NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 4

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*


*Gaisuwa mai tarin yawa gare ki yar tsohuwa mai ran ƙarfe kakata ta kaina abokiyar fadana, Zainab ummu Affan marubuciyar littafin MAJANEEN & SADEEQAT ina godiya da abin alheri Allah ya bar min ke ko ba kai ba kafa ko dan naci dariya????*

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
*HALIMATU USMAN BAKORI naji sakonki na gode da kauna da kulawar da kike bawa wannan littafi kuma insha Allah zan riƙa kokarin yi muku page biyu a rana*


*4*


Washe gari da safe na tambayi innah ina son xuwa gidan kanwarta Adda saratu sbd a nan kusa da mu take kuma na dade ban ziyarce ta ba,  kasancewar Baba baya barina na fita, maganganun su innah salamatu sun fara yi masa tasiri, wannan yasa yake saka min takunkumi sai wajen da ya yarda nake zuwa.

Sai da na gama shiryawa tsaf na fito tsakar gida, tarar da innah nayi zaune a kofar daki tana gyara shinkafa, a ladabce nace “innah na fito ko kina da sakon da zaki bayar a kai mata?” Murmushi innah tayi. “Ba ni da wani sako Sa’adatu abinda zan ce miki kawai ki kula da kanki kuma kada kiyi dare, kinga dai irin rayuwar da muke yi ki gaishe min da ita da kyau, alewar kwakwa ta miko min, karbi wannan ki kaiwa yaran nawa.
Sallama muka yi na fita a soro naci karo da zaliha wani kallon wulakanci tayi min a haka dai za a ƙare kullum a tafe an rasa mashinshini, ban saurareta ba sbd baxa tayi min haushi na rama ba.

Cikin nutsuwa nake tafiyata, har na isa gidan Adda saratu sallama nayi na shiga gidan, yaran ta na tarar suna wasa a tsakar gida suna jin muryata suka taho da gudu suka rungume ni, “sannu da zuwa Aunty Sa’adatu, kin manta da mu” karɓar kayan da ke hannuna suka yi muka shiga cikin dakin Adda saratu, bamu tarar da ita a ciki ba kasancewar ta shiga wanka.

Ruwa da lemo suka dakko min sannan muka fara hirar zumunci tare da su duk da cewa ƙanan yara ne amma suna da hankali da nutsuwa basu fiye shirme irin na yara ba, sbd Adda saratu mace ce mai nutsuwa da iya tarbiyya shi yasa ya’yanta suka fita daban a cikin yara.

“Wata sabon gani yau kece a gidan namu” da sauri na waiwaya Adda saratu ce ta fito daga wanka, da sauri na ƙarasa muka rungume juna muna farin cikin haduwa da junanmu, waje ta samu ta zauna “yau kece a gidan namu, nayi mamakin ganinki don kin jima rabonki da mu, shi yasa nima nayi fushi na daina zuwa babu ke babu innah”

Murmushi nayi wlh Adda makaranta ce ta boye ni, kin san na kusa haɗa haddata shi yasa bana samun lokacin ziyara”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
“Ayya shi yasa bana ganinki to Allah ya taimaka Allah yasa ta tsoron Allah ce, ai kuwa nima sai na hada miki walima ‘ya guda ta haddace Alkur’ani ai dole mu nuna godiya ga Allah” tambaya ta jefo min.

“Sa’adatu har Yanzu ba wani labari ne?”

Murmushi nayi da akwai Adda amma Akwai yan matsalolin da ba a rasa ba, labarin Izuddeen na bata da irin matsalar da nake fuskanta a gidanmu addu’a ta yi min kan Allah ya kare ni daga sharrinsu.

Haka muka cigaba da hira har zuwa yammaci sannan na tashi don tafiya gida, kayanta ta hado min kowanne da mayafinsa, saboda ta lura da irin kayan da suke jikina duk sun mutu, kusan kala goma ta bani, godiya nayi mata sannan na tashi na tafi.

A kofar gida naci karo da Baba, wani kallo yake min wanda ya sanya gabana faduwa a cikin xuciyata na fada “Allah yasa dai ba wani laifin aka ce nayi ba”

A sanyaye na tsugunna na gaishe shi amma sai naga ya kawar da kansa gefe, sake maimaita gaisuwar nayi a zatona ko ji ne bai yi ba, sai naga ya wuce ya barni a tsugunne.
Jikina babu ƙarfi na tashi na shiga gida a tsakar gida na tarar da innah tana alwalar sallar magariba.

A damuwar da ta ganni yasa ta saurin tambayata. “Lafiya Sa’adatu me ya same ki na ganki a haka”

Ban fada mata ba Saboda bana so ta shiga damuwa ga shi ita kanta ba wani koshin lafiya gareta ba, “bana jin dadi ne innah ji nake kamar marata xata yi ciwo” cikin tausaya wa ta dube ni “Allah ya baki lafiya amma yana da kyau kije daki ki dauki maganinki sbd bana so ciwon nan ya tasar miki da ƙarfi” to nace na wuce daki.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Shigowa tayi ta same ni, na hada kai da gwiwa “kin dai sha maganin ko, wai ni anya ma kuwa ciwon nan kike yi ba wani abu ne ya same ki ba?” amsa mata nayi da “shi ne innah babu wani abu da ke damuna”
Kayan da aka bani na mika mata “innah kinga kayan da Adda saratu ta bani” cikin farin ciki ta fara bude kayan “kai madalla mun godewa sarai ita dai bata gajiya da yiwa zumunci hidima Allah ya saka mata da alheri”
Cikin shagwaba nace
“Kema ki duba ki zabi wanda xai miki dai-dai innah”

“A’a Sa’adatu ki saka ai kece budurwa kin fini buƙatar kayan kwalliya, kuma ni wannan ɗinkin na yara ne ya xan yi da shi, ke dai ki saka ita kuma Allah ya biyata da aljannah”
Muna cikin maganar naga Baba ya leko kwalawa innah kira ya fara yi, ita kanta tayi mamakin kiran da yake mata don rabon da ya kirata har ta manta, da sauri ta tashi ta fita. Ni kuwa xuciyata kamar ta tsaga kirjina ta fito saboda fargaba nasan da kyar ne idan kiran ba nawa bane.

“Ina kika je yanxu don naga kwana biyu dabi’un ki sun fara canjawa ba irin yadda na sanki da kike ba”
Kafin nayi magana har na fara kuka wannan yasa na kasa yin magana saboda baƙin ciki, wato dai ta tabbata zargina Baba yake yi. 
Kafin nayi magana ya wanke ni da mari “baxa ki fada min inda kika je ba sai na ci mutuncinki ko? Innah ce ta bashi amsa “Ba wani guri taje ba malam gidan sarai taje, sbd ta dade bata ziyarce ta ba”

Dakatar da innah yayi “kada na sake jin kin min magana sbd kece munafukar da kike goya mata bayan duk abinda take yi, sbd ana shigo miki da leda ko, duk abinda yake faruwa ina ji kuma labari yana zuwar min, an fada min har yaron da yake lalata ta har gidan nan yake xuwa, to wlh duk randa na sake ganinsa sai ransa ya baci Allah yasa na sake ganin ƙafarsa a gidan nan”

Dakawa innah tsawa yayi. “Maza dakko min ledar da ta shigo da ita haramiyarku” da sauri innah ta shiga daki ta kawo masa ledar kayan da Adda saratu ta bani, kiran innah salamatu yayi, cikin hanzari ta fito tana dariyar mugunta. 
“Gani malam”

“Ina su zaliha” cikin kissa da makirci irin nata ta amsa da “suna daki”
Kirasu su zo su kwashe kayan nan, da murnarta ta kwala musu kira kamar jiran a kirasu suke yi suka fito a guje, kayana baba ya miƙa musu ku karba ku je ku saka, ke kuma xaki gamu da ni.

Ficewa yayi ya barmu a tsaye ni da innah, su innah salamatu da ƴaƴanta sai dariya suke mana tare da yi mana habaici.

A salube muka shiga daki gaba ɗaya na kasa daina kuka, sbd na gaza gane irin wannan kiyayar da Baba yake mana, wani lokacin shi da kansa yake bada kofar da xa a ci min mutunci, nasihohi innah ta rika yi min tare da kwantar min da hankali cewa komai mai wucewa ne.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Washe gari Baba bai fita ko ina ba sbd yana ta dakon xuwan Izuddeen, tunda dama sun riga da sun fada masa yau xai dawo, cikin ikon Allah sai kuma ranar bai zo ba, ban san uzurin da ya tsare shi ba kasancewar ba ni da waya, addu’a na riƙa yi Allah yasa dai ba su ne suka hargitsa min shirina ba don yanzu zuciyata ta fara kaunarsa Musamman da naga yadda yan gidanmu suka so su ya nema ba ni ba.

Gaskiya rashin comment dinku Yana karya min gwiwa shi yake hana ni typing da yawa


*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button