FARHATAL-QALB

FARHATAL-QALB 11

PG:11

  Tunda Marka ta kyallara idanu ita da Inna Sa’adatu akan kaji da yan kayan abincin da Umma Hadiza ta samo a gidan aikinta. Tsangwama, Kyara da tsantsar kiyayyar da suke wa Hadiza da iyalanta suka nunku cikin zukatan su.

Domin Alhamdulillah. Yan sauran canjin da sukayi ragowa awajen Hadizan. Tuni ta auno musu garin kwaki da sukari da kwanon gero. Da kanta takai wa me yar tsala. Zata dinga basu yar tsalan har na tsawon mako 2.

   Gashi duk sanda Umma Hadiza zata dafa abinci daga ragowar kayan abincin da gidan Hajia Hameeda taba su. Sai ta dafa ishasshe ta zubawa Marka. Amman duk kyautatawar da takewa Markan bata gani. Sai dai ta cinye ta lashe ta kuma ture kwano tana mitar kadan aka zuba mata. Sam ba godia bare yabawa ga Umma Hadizan.

Baya ga haka kiyayya ce zazzafa ta sake shiga tsakanin Marka da Waheedah. Tunda akayi taron gwaji da kuma wayar da kai akan cutar amosanin jini ta sickle cell Marka ke jin zafin Waheedah a ranta. Musanman da gwajin Na’Ateeku ya fito da matsala.

Tashi akayi da ruwa tamkar da bakin kwarya. Gari yayi luf luf. Bishiyu se kadawa suke suna bada iska mai dadi.

Yayinda ruwan ya yi gyara masha Allah. Wasu gidajen suka cika da ruwa sai aikin kwalfacewa ake.

Gidan MalamNalado da sauran gidajen dake baki bakin unguwar ta shurah duk sun cika maqil da ruwa.

MalamNalado da kansa ya sharce ruwan dakin Marka da nasa dakin. Yayinda dakin Inna Sa’adatu dana yaranta. Su ukashatu da basher suka tsaya suka kwalfe nasu.

Dakin Umma Hadiza kuwa. Waheedah ce ke kwalfewa gwanin ban tausayi. Sai Najib dake tayata kadan kadan domun jikin nasu ya sake motsowa.

Kamal na dakin su. Umma Hadiza na gefen sa tana masa sannu. Dawowar su kenan daga asibitin cikin unguwa.

Sai numfarfashi yake saki yana dartse hakoran sa hadi da tallabo kafarsa ta hagu yana hawaye .

Marka dake wajen dakali a zaune da rediyo a gefen kunnenta tsaki taja mai tsayi tana tabe baki. Kafin cikin kufulewa tace,

“Wai menene haka? Sai wani uban numfarfashi ka ke jerawa tamkar jemammen sa. “

“Kayi hakuri kayi shiru yayan su.” Umma Hadiza ta shiga lallabar sa.

“Radadi ne a cikin kasusuwanmu, Misali kafa ko hannu ko baya. Idan a kafa ne ciwon ya tashi sai ka ji kamar ana sara kafar ko ana raba ta biyu Marka, Radadi ne mai wahalar fassarawa.” a cewar Najib daya leka kansa wajen Marka

“To uban yan shisshigi da kai na ke?”

“To assalamu alaikum!! Jamaar gidan nan.. wai wai wai. Lalle kuma ruwa ya muku gyara. ” Cewar Najan Isubu data shiga gidan tana kwarara sallama hadi da karewa ruwan dake kwarara a gidan da kallo.

Marka na hango Najan ta sauya fuska. Hadi da juyar da kanta gefe tana kara setin rediyonta. Ai kuwa Najan ta zagaya gefen Markan tana daria

“Hajjaju makkatu.”

“Najaatu.”

“Naam tsohuwa mai ran karfe an buga da ke an bar ki. “

“To ya zaayi da ni.? A haka zaa ganni a bar ni.”

“Wannan zance haka yake. Shakka babu. To kar na cika ki da surutu tare muke da maaikaciyar lapia wadda sukayi gwajin jinin mu.”

“Ni fa banason tsurfa wallahi. Menene kuma iyye? “

“Kai Marka”

“Ah to yo ai gaskia ne. Karairakin su ne na banza da wofi.”

“Dan Allah marka kiyi hakuri kar ta jiyo.”

“Gafara can ni. Babu wanda ya isa yayi mum abunda Allah bemun ba.”

“Hakane. To dai zan shigo da ita yanzu.”

Da sauri Najan ta fita. Nan da nan kuwa sai gashi sun shiga da matar tana biye da ita a baya. Matar suka sbiga gaisawa da Marka da ke yauki kai kace Kashi tagani.

“Fito Hadiza ku koma can. Na tattare nan. Sannu Kamal. Allah ubangiji ya baku lapia.”

Umma Hadiza ta share hawayenta. Hannunta daya ta kamo na Kamal suka koma can dakin da shi su Waheedah sun gama kwarfe ruwan cikin sa.

Nan da nan Najan Isubu ta daure mayafinta a kugu ta shiga kwalfe ruwan tana tsane ko’ina.

Sai data gama tukun sannan ta leka ta kirawo Inna Sa’adatu dake kwance akan gadonta tana hambadar ridi.

“Menene ne ake nema na?” Cewar Inna Sa’adatu dake yauki.

“Abunda nagani kenan, Bayan ke da yaran ki lafiyayyu ne, kinga dakta canne dakin uwar marasa lapian ato.” Marka ta ce da maaikaciyar lapiar hade da miqa hannu ta nuna setin dakin Umma Hadiza.

Maaikaciyar lapiar ta girgiza kai kawaii. Kafin ta shiga cewa,

“Wato shi wannan ciwo fa Hajia abune daya kamata ace kun bada gudunmuwar lokacin ku da karfin ku kai dama aljihun ku akan wadancan yara masu fama da cutar amosanin jini.”

“A saboda me zamu bayar iyye? Bayan shi kansa me sunan malam asirce shi iyayenta sukayi ya aureta. Nan ya tasamun seda na sayar da gonar mahaifin su aka masa auren. Tunda ya aurota kuma gashi nan dansu na farko shanyayye. Ta biyu gatanan kalau akansa amman itama wai seda gilashi take gani. Sai na karshen shima gashi nan a shanye. Baki daya duk abunda mai sunan malam ya mallaka ya kare akan su. Hmm! Wannan yariinya Hadiza wallahi aurota kaddara ne”

“Kash iya kidena cewa haka .. Wato ita wannan cuta, Lokaci mai gajeren zango a dan baya kadan, idan aka yi aure, aka samu juna biyu, aka haihu, bayan kwanaki ko watanni kadan sai kaga yaron ko yarinyar da aka haifa sun mutu, haka ma’auratan zasuyi ta fama da mutuwar ‘ya’yansu, sunata neman magani, je-can, je-can domin samun mafita. Kasuwar bokaye da yan bori sai ta bude, yar-mai-ganye kuwa takan samu wurin baje hajarta a irin wadannan wurare, a karshe abinda za’ace shine, ai matar mayyace, ma’ana ita ce take cinye ‘ya’yanta ta hanyar lashe musu kurwa!

“Sai dai fa, abun ba haka yake ba, “matar ba mayya bace” ba kuma ta “lashe kurwar ‘ya’yanta” Tun farko ba’a tantance kwayar halittar bane, akwai jinsin mutanen da sam bazasu haihu su bayar da da mai nisan kwana ba.Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana dauke da abubuwa iri daban–daban, kamar su kwayoyin halittar jini masu dauke da ruwa (plasma), jar kwayar halitta (Red Blood Cells, RBC), kwayoyin halittar jini masu kula da garkuwar jiki (White Blood Cells, WBCs), kurgun ruwa (Platelets) da sauransu. Iya

“Cutar sikla ko amosanin jini tana faruwa ne idan aka samu matsala a jajayen kwayoyin halittar jini (red blood cells). RBC yana dauke da sinadarin ‘Haemoglobin (Hb) a cikinsa. Haemoglobin (Hb) kala-kala ne; akwai Haemoglobin A (HbA), Haemoglobin B(HbB), Haemoglobin C (HbC), da sauransu. HbA shi ne lafiyayyen haemoglobin. Sauran Hb ɗin ba lafiyayyu bane.

“Cutar sikila tana daya daga cikin cututtukan da ake iya kauce musu kafin samuwarta. Idan kuma cutar ta samu, to tana da wahalar magani.Idan aka ce mutum na dauke da cutar sikila ana nufin mutum yana dauke da sinadaran haemoglobin guda biyu marasa kyau (ba lafiyayyu ba) a jikinsa. Ma’ana dai ya gaji gurbatattun sinadaren haemoglobin daga wurin mahaifiya da mahaifi.A yanzu haka, cutar sikila na daya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jinin AS da AS ko SS da AS….Iya Ina fatan kina ganewa?”.

ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button