NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 5

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
           *NA*
*Jeeddah Tijjani*
       *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

*Wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ka ABDUL RAHMAN IBRAHIM admin Hafsat Hausa novels Facebook ina godiya da ƙoƙarin da kake yi wajen ganin littafin nan ya yadu ko’ina a duniya*




              *5*
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Washe gari ma shiru bai zo ba, tun daga lokacin hankalina ya tashi kewarshi nake yi sosai kamar mun dade da shi, tambayar kaina na shiga yi, anya ba baba ne yaje ya dakatar da shi ba kuwa, tunda mutanen gidan mu sun fada masa karya da gaskiya kuma sun san gidan da yake, ko kuma wani abu aka je aka fada masa a kaina, tambayoyin da na riƙa yi wa kaina kenan wanda na kasa samun amsar su, kasa hakuri nayi na tambayi innah ina son zuwa wajen Rukayya saboda nasan a wajenta ne kadai xan samu amsar tambayoyina.
Gidansu Rukayya na nufa amma cikin rashin Sa’a sai na tarar da gidan a kulle basa nan. Raina bai min dad’i ba naso samunta mun tattauna a kan matsalar dawowa gida nayi da sauri kafin Baba ya fuskanci bana nan, addu’a na shiga yi Allah yasa alkhairi ne ya boye shi ba akasinsa ba.

*WACECE SA’ADATU*

Malam Salisu Abubakar shi ne sunan Mahaifina, muna zaune ne a garin kano cikin unguwa uku da ke kano, mahaifina ɗan kasuwa ne sai dai ba wani babban ɗan kasuwa ba, yana da rufin asiri dai-dai gwargwado, mun fi karfin ci da sha. Gidanmu irin babban gida ne family house kasancewar kakanmu malam Abubakar shi ne mai unguwar unguwa uku don haka duk yayansa shi yake yanka musu fili, wannan yasa muka kasance a dunkule a gida daya, mahaifina shi ne babban dansa, sai kannensa guda shida biyu maza huɗu mata dukkan matan suna aure a Kano, ragowar mazan ne muke gida ɗaya da su. Mahaifina yana da mata biyu, innah salamatu ita ce uwar gida tana da ya’ya tawas biyar maza uku mata, salisu, Hamza, Yusuf, Ibrahim, Musa, Aisha, zaliha, zainab. Ta aurar da ya’ya mazanta gaba daya sai kuma zainab wacce tun kafin mu yi wayo aka aurar da ita, wato A’isha da zaliha ne suka rage bata aurar da su ba wanda suka kasance kanne a gare ni.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Innata Maryam ita ce amarya wacce na kasance yarta daya tilo kasancewar duk ya’yan da innah take haifa mutuwa suke yi ni kadaice na tsaya, shikenan kuma tun daga kaina bata sake haihuwa ba.

Tare muke da kannen Babana da matayensu amma ɓangaren kowa daban, Baba Sani shi yake bin mahaifina wanda kuma shi ne mahaifin ya salim yana da ya’ya biyar biyu maxa uku mata an aurar da mata biyu saliha ce kaɗai ta rage ba a aurar da ita ba. Sai kuma Baba Umar wanda ya kasance dan autansu shi ma ya’yansa biyar shi kuma duka maza ne.
A farkon zamantakewar gidanmu kan su innah da ragowar matan a haɗe yake babu wata matsala da ke tsakanin su, daga baya innah salamatu ta canja rayuwar gidan gaba daya da gulma da munafunci, aka hadewa innata kai muka zama abin tsangwama, babu laifin tsaye babu na zaune.

Back to story

A ɓangaren Izuddeen kuwa tunda ya koma gida yake fama da matsanancin ciwon kai, yayi ƙoƙarin zuwa yaga Sa’adatunsa amma hakan ya gagara sbd ko kofar gida baya iya fitowa sai dai abokansa su shigo su taya shi hira, ba karamin damuwa ya shiga na rashin ganin abin kaunarsa ba, ga shi ko waya bai bata ba ballantana ya kira yaji muryarta.

Yau dai ya ɗan ji ƙarfi a jikinsa wanka yayi ya sanya farin yadinsa mai kyau, kayan ya karbi jikinsa kasancewar Izuddeen mutum ne ma’abocin son fararen kaya, cikin gidan su ya shiga don gaida mahaifansa, kai tsaye dakin Hajiya Amina (mama) ya shiga kishiyar mahaifiyarsa wadda ta kasance ita ce amarya kuma uwar dakinsa, tun lokacin da taxo gidan Izuddeen ya zamto dan dakinta, komai nasa a wajenta yake baxa ka taɓa cewa ba ita ta haife shi ba, Kasancewar kan iyayensu a haɗe yake komai tare suke yi baka gane tsakanin su.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});   Da farin ciki ta karɓe shi “sannu da xuwa dana na kaina lallai jiki yayi sauki” guri ya nema ya zauna cikin ladabi ya gaisheta, amsa masa tayi tana mai tashi ta kawo masa kayan karin kumallo, bayan ya gama ci sun ɗan taɓa yar hira, sannan ya gyara zama “mama ina da magana da ke” da yake da sunan da yake kiranta kenan, hankalinta ta bashi ina “jinka dana na kaina”

Sunkuyar da kansa yayi “Dama mama fada miki zan yi na samo miki suruka” farin ciki ne ya bayyana a fuskar ta “Alhamdulillah Allah ya nufa nima xan ɗauki jikokina a hannu, ya sunan surukar tamu kuma a ina take”

Kansa a sunkuye yake magana “sunanta Sa’adatu a nan kusa da mu take”
Mamaki ne ya kamata “Izuddeen dama a nan kusa akwai yarinyar da zata burgeka gaskiya nayi matuƙar mamaki” 
Murmushi yayi “Dama lokacina ne bai yi ba mama shi yasa kika riƙa fama da ni a kan na samo mata to yanzu dai na samo na huta” murmushi suka yi gaba daya, fatan alkhairi tayi, “insha Allah yau xan gayawa malam, na san ba ƙaramin dadi xai ji ba” kujera ya nema ya kwanta.

****************

Innah salamatu ce zaune a bakin Kofar dakinmu yau saboda tsabar raini da tsokana yau a Kofar dakinmu take bushe masara, tana busar tana habaici abinda na lura da shi a habaicin nata, da akwai abinda yake shirin faruwa da ni, ni dai addu’a nake Allah ya kare mu daga dukkan sharrinsu ni da innata.

Sallamar Rukayya ce ta katse min tunanina da sauri na amsa mata lekowa nayi sbd baxan iya wucewa ba tunda innah salamatu ta tare bakin kofar da kayanta. gaisheta tayi amma bata amsa mata ba, sai ma bin ta da tayi da wani matsiyacin kallo, bata kula da ita ba ta cigaba da magana da ni. “innah innarmu” amsa mata nayi tare da harararta “Ba a sani ba jiya ina ta nemanki kika kulle gida kika tafi” murmushi tayi “unguwa muka je ni da umma shi yasa baki ganni ba, ina innarmu nace miki?” “Bata nan taje unguwa”

Hijabi na dakko tare da mika mata allona nace ta riƙe min kasancewar idan na fito da shi da kaina xan iya buge innah salamatu, ko samun kulle dakin ban yi ba sbd tare kofar da tayi.
Wucewa muka yi muka makaranta. Muna barin kofar gidan mu abinda na fara tambayar Rukayya shi ne “ina Izuddeen kin ji wani labari daga gare shi” kallon saroro tayi min “ban gane ina Izuddeen ba ke da masoyinki ke xan tambaya inda yake”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Rausayar da kaina nayi kamar xan yi kuka “tunda ya tafi bai sake dawowa ba dalilin da yasa naje gidanku nemanki kenan sbd hankalina ya tashi kwarai da gaske, kinga ranar da yaxo na tarar da su innah salamatu da yayanta har yayan wajensu ya salim sun kasa kunne suna jin tattaunawar da muka yi da shi, da Baba ya dawo sai suka juya min zance suka ce wai ɗan iskana na kawo shi ne Baba yace zai je ya dakatar da shi kada ya sake zuwar masa gida”

Cikin tausayawa ta dube ni “kai amma mutanen nan an yi munafukai azzalumai, ta Allah ba tasu ba idan ina jin matsalolin gidanku sai na riƙa ji kamar a film, me yasa su innah salamatu suke haka na rasa dalilin wannan kiyayyar, ki kwantar da hankalin ki idan Izuddeen rabonki ne duk rintsi duk wuya sai ya aureki, matar Mutum kabarinsa wannan hassadar da suke miki baxa tasa kiyi ƙasa ba da yardar Allah sai kin fi ƴaƴansu komai”

Har muka isa makaranta tattaunawar da muke yi kenan, don ko damar karatu bamu samu ba muna ta kullawa muna kwancewa, wani yaro na gani tsaye a kaina ɗaya daga cikin almajiran makarantar mu, “kixo inji malam jibo” kallon mamaki na hau yi masa a zuciyata na riƙa cewa kiran me malam jibo yake min, Rukayya ce tayi saurin cewa kace “Bata nan” dakatar da ita nayi “ki bari naje naji kiran kika sani ko maganar haddarta ce” har na miƙe ta zaunar da ni “wlh ba inda zaki je idan hadda ce ai da kansa yake xuwa, kika sani ko kararki Baba ya kawo, haka kawai ki kai kanki inda za a rika jibgarki kamar jaka”
Komawa nayi na zauna ‘Haka ne kuma Rukayya ni na manta da hakan ma sai da kika tuna min, ban san sharrin da aka kulla min ba” sake dawowa yaron yayi “Yace idan baki zo ba zai zo da kansa”
Jikina na rawa na tashi na tafi, a cikin rumfar da yake karatu na tarar da shi zaune a kan buzunsa yana karanta Kur’ani, ga dogon carbi a gabansa, sallama nayi da fara’a ya amsa min, nayi mamakin karbar da yayi min kasancewar shi mutum ne ba mai yawan sakin fuska ba musamman ga dalibansa.
Cikin ladabi nace “Gani malam”
Murmushi yayi “Babanki bai fada miki komai ba?” kaina a sunkuye nace bai fada min ba, a xuciyata nace me Baba xai fada min haka? Katse min tunanina yayi da gyaran muryar da yayi, kallonsa nayi yana min murmushi tare da gyara hularsa. “to!! to!! to!! Tashi zai faɗa miki don jiya yazo nan ya same ni da wata magana ina fatan xaki bani hadin kai, amma nafi so dai kiji komai daga bakinsa”
Jikina a sanyaye na tashi har na fita yana bi na da wani kallo da ni kaina ban san fassararsa ba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Wajen Rukayya na koma hankalina a tashe, tana ganina ta miƙe dafa kafadata tayi “lafiya naga walwalarki ta canja kawata faɗa min abinda ke damunki”

Kwashe labarin yadda muka yi da malam Jibo nayi na fada mata, tunda Rukayya ta sunkuya bata dago ba ban san me ya hana ta dago bata kalleni ba.


Jiya naji dadin comment dinku mutanena na group din DUKKAN TSANANI fans da JEEDDAH TIJJANI NOVEL mutanena na facebook ina gode muku ina jin dadin comment dinku Allah ya bar zumunci


08094136204



*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button