lokaci kaɗan take farin ciki ragowar duk bakin ciki take yi, jikinmu babu ƙarfi muka koma gida.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Tunda na koma na shiga daki ina tunani da kuka, wane irin uba Allah ya bani da yake yi min wulakanci yake ƙoƙarin wulakanta mahaifiyata, yana iƙrarin yana sona amma ko kadan babu kaunata a xuciyarsa, tunda ga shi yana neman jefa rayuwata a halaka, gaba daya sha’awar zaman gidanmu ta fita a raina gara naje ko’ina nayi rayuwa a kan na xauna a gidanmu, amma kuma ina tunanin irin cin mutuncin da Babana xai yiwa innata a duk lokacin da ya duba yaga bana tare da shi, ko ina so ko bana so dole na koma indai ina son na samarwa mahaifiyata farin ciki.
Ban san lokacin da hawaye suka riƙa gangarowa daga idanuna ba, ina a wannan halin Adda saratu taxo ta same ni, cikin kulawa take min magana tare da bani hakuri a kan irin jarrabawar da nake fuskanta, ta kuma yi min alkawarin duk rintsi duk wuya baxa ta bari na koma gidanmu ba sai dai duk abinda xai faru ya faru.

*************

Baban Izuddeen ne a zaune gaban yan sanda suna tattaunawa dangane da abinda ake xargin Izuddeen din da shi, saboda yau har yayi sati daya babu wata kwakkwarar magana a kan xa a sake shi ko za a bada belinshi, shi yasa yau ya taso da kansa yaxo don jin inda aka kwana.

Yana zaune Baban Sa’adatu yaxo, da izza da rashin mutunci ya shigo wajen bayan sun gaisa da yan sanda ya mayar da kallonsa ga mahaifin Izuddeen, wani kwarjini da kimarsa ne suka kama shi bai san lokacin da ya zube kasa yana gaishe shi ba, su kansu yan sandan sai da suka yi mamakin hakan, mutumin da ya dau xafi a kan abinda ya faru amma yau shi ne da xubewa kasa yana gaishe da mahaifin wanda ake zargi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Ba tare da bata lokaci ba aka fara magana daga ƙarshe aka cimma matsaya a kan xa a bada belin Izuddeen amma da sharadin nan da sati biyu idan ba a ga Sa’adatu ba za a sake cafke shi, fito da shi aka yi suka tafi gida tare da mahaifinsa.
Yan uwa da abokan Izuddeen ne suka taru don tabarsa kowa na tofa albarkacin bakinsa wasu su ce ya rabu da Sa’adatu tunda ba yar gwal bace, wasu su ce ya cigaba da sonta tunda ita ma tana kaunarsa, sai da ya shiga wanka ya fito sannan ya ci abinci ya shiga wajen iyayensa don ganawa da su.

A cike gidan su Sa’adatu yake da mutanen kauyen bankaura da kuma mutanen jarumawa, duk sun taho ne don jaje da kuma daura auren Sa’adatu wanda mahaifinta ya shaida musu za a daura shi da misalin karfe hudu na rana.

Baka jin komai sai tofin ala tsine da yiwa Sa’adatu habaici, wasu su ce bakin mahaifinta ne ya kamata wasu kuma su ce yawon bariki ta tafi.

Wasu daga cikin matan gidansu ne da waɗanda suka zo daga ƙauye, suka tafi gano dakin amarya don kai mata katifa da kuma shimfida mata leda.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Gida ne karami mai ɗauke da dakuna guda hudu falle d’ai-d’ai ragowar dakuna uku na sauran matansa ne, sai kuma daki daya wanda ya barwa Sa’adatu, kyan gidan zaman mace daya a hakan ma zata takura musamman idan tana da ya’ya, amma mata uku ne da kusan yaya ashirin da biyar suke rayuwa a cikin gidan kowane yaro a dakin mahaifiyarsa yake kwana, shi hoton naka ma ba shi da daki sai rabe-rabe da yake a dakin matansa, duk matar da take da kwana sai dai yaranta su kwana a shago shi kuma ya kwana a dakin, gaba ɗaya gidan yayi musu kaɗan rayuwar takura kawai suke yi, shi yasa gidan ba tsafta duk a jike ga tarin tsummokaran yara.

Sallama suka yi tare da tambayar matan gidan dakin amarya a yatsine suka amsa tare da mika musu mukullin dakin, daga gefe dakin Sa’adatu yake, sai kuma kitchen na langa-langa da yayi mata, shi kaɗai ne dakin da aka yiwa farar kasa sai faman jirwaye take alamar dakin ya dade bai ga fenti ba, kyauran dakin da tagar duk na katako ne, sai ka xura kafarka sosai sannan xaka iya shiga dakin idan baka yi da gaske ba xaka iya fasa baki, duk flastar da ke dakin ta cinye haka dai aka samu aka yi farar kasar ba tsiya ba arziki, ceiling din dakin ma na kwali ne banda uban duhu babu komai, kasancewar dakin tsohon daki ne ya dade a gine kuma daga lungu yake. A gaggauce suka shimfida ledar tare da jingine tsohuwar katifar da aka siya mata a gidan wata dillaliya, fitowa suka yi ko arxikin labule dakin bai samu ba. Sai rike baki suke suna mamakin irin wannan gida, duk macewar gidansu ya fi wannan kyau.

Tunda suka dawo suke dariya an yi wa Sa’adatu auren mugunta, sai maganganu marasa dad’i suke fada.
A fusace salim ya fito daga daki yana masifa, wajen yan uwan mahaifin nasu ya nufa “indai kuna ganin mugunta ku ka yiwa Sa’adatu insha Allah kanku xai koma, kuma ko ni kadai na ishi auren nan indai ina doron kasa Sa’adatu baxa ta auri almajiri ba” yana cikin wannan maganar malam Salisu ya fito daga dakinsa, dukansa ya fara yi kamar ya samu karamin yaro, hakan yasa salim ya bar cikin gidan tare da alƙawarin baxai sake dawowa ba indai wannan xaluncin za a cigaba da yi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ƙarfe hudu dai-dai aka taru don daura auren Sa’adatu da malam Jibo ango ya sha tsohuwar farar shaddarsa wacce ta ji jiki kamar an kwatota daga bakin kura, sanye yake da jar Dara takalmin kafarsa baƙi ya saka, duk inda ya bi sai zundensa ake yi wai tsabar son xuciya shi xai auri Sa’adatu, mutane da yawa sun san auren cuta za a yi mata kuma laifin mahaifinta suke gani, a kan tabarmar da aka baxa a kofar gidan su ya xauna yana jiran fitowar sauran waliyyan Sa’adatu, don bashi aurenta.

*Kada a manta da comment da sharing*


*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button