BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 19

19

………. Ɗagowa yay daga latsa wayar da yake yana kallonta, dan ƙamshin turarenta da takunta ya sanar masa da zuwanta duk da ta kasa magana. Idanunta ta ɗauke daga kallonsa tana faɗin “Good Afternoon”.
           “Ni kike ma gaisuwa kina juyar da fuska?!”.
    Juyowa tai Idanu cike da ƙwalla tana kallonsa. “Ni wlhy Yaya ban san mina maka ba duk kabi ka tsaneni ka takura ni. Komai nayi a duniyar nan a wajenka ban iyaba”. Ta ƙare maganar da sakin siraran hawaye.
         Kallonta kawai yakeyi ko ƙyaftawa babu. Ji tai kallon ya sake saka mata jin haushinsa, juyawa tai da nufin barin wajen…..
     “Kika bar wajen nan sai ranki ya ɓaci”. 
    Idanunta ta rumtse tana jin wasu zafafan hawaye da sukafi na farƙo na neman kufce mata. Ita kam ta rasa mita tsarema bawan ALLAHn nan a duniya, tana fatan watanin nan bakwai da suka rage mata su maza suzo ta kammala abinda ya kawota tabar ƙasar nan, dama tun farko abinda ta gujemawa kenan amma su Mamie suka kasa fahimtarta. Haɗiye hawayen tai batare data barsu sun zubo ba sannan ta juyo garesa, yana a yanda yake har yanzu, sai dai idanunsa masu kwarjini da kaifin dake hana ƙarfin halinta tasiri na nan tsaye kanta ƙyam har yanzu. Kasa jurar kallonsa tai, tai ƙasa da nata, shima sai ya janye nasan, juyawa yay kujerar gefensa ya ɗakko ledar dake ajiye. Miƙa mata yay kansa tsaye.
     Ledar ta fara kalla tare da hanunsa dake ɗaure da agogo da zoben azurfarsa da ya jima yana birgeta, har addu’ar damar sace zoben ta taɓa yi a zuwa na karshe da tai kafin wannan…. Saurin ɗagowa tai tana kallonsa jin ya kamo hanunta cikin nasa, ya wani sake ƙanƙance idanu cike da salon kallon da a duk sanda ya jefeta da shi yake firgitata, ta fara son zame hanun a hankali dan gaba ɗaya lakar jikinta neman daina aiki takeyi, kanta ta fara juya masa tamkar mai ciwon wuya, tana son zare idanunta daga cikin nasa amma yaƙi bata damar hakan nan ma, sai kawai ta sakar masa kukan karya.
    Hanun nata ya saki a hankali bayan ya saka mata ledar, kamar wadda ake control da remote fitt ta ɓace a wajen. Tsabar sauri har tintiɓe tayi ALLAH dai ya taimaketa bata faɗi ba ta dafe gate.
           Murmushi ya saki mai ɗan sauti daga ƙirjinsa yana kauda kansa. Ya maida ƙafafunsa cikin motar tare da rufeta yabar wajen.

Itama koda ta shiga sai da ta samu jikin wata mota ta huta tare da share hawayen ƙaryarta sannan ta buɗe ledar. Shawarma ce da ice-creem sai yogurt da robar ruwa. Haka kawai sai kuma ta samu kanta da sakin murmushi. A fili tace, “Ga rashin mutunci ga kirki idan yaso”. Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da shi dan haka kawai drama ɗin tasu ta yanzu take maimaita kanta a zuciyarta tana saka mata nishaɗi.


Yau kam tayi aniyar kozai daketa bazata yarda tabi motarsa ba, dan haka kawai ragwantakar data nuna ɗazun a gabansa ke hanata sukuni, sai dai murmushi ya kasa barin fuskarta har Yaseer sai da ya kasa haƙuri ya tambaya. Ƴar dariya kawai ta masa batace komai ba. Ana tashi itace farkon fitowa, bata son bin Yaseer ɗin badan tana jin tsoron tabbatar hukuncin Yaya Shareff ba, ba kuma ta buƙatar shiga tasa motar shima gara ta hau napep.

Sai dai kuma cikin rashin sa’a tana fitowa taci karo da motar tasa a wajen gate, kuka kawai ya rage ta fasa ta huta, tai tsaye ta kasa matsawa ga motar har tsahon wasu sakani. Sauke glass ɗin da dariyar Khaleel ta sata sakin ajiyar zuciya, dan tunda ta fito idonsa a kanta. “Ai ba mai motar bane sai ki taho mu tafi farar kura kawai”.
“Humm ALLAH Yaya bazaka ganeba. Shi Yaya Shareff ɗinne ya cika takura da hana mutane sukuni suji daɗin rayuwa”.
“Maybe yana tsare mutuncin kayansa ne kar kiga laifinsa”.

Bata wani gane mi Khaleel ɗin ke nufi ba, saboda da hausa yay maganar ta buɗe ta shiga tana dariya kawai. Shima yasan bata gane ɗin ba dan haka ya dara.

Tun daga waccan ranar Anam ta sake kafa wasan ɓuya da Yaya Shareff, motar Khaleel ta samu matsala, sai kawai ta koma bin school bus na yaran gidan. Kasancewar suna fitar sassafe kafin Shareff daya tsiri zuwa gidan da safe ya iso har sun wuce. Ana tashi kuma zatai wuff ta fito ta tari napep. Motar Yaseer ma dai ta daina shiga duk da yata bibiyarta da son jin ba'asi tana tabbatar masa babu komai.

Samarinta biyu da sukafi takurama rayuwarta taga sun rage manne mata. Dr Jamal da Muzzaffar. Kowannesu kuma yanada gurbi na musamman data ajiyesa dan koba komai suna sakata nishaɗi a wasu ɓangatorin na rayuwa. Sai dai ta gagara neman jin dalilin kowannensu akan ɗan janye mata da yayi, garama Muzzaffar sukan ɗanyi waya jefi-jefi ko chart wasu ranakun.
A gidan nasu kuwa bata da wata damuwa sai su Hussaina wataran, dan idan rashin kunyarsu ya tashi sukan mata sai dai bakinsu nashan bugu dan bata ɗaga musu ƙafa. Ta daina zuwa gaida Mommy da Gwaggo sai in ta ritsa sun haɗu a hanya taita sinne kai wajen gaishesu. Ko kallonta basayi, dan a ganinsu ma ƙin zuwa gaishesun ta taimakesu koba komai sukan manta da wanzuwarta a gidan. Hakan baya damunta, takan wataya tsakanin sashen aunty amarya da Mom abinta. Ita da Aysha da sauran yaran gidan kuwa sai sambarka. Hakama Daddy da Abbah a koda yaushe cikin bama rayuwarta kulawa suke fiyema da yaransu, dan kullum da tsarabar da waninsu zai kawo mata gidan da kuma mata nasihar tsare mutuncinta suke.
Kusan kwanaki goma kenan basu haɗu da Shareff ba, sai a yau da akai sa ranar auran Maheer da sam bata san da zancen auren ba sai da taga akwatina a sashen Mom akace na auren Maheer ne yau za’a saka rana da kai akwatinan. Tayi mamaki sai dai batace komai ba, sai daga baya Aysha ke bata labarin ai Maheer ɗin baya son auren Mommy ce ta takura kamar yanda ta takurama Shareff shima. Auren zumincine da ɗiyar ƙanwarta. Sosai Anam taita mamakin hali irin na Mommy, a ganinta ta cika takurama ƴaƴanta a gidan, musamman Yaya Shareff da Yaya Maheer ɗin. Gashi suna mata matuƙar biyayya fiye da duk sauran yaranta, dan tasha ganin Mommy nama Aysha da su Hussaina faɗa suna ƙunƙuni. Itace ma kema Aysha faɗa da nuna mata illar hakan ga iyaye. Sai kuma gashi masu mata biyayyar sunfi shan wahala a hanunta fiye da su Ayshan da sai abinda suke so sukeyi.
Batabi takan duk hayaniyar da ake a gidan ba, kasancewar ma a sashen Mom baƙin da zasuje kai kayan suke isowa, saita fito domin wucewarta sashen aunty amarya ta huta dan asabar ne. Kamar ta juya taji, lokacin dataga motarsa na ƙoƙarin yin fakin gab da sashen Mom ɗin, amma sai ta dake ta fuske zata wuce abinta.
Siririn tsakin da taji anyi dai-dai zata gitta ya tilasta ta juyowa, dan sam baiyi kama da tsakin Yaya Shareff ba. Fadwa ce a tsaye cikin shigar madam getzner shadda da taci uban aiki sai walwali take, tabbas tayi ƙyau sosai. Anam ta sakar mata wani murmushin ƙularwa da kashe mata ido ɗaya ta cigaba da tafiyarta. Kusan ɗan cin karo sukai da Shareff daya zagayo waya manne a kunensa yana magana. Shima dai sanye yake cikin shaddar fara tas datai masa ƙyau da fiddosa a asalin bahaushensa ɗan arewa dan harda hula. Ta ɗan ja baya yayinda shi kuma ya tsaya cak dan gaba ɗaya hankalinsa akan waya yake baima san wainar da suke toyawa da Fadwa ba. Kallonsa tai tana wani ƙyaƙyƙyafta idanu, sai kuma ta tunzura baki gaba ganin kallon nata da yakeyi shima tamkar idanunsa zasu cinyeta. “Good morning”. Ta faɗa tana gittasa da ƴar sassarfa.
Cikin basarwa ya cigaba da wayarsa, hakan sai yayma Fadwa data tsaresu da idanu daɗi harda matsowa zata rungumesa ya kauce mata yana nuna mata sashen Mom. Cikin shagwaɓa tace, “Ni dai ka gama mu shiga tare ALLAH kunya nake ji”.
Sarai yasan ƙarya takeyi, amma sai baice mata komai ba har ya kammala. Gaba yay ta bisa a baya….

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button