NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 9

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)**Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

   

              *9*


*Yau shafin gaba daya na baku shi kyauta ku yi yadda kuke so da shi saboda dadin comment dinku da naji Maryam Amatullah (maman kausar) da Ramcy k Aleeyu*Gari na wayewa na tafi gidan su Rukayya tunda ta ganni da sassafe haka ta san ba kalau ba, tana ganina ta miƙe tana tambayata “kada dai kice wani abin ne ya sake faruwa Sa’adatu” 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); cikin kuka nake bata labarin zuwan Izuddeen da labarin batan wayar da ya bani, tayi bakin cikin batar wayar sosai, ummansu ce ta bani kudi muka siyo alewa tace mu kai makaranta a yi sadaka a roki Allah ya bayyanata, malamin ƙananan yara na samu na bawa na fada masa a kan bukatar da nake so a yi min addu’a Allah ya bayyana barawon da ya saci wayar, tun kafin na bar gurin aka sa yaran suka fara hasbunallahu abinka da yara sun ga alawa sai ƙara bada himma suke sosai.

Mun juya xamu tafi kenan naji an kirani ban amsa ba sai da na juya don naga mai kirana, malam Jibo ne ya leko da kansa daga rumfar da yake karatu, nuni yayi min da hannu naxo, kallon Rukayya nayi tare da cewa “kixo ki raka ni” kafewa tayi a kan baxa tayi min rakiya ba, kuma nima baxan je ba, ganin yadda ya kafe ta da ido ne yasa ta sake ni naje kiran.

Raina a haɗe naje yau ba irin tsugunnon da na saba nayi masa ba, a takaice nace ina “kwana”
Yana murmushinsa mai cike da ban haushi ya amsa.
Ina gama gaishe shi na miƙe na juya baya zan tafi ya kira sunana “sauri kike haka ne Sa’adatu daga gaisuwa sai tafiya, me yasa yau baku zo makaranta ba, naga kwana biyun nan kuna wasa da hadda bakwa bada himma irin da” a gintse nace “ina da abin yi ne shi yasa” 
Ina gama magana na fita ina ji yana kirana nayi banxa da shi na tafi.

Ko da na dawo babu Rukayya babu dalilinta da alama fushi tayi shi yasa ta tafi ta kyale ni, a hanya naci karo da ita ta rabe jikin wani gini tana jirana, bi na tayi da harara duk maganar da nayi mata bata amsa ba sai can tayi min magana cikin fada “wlh duk kece kike bawa mutumin nan kofar da zai raina ki me xai hada ki magana da shi, kawai don ya kiraki sai ki bi shi kamar wata jela, idan bakya saurarsa ko shi ne shugaban marasa zuciya dole ya hakura ya kyale ki, wannan sanyin naki idan baki daina shi ba bazai haifar miki da ɗa mai ido ba, idan baki ɗauki mataki ba ke zai zo addaba ba ni ba, shawara nake baki tun wuri kiyi maganinsa don naga ke kamar ta ruwan sanyi kike binsa” 
Mayar da ajiyar zuciya nayi ina nazarin maganganunta wanda suke da tasiri a gare ni, shiru nayi har muka kusan zuwa gida tana min faɗa. komawa gidansu muka yi muka sanar da umma cewa mun bayar har an fara addu’a.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
**************

Yau Izuddeen a makare ya tashi tun bayan da yayi sallar asuba ya kwanta ba shi ya farka ba sai wajen sha biyu saura. Saboda jikinsa ba ƙarfi zafin abinda Baban Sa’adatu yayi masa ne yake taɓa xuciyarsa, shi yasa ya zabi yayi ta bacci ko xuciyarsa xata yi sanyi, a hankali ya mike daga shimfidarsa banɗaki ya shiga yayi brush ya dan watsa ruwa, bayan ya fito ya fesa turare kala-kala masu daɗin kamshi saboda shi ma’abocin tsafta ne da son kamshi shi yasa bai fiye fesa turare kala ɗaya ba, sanya farar jallabiya yayi, sai da ya kulle dakinsa sannan ya nufi hanyar shiga gida don ya gaisa da mahaifansa, tunda yau tun safe basu ji motsinsa ba zasu iya shiga damuwa idan basu ganshi ba musamman Mama da yake dan lelenta.

A bakin kofa ya ci karo da wata mata wacce baxai iya tantance ko wace ce ita ba, sai dai abinda ya bashi mamaki ganin kwalin wayar da ya kaiwa Sa’adatu jiya a hannunta, tambayar kansa ya shiga yi “me kuma ya haɗa wannan matar da kwalin wayar Sa’adatu, ko dai ita ce mahaifiyarta, idan kuwa haka ne ya san duk shirinsa sai an tarwatsa masa, don ya fuskanci kamar iyayen Sa’adatun basa son alakar shi da ita”

kai tsaye yaga ta shiga cikin gidansu wannan ya tabbatar masa da cewa tuntuni dama ta san gidan, don bata tsaya tambayarsa hanyar da xata sadata da wajen iyayensu ba, kasancewar gidan su Izuddeen babban gida ne ɓangaren kowa daban.

Ɓangaren mama yaga ta nufa, dalilin da yaja hankalinsa kenan ya bi bayanta saboda ya san kowace ce daga gidan su Sa’adatu aka turo ta.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Ganin ta shiga dakin mama ne yasa ya dawo da baya tunda ko menene indai maganar ta shafe shi sai yaji, dakinsa ya koma ya zauna ya cigaba da latsa wayarsa yana Game kamar yadda ya saba.
Da sallama ta shiga dakin a zaune ta tarar da mama saboda a lokacin ta idar da sallar walha tana addu’a, sai da ta shafa sannan ta juyo gareta da karamci ta karɓe ta gami da yi mata sannu da zuwa, cikin farin ciki ta amsa.
Bayan sun gama gaisawa mama ta mayar da kallonta gareta da cewa “kiyi hakuri Hajiya ban wanye da ke ba, da yake jama’ar tamu da yawa”
Sunkuyar da kai kasa tayi sannan ta fara magana “La ba komai Hajiya ai komai sai da dalili, Ni sunana Hajiya salamatu a nan makotanku muke, nice matar malam Salisu”
Murmushi Mama tayi “Ayya sai kuma da kika yi bayani na gane ki, kin san an dade ba a hadu ba”

“Wlh kam haduwa tayi wuya kin san da yake komai sai Allah ya nufa” Bayan sun gama gaisuwar yaushe gamo ta kalli mama
jin daɗin yadda tace ta gane ta ne yasa ta saki jikinta ta fara bayani.
“Dama na zo ne a kan Maganar danku Izuddeen da yaje neman auran yarmu” cikin farin ciki tace “Oh Allah sarki kwarai kuwa ya faɗa min da har muna shirin aikowa ma kwanan nan tunda ya gama karatu me ake jira sai aure kawai”
Rausayar da kai innah salamatu tayi “Hmm da kin san Abinda Ya kawo ni da baki fadi haka ba”
Cikin rashin fahimtar abinda take faɗa ta dubeta, “Ban fahince ki ba Hajiya wani abin ne ya faru” jinjina kai tayi kwarai kuwa hakan ne ma yasa mahaifinta yace na taso da kaina na faɗa muku abinda ke faruwa don ku kula”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Gyara xama mama tayi, a zuciyarta addu’a take Allah yasa dai ba wata maganar Izuddeen ya dakko musu ba, duk da cewa ta san ɗan nata kamili ne ba a taɓa kama shi da wani laifi ba, amma ta san sharrin zuciya ba tada Kashi ko ita ce, ta ja shi ya aikata laifi, jefa mata tambaya mama tayi “wani abin Izuddeen dina yayi”
Jinjina kai innah salamatu tayi “A’a babu abinda yayi amma mun zo mu ankarar da ku ne, yarinyar da yake nema ‘yata ce amma ba ni ce mahaifiyarta ba, amma ni nake rukonta duk halinta na sani yarinyar ba tada dabi’u masu kyau, an zubar mata da ciki ya kai sau biyar, jiya yaron yazo xance mahaifinta da kansa ya kamata tana ƙoƙarin lalata shi, kinga fitina tun tana karama ake maganinta shi yasa Babanta da kansa yace naxo na faɗa muku ku katange danku ku raba ta da shi tun kafin ta lalata masa kuruciya, saboda bai kamata a ce gida kamar wannan da ku ka yi shuhura a arxiki da ilimi a ce an auro muku mara tarbiyya ba, kinga abu bai yi kyau ba kenan” tunda ta fara fada mata wannan maganar mama ta kasa magana duk hankalinta ya tashi, yanxu a ce duk tarbiyyar da suka bawa Izuddeen sakayyar da xai musu kenan.
Miƙa mata ledar wayar da ya bawa Sa’adatu jiya tayi ” kinga Babbar shaida ko, don kada ma ki zaci ko sharri aka yi musu, jin dadin abinda tayi masa ne yasa yake bata kyautuka daban-daban, amma kada kiga laifin danki domin janye hankalinsa tayi har ya biye mata kuma kin san dai yadda mace take da tasiri ga da namiji, duk girmansa duk iliminsa duk abinda yake ji da shi cikin ƙananan mintuna zata gama da tunaninsa, shawara ki jawo danki a jiki ki nema masa yarinya ta mutunci ,ko mu a nan gidan namu idan yana so akwai yan mata kyawawa masu tarbiyya sai yaxo ya nemi wata” tana gama fadin Abinda Ya kawota ta mike. 
Duk gwiwoyin mama sun yi sanyi ta kasa magana ji take kamar ƙasa baxa ta dauke ta ba, tunda suke neman aure basu taɓa cin karo da matsala irin wannan ba sai a kan Izuddeen, sun aurar da yaya sama da sha Biyar amma babu wadda aka taɓa zuwa har gida aka fadi aibunta sai ta Izuddeen.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Sallama innah salamatu tayi mata, cike da farin ciki ta bar gidan, har mama ta kama hanyar shiga dakin Izuddeen ta fasa saboda maganganun da aka faɗa mata suna buƙatar nazari
dakinta ta koma ta kwanta rigingine idanunta sun yi ja saboda ɓacin rai, ta fahimci a maganganun innah salamatu akwai karya amma kuma wani abin gaskiya ta faɗa, tunda ga shaidar waya ta nuna, sai dai abinda ya bata tsoro a maganarta da tace idan yana bukatar aure yaje ya nema a gidan su, ta fuskanci kamar wata manakisar ake shirin kullawa yarinyar, sai dai har Yanzu ta kasa amincewa ɗari bisa ɗari cewa ba lalata suke da Izuddeen ba duk da cewa ta san halin danta amma ba a shedar dan yau.
Tunani ta rika yi a kan ta samu mahaifinsa ta faɗa masa ko kuma ta fara tunkarar Izuddeen da maganar saboda bata so ta bata masa suna a idon yan uwansa.

*******
A Hanyar mu ta komawa gida muka ci karo da innah Salamatu bin mu tayi da wani matsiyacin kallo, sannu da zuwa muka yi mata amma ko yan kallo bamu isheta ba, a soro suka ci karo da Baba shi ma sannu da zuwa yayi mata tare da cewa “Har kin dawo da wuri haka kin mayar musu da wayar su dai ko” kallon kallo muka rika yi ni da Rukayya dama su suka ɗauki wayar? 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Cikin kissa tace “naje mun gama magana da su sun yarda da dukkan abinda na fada musu kuma sun ce xasu katange dansu” tana gama faɗa ta juyo kaina tana bi na da kallo mai cike da tsana.

Da gudu na shiga gida na fada dakin innah ina kuka “innah tashi kiji ashe innah salamatu ce ta sace min wayar nan mayar gidan su Izuddeen, sannan ta fadi karya da gaskiya a kaina, na shiga uku innah me matar nan take nufi da ni” A gigice innah ta tashi sai a lokacin na lura da bacci take, innalillahi wa inna ilaihi raji’un naji tana maimaitawa “ALLAH kayi mana maganin abinda ya fi karfinmu” kuka mai cin rai nake yi ita ma Rukayya haka, innah sai faman rarrashi take yi tana janyo mana hadisai da ayoyi masu magana a  kan hakuri da yarda da kaddara da kyar ta samu kanmu muka yi shiru.


Kada a manta a yi sharing yan uwa su karanta
*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button