NOVELSUncategorized

EL BASHEER 1-5

*EL-BASHEER* 

1-5
*****Kwance yake kan daya daga cikin kujerun parlon nasa, a yadda yake kwancen zaka tabbatar da shidin dogo ne domin kujerar ma ta masa kadan kawai ya kwanta ne, fuskar sa a
matukar hade take babu alamar Annuri a tare dashi, wata irin qasumba ce ya tara tamkar shugaban en daba sam babu wani gyara, idonsa na kallon sama Alamar tunani ya tafi hakan zai nuna hasken fararen idanun sa tass tamkar madara, dukda ya tara kasumba hakan bazai hana a gane tsananin kyawun da Allah yyi masa ba, saidai idan kayi masa kallon tsanaki zaka hango yadda farar fatarsa tayi duhu, yyinda wata er rama kadan ta bayyana a gareshi *EL-BASHEER USMAN TAFIDA*  shine cikakken sunan sa, dan zakutawa yyi daga kwanciyar da yake ya lumshe idonsa kamar me bcci.

Sakkowar su kenan daga bene wani matashi da be kai el-bash ba yace,

 “haj amma fa kina fama da kato a gida,” 

 wacce aka kira da haj ta tabe baki tace, 

 “ni wlh lamarin sa ma ya fara isata babu biyan bukata sai aikin wahala ni wannan *HAUKA* ta isheni nayi kokari ma da muke kwana da *MAHAUKACI* a gida daya wlh,” 

 matashin yayi dariya yace, 

“Sannu fa haj gsky na yadda komai ma waje yake samu, shi da gidan ubansa kice kin gaji? 

Haj ta bata rai tace,

“Toh yimin gori sale sai nasan bani da gado da gidan dan rainin hankali.”


Sale yana rike dariyar sa yace,

“Maida wukar hajjaju ai gadon ma gaba1 naki ne yyinda kika aika shi lahira shi da tsohon ubansa.” 

“Haj ta washe baki tana tafi tace yanzu ka dawo hanya qanina salele”

Sale yace,


“Kefa wani lkcin Yaya suwaiba kinada Wulakanci meye kuma salele? Sai kace sillen kara”


Haj ta rufe bakinta dan tasan ta tabo inda bayaso tace,

“toh naji na daina Sale.

Sale yana tabe baki dan be gama hucewa ba yace,

 “har yanzu baki samo solution bane?

 Haj tace,

 “kai Sale sau nawa zan maka mgnr? Na rasa inda ya boye takardun nan wlh ai da tuni mun aika shi,”

 sale ya fara yin hanyar fita yace, 

 “ya kamata duk inda ya ajiye takrdun nan a samo shi dan wlh bazan kashe kudi a banza ba kin sani sarai gadon mu aka siyar dan kawai mu samu biyan bukata amma har yanzu shiru.” 


 haj ta bishi wajen suna karasa mgn tace,

 “dadina dakai sale baka da hakuri, kana gani dai mahaifin sa baya kasar bare mu samu wani abin, shi kuma da muka *HAUKATAR* dashi mun duba ko’ina bamu samu takardu ba, gashi duk accnt dinsa a kulle bare mu kwasa dole sai da sanin sa,”

 nisawa sale yyi yace, 

 “ni kinga tafiya ta saina dawo.” 

 haj tace, 

 “to shikenan nan itama ta juya.” 


~
 karar fashewar abubuwa ta fara ji a parlon, lekawa tayi ta window nan ta hango el-bash duk yyiwa parlon upside down, kujerar da yake kai ya juyata, haka sauran kujerun ma, komai dai ya hargitse, wani wawan tsaki haj taja kafin ta koma bangaren ta, dama bangaren nasa sukaje sukayi bincike ko Allah zaisa suga takardun da suke nema.


*
Wata irin wawiyar parking tayi a parking lot, sanye take da wani irin dinki da yyi matukar kama ta, duk wata sura ta jikinta ana gani idonta toshe yake da wani katon glass daya cika mata ido, kas-kas take tauna chewing gum dinta, yyinda take taku dai-dai kan takalmin ta me matukar tsini, *Sakina* kenan ‘yar gidan haj Suwaiba kuma a matsayin Agola a gidan Alhj Usman, A sangarece ta karasa parlon tana hura chewing gum irin na rikakkun en bariki ba tare da tayi sallama ba ta zauna akan kujera hade da dora kafa daya kandaya. Haj suwaiba dake parlon ta juye tana kallon yarinyar tata tace,

 “sakina har kun tashi lecture?”

 Sakina ta tabe baki tace,

 “wlh momy na gaji skul saikace dole.” 

momy tace, 

 “dan ubanki idan bakiyi karatun ba dame zamuyi kudi? Kina gani dai yadda nake fama na sama mana dukiya duk dan sbd kiyi Alfahari Amma na kula ke bakida hankali sai kace tinkiya,” 

sakina tace, 

 “momy da wannan wahalar da kike ku aura min shi mana,” 

 momy tace, 

 “shi wa?” 

 Sakina batare da damuwa ba tace, 

“El-bash.” 

A razane momy ta dago tana kallon sakina tace, 


 “kina da hankali kuwa? *MAHAUKACIN* zaki aura? kai amma anyi gantalalliyar yarinya wlh, duk samarinki ki rasa wanda zaki so sai shi?” 


 Sakina tace, 

 “oh momy calm down da wasa nake ni me zanyi dashi? Haba wuce nan” 

 sai a lkcin momy suwaiba ta sauke ajiyar zuciya tace, 

 “haba yanzu naji sanyi a raina amma da kina nema ki samin hawan jini.” 

 Dariya sakina tayi tana me tashi dan tafiya dakinta.

~~
Tana shiga daki ta kira kawarta zee, 

“sakna ya dai hop momy ta amince?” 

Sakina tace, 

“yaushe zata amince min? Daga mgn bakiga yadda ta wani gigice ba sai nace mata da wasa nake ina tunanin zamuje plan B kin sanni sarai idan na kwadaita da mutum sai inda karfina ya kare.”

Zee tace,

 “wannan haka yake badan yana hauka bama ai gwarzon namiji za’ayi anan. 

Sakina ta lumshe ido tace, 

Bari tunamin zee inaji kamar nayi tsuntsuwa naje gareshi, wlh ina matukar kwadayin sa, ba hauka ba koma me yake wlh saina dandana shi.

Zee ta kwashe da dariya tace, 

 ” ina yinki sakna big gal zanso naga yadda zaki kaya da mahaukaci.


Sakina tayi murmushi tace,

 “kedai bari zan gwada sa’a ta.”

Zee tace Duk yadda ake ciki just hala me. 

Sakna tace no p. 

Nan dai suka katse wayar.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button