FARHATAL-QALB 13
PG:13_
“Hadiza.. Ki kula da yaran nan naki, Domin cutar sikla mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al’umma baki daya…Bazan manta ba, Farfesa Aisha Indo Mamman ta ce har yanzu mutane na da karancin sanin girman cutar sikila. Ta ce mutane sun dogara da camfi da danganta cutar kan aljannu ko maita.Sai dai ta ce ba a warkewa daga wannan cutar ta sikila har abada, illa dai a samu sauki ko kuma a gujewa kamuwa da ita ta hanyar yin
gwajin kwayoyin halitta kafin ayi aure….”
“Likita akance wai ana warkewa?”
“Gaskia abune me kamar wuya. Duk kuwa da Allah shine mai warkarwa, Amma dai, Wadanda suka ce sun warke sau da yawa sun dauki wani mataki ne na dashe bargo, a bisa
fahimtar kimiyya, A medical terms muna cewa da shi bone marrow, Akan dauki bargon dan uwa ko iyaye ko wani makusancin mai fama da cutar sai a dasa masa, kuma daga nan idan aka yi nasara an rabu da cutar kenan.
Sai dai bayan dashen, mai fama da cutar ne kawai zai samu kariya daga amosanin jinin amma za su iya haifar ‘ya’ya masu dauke da wannan cuta ta sikila… Kuma yana da matukar tsada aikin sa don a kasashen waje aka samo usulin sa. Sannan ba kowane yake dace ba idan anyi. Abu ne mai wuyar sha’ani…”
“Gaskia Kam. “
Nan dai maaikaciyar lapiar ta shiga sake budawa Umma Hadiza bayanan komai kafin daga bisani tayi musu sallama ta tafi. Bisa jagorancin Najan Isubu datayi mata rakiya.
===
===
Haka rayuwa ta cigaba da ja. Kwanakin nata shudewa. The Adams family basu waiwayo kano ba sai bayan sati biyu da tafiyar su.
Indo ce ta kira Najan Isubu a waya kan Umma Hadiza ta dawo bakin aikinta washegari.
Hakan kuwa akayi. A daren Najan Isubu taje gidan nasu Umma Hadiza ta sheda mata.
××WASHE–GARI××
Tun asubar fari Umma Hadiza bata runtsa ba. Ta shiga kintsa ko’ina. Ta shiga dakin su Kamal da suma sun farka.
Ta dan tattare wasu abubuwan. Yayinda Waheedah ke jido ruwa a tuqa tuqa tana zubawa a cikin jarkokin su.
Tana gamawa tayo wanka hade da alwala. Bayan tayi sallah ta zauna akan sallaya tana jiran Umman su .
Can sai ga Umman ta su ta lekar da kanta cikin dakin da Waheedah ke a zaune.
“Waheedah je ki karbo yanzu “
“Tohm Umma.”
Ta miqe hade da gyara zaman hijabin jikinta. Ta zura takalmanta ta tafita zuwa gidan yar tsala .
Da ke Allah ya sanyawa mai yar tsalan albarka acikin kasuwancinta. Da wuri take fara tuya. Ita acikin gida daga soro yayinda dan ta namiji ke suyar fanke da wainar kuli awaje.
Mutane uku ne ke agaban Waheedah. Duk dako sammakon da take yi takan samu mutum biyu zuwa uku sun ruga ta a koda yaushe.
Don haka ta shiga soron ta tsugunna daga gefe,
“Ina kwana Jummai?”
“Mun kwan kalau Waheedah? Ya gyatumar taki da su Marka?”
“Duk suna kalau…”
“Inata cewa zan shigo dubiyar su Kamal ban zo ba. Yaya jikin na su?”
“Da sauki Alhamdulillah.”
“To masha Allahu. Allah yakara sauki.”
“Aamin Yaa rabbi.”
Jummai ta cigaba da suyar yar tsala ta gama sallamar sauran tukun sannan ta fara suyar ta su Waheedah.
“Kuna lissafawa ko?”
Waheedah da kanta ke a kàsa tana shata kasa da tsinke ta girgiza kai kafin tace,
“A’ah… Amman de Umma shekaran jia tace ta kusan karewa.”
“Yauwa… Kina ji ko. Daga yau ya zamana sauran karba 2. Kingane ko?”
“Eh.. Nan da kwana biyu kenan ko?”
“Yauwa. Nan da jibi insha Allah da kun karba ta kare.”
“Tohm. Zan gayawa Umman insha Allah.”
“Yauwa.. “
Nan da nan Jummai ta gama suyar yar tsalan su Waheedah. Ta zuba mata a bakaken ledoji guda 5. Kamar ko da yaushe, Ta mika mata. Ita kuma ta saka hannu biyu ta karba ta mata sallama ta fita zuwa gidan su
“Yauwa Umma gashi ” Ta ajiye ledojin agaban Umma Hadiza
“Kin karbo. Sannu Allah yayi albarka “
“Aamin Umma.”
“Gashi kai wa Marka ta ta.”
Da sauri Waheedah ta karbi ledar ta fice zuwa dakin Marka. Bakinta dauke da sallama
“Waye ne?”
“Ni ce Marka .. Ga yar tsalan ta ki “
“Ajiye can.”
“Ina kwana?”
“Lapia.”
Daga haka Waheedah ta tashi daga tsugunnawar da tayi ta koma dakin su jikinta a sanyaye.
“Maza kici ta ki kar tayi sanyi.”
“Tohm.” Taja ledar gabanta. Da kofin ruwan bunun da Umma ta zuba mata. Ta shiga karya yar tsalan tana dangalar kuli kuli tana dannawa a bakin ta. Hade da korawa da ruwan shayi.
Tana karasawa ta yi hamdala. Hadi da ficewa wajen jarka ta kuskuro bakinta. Ta koma daki ta sauya kaya zuwa uniform.
Dan gilashinta ta janyo ta shiga goge shi kafin ta sakala shi a idanunta. Tana mai kallon kanta a mudubin hodar ta.
Cikin haka Umma Hadiza ta shiga dakin itama tanata sauri.
“Yanzu zaki tafi ne ke ma Umma?”
“Eh Waheedah. Kinga sun kira waya tun jia sun fada. Najaatu nata nanatamun dan Allah kar na makara.”
“Hakane. Allah yasa ki fara a saa.”
“Amin Amin Yaa rabbi “
“Umma na ta fi.”
“Tsaya ni mu tafi tare. Yayan ku har ya koma bacci ma. Maganin da likitar nan ta bayar yanada kyau wallahi. Sunce sun fara jin dadin su “
“Alhamdulillah. Allah ya kara musu lapia Amin.”
“Amin…”
Waheedah ta fita zuwa tsakar gidah. Dai dai lokacin da Inna Sa’adatu ta fito daga cikin dakin ta.
“Ina kwana Inna? “
“Da ban kwana ba kya ganni haka?”
“A’ah…” Cewar Waheedah. Tana lankwasa yatsunta. Kafin ta sake cewa,
“Zainab zo mu tafi.”
“Tatafi. Zata tsaya jiran ki ne kina makarar da ita kullum?”
Girgiza kai Waheedah kawai tayi. Ta koma kofar dakin su ta tsaya. Umma Hadiza na sauraron komai. Hijabin ta ta zura. Hade da ficewa daga cikin dakin.
“Muje….”
Waheedah tayi gaba. Yayin da Umma Hadizan ta nufi dakin Marka
“Marka zan tafi wajen aiki. Sai na dawo “
Cikan ki Marka bata ce mata ba. Umma Hadiza ta gaji da tsaiwa ta miqe daga tsugunnawar da tayi.
“Muje Waheedah. “Ta fada tana kakaro murmushi. Don kada Waheedah ta fuskanci tana cikin damuwa.
“Umma kiyi hakuri.”
“Da akayi me Waheedah?”
“Abunda su Marka su k…”
“Ya isa karki karasa. Muyi sauri karki makara. “
Tafiya suka shiga yi da kafafun su. Daga cikin unguwar su ta shurah har ya zuwa cikin titin unguwar gra ta shurah. Wanda yake a matsayin short cut na saurin zuwa makarantar su Waheedah
××NEW GRA SHURAH××
Ba abunda ke tashi sai karar tsuntsaye da kanaru. Shiru unguwar mai dauke da jibga jibgan gidaje na kosassun masu kudi da suka tada kai da arziki.
“Allah ka azurta mu Umma. Dan Allah kalli wani gidah. …”Waheedah ta karasa fada hadi da saka yatsa ta nuna wani jijjigaggen gidah mai matukar kyawu da tsaruwa
“Masha Allah! Ki dinga hadawa da Allah ka azurta mu da wadatar zuciya kinji ko?”
“Tohm Umma.”
“Yauwa.. Allah kuma ya bamu ta hanyar halal ba haram ba.”
“Aamin Yaa rabbi “
Gaba daya sun shagala da kalle kalle. Musanman Waheedah da ke sake da hanci da baki tafiya kawai take
“Ba zaki dago kafa ba sai kin makara ko?”
“Ga ni nan.” Ta shiga sassarfa don cinma Umman da tayi gaba abunta .
Sanye yake cikin kaya tamkar na bacci. Wando daya wuce gwiwa. Da kuma wata riga mai dogon hannu. Sai takalma irin na gudu dinnan. Yayinda kunnuwan sa ke sakale cikin earphones.
Gefen dantsen hannun sa kuma wani madauri ne da robar ruwa aciki. Ya hada gumi sharkaf . Yanata gudu da alama atasaye yake. Motsa jiki/exercise.
Bayan sa kuma wani matashi ne shima yake biye da shi. Sanye cikin irin kayan sa. Amman nasa wandon har kasa yake .
Tsabar kwarewa a gudun da suke. Har Wani juyawa suke suna hira da juna. Acikin juye juyen da yake ne yana magana dana bayan sa.
Garaf yaci karo da Waheedah wadda ke dagawa Umma Hadiza hannu zata shiga gidan aikinta .
Yar jarkar ruwan data dura ruwa aciki ta fadi a kàsa. Hakama gilashin ta daya ballo daga idanunta ya fadi kasa