NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 10

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*


*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*


              *10*

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Tun lokacin da innah salamatu ta je gidan su Izuddeen Mama bata ƙara samun kwanciyar hankali ba kullum a cikin tunanin yadda zata bullowa al’amarin take yi, ga shi ta kasa fadawa kowa kuma ta kasa tunkarar Izuddeen da maganar, ita kaɗai ta bar abin a ranta yana yi mata yawo, saboda har yanzu hankalinta ya kasa kwanciya a kan gaskiya ta faɗa mata ko akasin haka.
Yau dai ta yanke shawarar faɗa masa ko zata ji sanyi a ranta, tashi tayi da kanta ta nufi dakinsa, sai dai tayi rashin Sa’a baya nan dakin nasa a kulle, dawowa cikin gida tayi sannan ta ɗauki waya ta kira shi cewa tana kiransa da gaggawa.

Yayi nisa da gida amma haka ya daure ya juyo saboda yadda mama ta jaddada masa cewa tana son ganinsa da gaggawa. Gabansa ne ya riƙa faduwa Allah yasa dai alkhairi ne yasa ta kira shi don tunda suke bata taɓa yi masa irin wannan kiran ba.

A daki ya sameta tayi tagumi tana tunani, har yayi sallama bata san ya shigo ba sai a karo na biyu da ya sake yi sannan ta san da shigowarsa, cike da mamaki ya karasa wajenta tare da xama a ƙaramar kujerar da ke gefenta, fuskarsa bayyane da damuwa”mama lafiya yau na ganki a irin wannan halin me yake damunki? tunda nake ban taɓa ganin damuwa a bayyane a fuskar ki ba irin yau, ga shi kuma naga kina min kiran gaggawa Allah yasa dai lafiya”
Mayar da ajiyar zuciya tayi.
 “Zan iya cewa lafiya amma ba lafiya ba, amma muna fatan Allah ya tabbatar da lafiyar zuwa nan gaba, Allah ya kawo mafita ya nuna mana gaskiya a kan tunanin da muke yi” 
Cikin kulawa ya amsa da “Ameen amma ban fahimci maganganun ki ba Mama”.
Murmushi tayi “zaka fahimta ne ɗana ka bari xan faɗa maka komai”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Shiru suka yi na wani dan lokaci sannan tace.
“Abinda yasa na kiraka matsala ce dangane da kai kuma ina so ta xama sirri tsakanina da kai, don bana so kowa yaji abinda ke tsakanin mu, amma kuma ina rokonka ka fada min gaskiyar abinda ka sani kada ka munafunce ni”
Jikin Izuddeen ne ya dau rawa “wani abin aka ce nayi mama” jinjina kai tayi “Baka yi komai ba amma dai ana zargin ka aikata, don haka ka kwantar da hankalinka ba wani abin damuwa bane”

Gabansa ne yake ta dukan uku-uku jira kawai yake ya ji abinda zata fada, “ina saurarenki mama wlh na kosa naji laifin da nayi miki”

“Dama daga gidansu yarinyar da kake nema ne…….” gabansa ne ya yanke ya fadi dama tunda yaga matar nan da wayar da ya bawa Sa’adatu a hannunta ya san wani abin ne ya kawo ta addu’a yake yi a zuciyarsa Allah yasa dai ba cewa aka yi an raba shi da ita ba, da sauri yace
 “wani abin aka ce nayi mama?”
Dakatar da shi tayi “A’a ka tsaya ka saurare ni mana” hankalin shi ya bata gaba ɗaya yana saurarenta.

“Ta zo ta faɗa min cewa yarinyar da kake nema ba yarinyar kirki bace, bin maxa take sanadiyyar hakan ta xubar da ciki ba adadi, Sannan kaima kuma tana ƙoƙarin janye hankalinka kuna lalata da juna saboda daɗin abinda take maka ne yasa ka bata kyautar waya ka ganta nan ma a hannuna”

Miƙa masa wayar tayi ya gani sannan ta mayar da ita gefenta sannan ta cigaba da magana. “wannan dalilin yasa taxo da kanta ta sanar mana gudun kada mu yi kitso da kwarkwata” kafin ta kammala fada idanun Izuddeen yayi jawur kamar zai yi kuka, yanzu Sa’adatun tasa nutsatstsiyar yarinya kamila za a jefa da wannan kalmar, yarinyar da bata san komai ba sama da ibada da xuwa makaranta, bai san lokacin da ya sawa mama kuka ba.
 “wlh Mama duk abubuwan nan da ake fada sharri aka yi min, kuma ita ma yarinyar sharri aka yi mata, Sa’adatun da take kamila za a jefa da wannan kalmar sannan nima a yi min sharri, wlh ban yafewa matar nan ba Allah ya bi min hakkina, don ta zubar min da mutuncina a idonki” cike da kulawa ta fara yi masa magana 

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); “Ni fa dama ban yarda da abinda take fada ba kawai dai na ji ta ne, sbd har cewa tayi kaje ka nemi ɗaya daga cikin ƴaƴanta kaga ya tabbata auren yarinyar ne bata so shi yasa taxo ta kulla wannan sharrin, dalilin da yasa na same ka kenan na fada maka yadda muka yi da ita, don mu warware bakin xaren kaga bai kamata na yanke hukunci a bisa rashin sani ba, nice mahaifiyar ka Izuddeen nafi kowa sanin halinka, gaba daya ban yarda da abinda ta fada min ba, ka kwantar da hankalinka xan fadawa babanka a je a bincika a tabbatar da gaskiyar abinda take fada”

Izuddeen ya dade a xaune bai tashi ba yana kukan takaicin jifansa da aka yi da zina, shi da ko hannun mace bai taɓa tabawa ba shi xa a yiwa kazafin zina, ya ji xafin abinda matar nan tayi masa kuma ya dauri aniyar duk lokacin da ya gano ko wace ce ita, sai ya ɗauki matakin Shari’a a kanta.

Bayan ya tashi daga dakin Mama gidan su Rukayya ya wuce, yaro ya aika ya kirata a tsakar gida ya sameta tana tankade, cike da nutsuwa yaron ya fada mata cewa ana sallama da ita,tayi mamakin jin ana sallama da ita saboda ta san mai sonta baya nan da yake ba a gari yake aiki ba, kuma indai zai zo sai ya sanar mata.

Hijabinta ta saka tare da leka kanta dakin umma “umma ana kirana a kofar gida zan leka naji mai kirana” amsa min tayi da to
Leka kainta tayi kafin ta fita, hango Izuddeen tayi jingine da machine dinsa, yana ganinta ya taho da sauri da ganinsa yaƙe yake don ga damuwa nan bayyane a fuskarsa.
Cikin sakin fuska ta karɓe shi tare da cewa.
“yau kuma an tuna da ni kenan xiyara aka kawo min” a gintse ya amsa mata da “eh ai girmanki ne ranki ya dade” shigo da shi soro tayi tare da cewa “bari na samo maka abin zama” bai musa mata ba ta shiga gida ta dakko masa farar kujera ajiye masa tayi sannan ta nemi gefe ta zauna tana fuskantar sa.
yadda taga fuskarsa ba walwala ne yasa ta fahimci yana cikin damuwa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Sun ɗauki lokaci mai dan tsawo kafin kowa yace da dan uwansa wani abu, ita ce tayi ƙarfin halin yin magana.
“Daga wajen kawar tawa kake ne ka biyo ka gaishe ni” ta ƙarasa maganar tana ɗan murmushi.
Ajiyar zuciya yayi tare da cewa “Daga gida nake na shigo  wajenki ne don ki ɗan ƙara min haske game da abinda yake damuna” cikin mamaki tace
 “to!!! Me kuma ya faru da kai mijin kawata?” Kafin ya faɗa mata abinda ya faru idanunsa sun yi ja kamar zai yi hawaye, sai da zuciyarsa ta ɗan yi sanyi sannan ya kwashe dukkan abinda ya gudana tsakaninsa da Mama ya faɗa mata.
Tunda ta ji inda maganar ta dosa ta gano makircin innah salamatu ne, don sun ji lokacin da take fadawa Baba dawowar ta daga gidan su Izuddeen.

Girgiza kai kawai Rukayya take yi ta rasa bakin magana sai can tace “bazan boye maka dukkan irin rayuwar da Sa’adatu take yi a gidan su ba, xan iya cewa rayuwa ce irin ta tatsuniyar yar mowa da yar bora, tsananin tsana da kiyayya kishiyar mahaifiyarta da yayanta suke mata wacce ba tada asali ballantana toshe, kuma ita ce taje gidanku ta kulla wannan sharrin, hatta abinda Baban Sa’adatu yayi maka ranar da kaje wajenta duk da sa hannunta, na san ka fahimci abubuwa da yawa a ɗan xuwan da kake yi, xaka san cewa Sa’adatu da mahaifiyarta rayuwar hakuri suke yi, kada kayi mamakin dukkan abinda zasu faɗa a kanta zasu iya fadin abinda ya fi haka ma, tunda babu soyayyarta a zuciyarsu da suna da hali da tuni sun koreta daga gidan ita da mahaifiyarta, fatana a gare ka shi ne ka bincika komai kafin ka yanke hukunci, na san ba kai tsaye kaxo kace kana son Sa’adatu ba sai da ka binciki dabiunta kafin kace kana sonta, ka kwantar da hankalin ka a kan abinda aka faɗa maka, kayi naxari sosai kafin ka yanke hukunci”
 numfashi mai zafi Izuddeen ya fitar daga bakinsa “nima ba cewa nayi na yarda ba kawai naxo na tambaye ki ne sbd abin ya daure min kai na san wannan duk ba halinta bane, kuma ba Sa’adatu kadai abin ya taɓa ba har da ni, tunda gashi nima tace min  lalata nake yi da ita, sauki ɗaya na samu da iyayena suka kasance mutane masu nazari da tunani, da wasu ne da tuni ba wannan zancen ake yi ba, amma xan bincika iyayena ma xasu taya ni mu gano bakin xaren, bana so bikinmu ya dauki wani lokaci saboda mu yi maganin makiyan mu” 

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Rukayya taji dadin maganganun Izuddeen musamman da yace ya yarda da kawarta, kuma za su yi aure nan ba da jimawa ba, sun ɗan yi hira kadan sannan ya tashi ya tafi.

bata iya shiga gida ba gidan su Sa’adatu ta zarce, a soro na biyu ta tarar da taron mutane kanta ta tambaya ko me yake faruwa a gidan haka, danna kanta tayi cikin gidan tare da cire takalminta kasancewar baxa ta iya wucewa da takalmi ba saboda shimfidar da aka yi.

Wata magana ta ji ana yi wacce ta daki kunneta kamar saukar aradu taji an fadi wani abu, da sauri ta juyo ta tsaya gefe don sauraren abinda suke tattaunawa, kamar daga sama taji an ce…………….Yawan comment yawan typing kada a manta da sharing*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button