NOVELSUncategorized

KWARATA RETURN 10

???? —— 10

       Shafin nan daga farkon shi har can² karshenshi. Sadaukarwa ne gareku “ya “ya masu albarka.
*ABDULRAHMAN B ‘ K LAWAL*
                   &
*JA’AFAR B ‘ K LAWAL*

Ina roƙar Allah subahanahu wata’ala da ya albarkaci rayuwarku. Ya jiɓanci lamurranku ya jiƙanku ya ɗaukaku darajarku yasa ku gama da duniya lafiya. Ina roƙon ubangiji da yasa kuyi kyakkyawan ƙarshe. Allah ya dafa muku ya kareku da kariyarSa , ya tsareku da tsaronSa a duk inda kuka shiga yasa albarka a rayuwarku ya ƙulle idanuwa da zuciyoyin duk wani gurɓatacce daga gareku. Allah yasa ku dace a gidan duniya da ƙiyama. Allah yai muku albarka don darajar fiyayyen halitta Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam. Ameen ya Allah. Duk mai san manzan Allah S. A. W yace amin….. Duk wanda yace amin , ya Allah kasa ya gama da iyayenshi lafiya. Idan kuma sun rigamu gidan gaskiya Allah ka jiƙansu ka sadasu da rahmar ka , kasa can ya fiye musu nan har Babana…. Allah kasa sun huta. Mu kuma ka kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo Amin.

          Idanuwa na cike da hawaye nace ai dama ba fita zanyi ba haƙuri zan baka. Na ƙarasa maganar ina ƙoƙarin durƙusawa ƙasa. Tausasa murya nayi cike da ladabi na furta kayi haƙuri insha Allah bazan sake ba. Komawa yayi ya zauna danshi yana da karyayyar zuciya , ko yana furta sai na kasheki………. Saina kashe² idan dai zanyi kuka ko yaga na ɓata rai zaice An mata bakijin magana kaza². Da lallausar murya ya furta gaskiya banji daɗi ba. Kuma karki sakemin irin haka daga yau…? Nace tom. Duk abinda ni nawa ne ? Idan dai har nine na siyoshi da hannuna koma miye ko mene ne ko wane iri ne karki kurkusa ki yanke hukunci ba izinina na faɗa miki. Na sake cewa tom. Ni kwanaki da zan aske ya nuna gemunshi ba kuka kikayi ba ? Shiru nayi ina kallon ƙasa kamar mijin da matanshi suka ritsa a ɗakin “yar aiki.

       Ke me yasa kikayi kuka ? Cewa kikayi in rufa miki asiri ko ni ina so idan kika ga masu gemu kiyi ta kallonsu ne ? Cikin ɗaga murya yace tou da irin wannan dalilin da zaisa ki kalli wani mai gemun a waje , tou nima irin wannan dalilin ne yasa na siyo rigar nan. Ko an faɗa miki niba mutum bane ba ? Ance miki ni nawa idon bai iya kallon mata ba ? Ko an faɗa miki ni banajin irin yadda kike ji ? Ko an faɗa miki niɗin dutse ne ni da banajin yanayi a jikina iye ? Ya faɗa yana nuna kanshi da ɗan yatsa. Tou irin abinda kikeji idan kika kalleni da yanayin da kikaji idan kika shafa fuskata ko kika zo kika rumgumeni , duk irin yanayin da kikeji idan kina shashshafa ko ina a jikina ni nafiki na wuce na zarce ki jin irin wannan yanayin. Ko sai ke kaɗai kike so a burge ki ? Wannan ai rashin adalci ne, zalinci ne. Ji nakeyi kamar ince miki ban yafe ba. Fashewa nayi da kuka nace Allah ya isa zakayi min ne ? Cikin ɗaga murya yace dan in nuna miki girma da ciwon da naji wallahi akan bayar da rigar nan da kikayi ? Yau da kin sameni akan tsini duk wanda ya tsaya miki da sai nasa kin anso rigunan nan…. Cikin shashshekar kuka nace dan ci baya ? Kece kika ci baya mai shiga haƙƙi miji. Har wasu banzaye sunfi mijinki mutunci , “yan gidan namu ne banzaye ? Suɗin , duk wacce kika gani a cikinsu idan ta dafe kan mijinta shiru zakiji. Irinki ne masu duhun tunani mutane ke rabawa da miji. Kila ma kin basu labarin ni na siyo sai su ɗauka , ke baki iya sakawa su bara su riƙa sakowa suna burgeshi , kina can kwance kina yarinta za’a buga wasan a barki da hauka. Idan ma kika ɓatamin rai na hasala da yawa duk shegiyar dana sake gani a gidan nan saina bata kashin bala’e. Me yasa nake baki kuɗi ? Dan kiyi rayuwarki karki shigamin rayuwa kije kiyi huɗɗarki da mutanenki ko na hanaki ? Ko nace karkiyi ? Ban takura miki ba ban shiga rayuwarki ba An mata , na barki kiyi sabgar gabanki dan kema ki zama mai “yan ci kamar yadda ko wane ɗa yake da “yanci , amma kin ɗaukeni kamar wani lusari ko an faɗa miki tsoro yasa na barki kike abunda kika ga dama ne ? Bana san na matsa miki ne ke kanki idan na takura miki rayuwar gidan nan bata miki daɗi. Nawa ne ba naki ba.

    Ko kayanki ne ba nawa ba iye ? Ke kika siyo su ne ? Nine na gani ya burge na siyo domin ki , ki saka nima inji shauƙi inje irin yanayin da kike shiga idan kika kwanta jikina , ke wai bakya gane komai ? Komai sai an fito ɓaro² an fallasa miki saboda kina da jakin kwalwa. Da kinga na fara sauke²n kaya baki da zama lafiya. Kar in bada miki wannan , kina so kiga na saka wannan , ke wannan yana miki kyau. Ko nace bana sanshi sakani gaba kike kitaimin kuka ke mai idon fitar da hawaye. Shin yanzu ke ba da kanki kike fidda kayan dake baki ra’ayinsu nawa ki bada su ? Duk yadda nake san abu idan kika ce baki sanshi dole haƙuri nakeyi dashi. Duk yadda bana san abu idan kika cemin kina so haƙuri nakeyi. Sanyaya murya yayi yace duk dai dan in burgeki. Amma da yake baki da adalci babu abinda ya dameki inyi farin ciki ko kishirya haka. Ki burgeni ko karki burge kedai kanki kika sani burinki in miki kiji daɗi. Wannan shine rayuwar farin ciki…..? Ya ƙarasa faɗa yana kaiwa katifa duka , baki da adalci sam² kullum baki da burin burgeni saidai neman hanyar musgunamin. Tou daga yau tunda iskanci ne abun naki na rantse da girman Allah kika sake ɓatamin rai saina lalata miki fata…. Tom. Zazzaro ido yayi yace karki cemin tom akan komai kice bazaki ƙara ba………. Ya faɗa yana rufe idanuwanshi. Da sauri nace bazan ƙara ba insha Allah. Hanya ya nunamin in fitar mishi daga ɗaki. Da sauri na fice na barshi yana ta mita…..

     Tsaye take a kitchen tasha ado kamar zataje gasar wanka sai fitar da wani irin sirrintaccen ƙamshi takeyi. A gabanta kuwa kiret in kwai ne take ta dandaƙa ba sassauci. A gefenta kuma “yar matsadiyar wayarta iphone ce keta rero waƙoƙin turanci ita kuma tana rakiyarsu da bakinta. Wata irin zundumemiyar ashariya Yazeed ya ciko bakinshi da ita ya zundumawa Jiddah dake ta farfasa kwayaye……. Wandon jikinshi kuwa sai riƙonshi yake a hannu yana ƙoƙarin ɗaure belt dan wandon ya tsaya. Kuturmar dumadu…..? Kwan zaki cinye dan uwarki…… ? Waye yace miki anacin ganyen filawar da aka jera dan ƙawata ƙawar gida ? Cike da masifa Jiddah tace kai kaima dan uwarka ! Ko an faɗa maka shiru² tsoro ne wai iye ? Idan baka so inci kwai kawai ka bani sakina inyi gaba ai muma a gidan namu anacin kwan. Cike da ɓacin rai Yazeed yace kin taɓa ganin majiyyaci a maƙabarta ? Ai asibiti shine majiyyaci yake zuwa dan ganin likita , shine zai dubashi ya gano ciwonshi ya bashi magani sai ya samu waraka da izinin Allah. Maƙabarta kuwa gidane na matacci , wannan gida da kika ganshi nahir jinyace daga gareni idan kuwa har kika fita a gidan nan gawarki ce aka fidda. Ni bana aure dan saki saidai inci uwar fatar mace tai iskanci. Aurena yana nan ram² baya girgiza no saki an no barkono yaja yaji da bakinshi. Ni nan da kika ganni matakin iskanci na taka bansan iyakar nahiyoyin rashin kunyar dana ƙyetara ba. Ɗan iska ne ni na nunawa a satilayit banda mutunci ga muni banda kyau ko nai wanka….. Da ke a tunaninki na aureki domin kisan wuta ? Nine ma zaki kashe wuta dani ? Tou yanzu na kunnu nayi ta ci gaba da ci daga nan har a tsaida ƙiyama. Bana sanyi bana siƙewa bare kuma kiyi tunanin zan mutu.

1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button