Labaran Kannywood

Gaskiya ta bayyana… Ba fim ne ke kawo mana kudi ba – Asiri ya tonu yanzu-yanzu

Ba Fim Ke Bawa ‘Yan Fim Kuɗi Ba, Harkokin Da Su Ke Yi A Waje Ne Suke Samun Kudi, Ta Dalilin Sanuwar Fuskar Su, Kuma Nima Na Ci Wannan Gajiyar Ba Kaɗan Ba, Har Yanzu Kuma Ina Kan Cin Ta, ~ Cewar Mawaki Kuma Jarumi Adamu Hassan Nagudu

 

Daga Adamu Hassan Nagudu

 

“Tun da na fara Fim, kawo yanzu, ban yi Fim ɗin da aka ɗauki dubu 50 ko dubu 30 ko dubu 20 aka ba ni ba, balle in yi tanadin wani abu”.

 

Dangane da waɗannan kalaman da dattijuwar jaruma Ladin Chima ta furta da yadda mutane su ka ɗauke su, su ke kuma amfani da su wajen ɗora kafatanin ƴan Fim akan mizani guda su na zartar musu da hukunci ɗaya, na rashin kyautawa ko rashin kirki har da rashin adalci da ake kallon ƴan Fim da shi game da abun da ta yi ikirarin ana biyan ta, na fahimci akwai rashin takamaimai yadda tsarin harkar Fim a Ƙasar Hausa musamman a wajen mutanen mu na Arewa da su ke hangen abun daga nesa.

 

Abun da mu, mu ka sani a cikin gida daban ne da wanda mutane su ke zato ko tsammani da hasashe, tun kusan kafuwar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

 

Amma bari na takaita akan iya abun da na ke son yin martani a kan shi na biyan jarumai kuɗin Fim, wanda abun farko da ya kamata mu fara sani shine, nawa ake kashewa ne ma gaba ɗaya wajen shirya Fim ɗin sukutum ɗin sa.

 

Domin idan aka ce kuɗin da ake kashewa wajen shirya Fim, ya kunshi tun daga samar da labari har zuwa matakin da Fim zai kammala ya shiga kasuwa ne. Kenan bayan jarumai akwai wasu da su ke zaman mahadin da sai da su ma Fim ɗin zai yiyu, wanda su ma kuma dole biyan su ake yi.

 

Waɗannan kuwa sun haɗa da, marubuci, darakta, mai ɗaukar hoto, mai kwalliya, mai kawo sutura, mai haska fitila, mai naɗar sauti, mai haɗa hoto, mai zanen fasta, mai kula da walwala, mai zirga-zirga, mai shiryawa, mai samar da dandali, mai kula da ci gaban shiri, makaɗi, mawaƙi, duka su na da ruwa da tsaki da rawar takawa a cikin Fim. Kuma duk biyan su ake yi.

 

Amma abun da ya kamata a sani anan shine, wanda ba lallai ɗan kallo ya sani ba, duka waɗannan ma’aikatan da ma ƙarin wasu da akan iya samu, da yawan adadin jaruman da za su taka rawa a cikin Fim, ƙaddara mutum 20 ko 30 ko 40, ana iya aiki da su a samar da kammalallen Fim cikakke akan kuɗin da bai wuce dubu 500 ko 600 ko 800 ko Miliyan Ɗaya ba.

 

Fim kuma mai tsawon mintoci 150, wanda za a gutsura shi zuwa na 1 na 2 zuwa na 3 da na 4.

 

Idan Fim mai ɗauke da mutum 30 ko 40 da ma’aikata 20 na fili da na ɓoye, za a kashe masa kuɗi dubu 700 ko 800 zuwa miliyan 1, (wanda kuma irin waɗannan fina-finan su ne kaso ma fi yawa a masana’antar Kannywood tun samuwar ta a 1988) nawa ne kenan za a biya kowa a matsayin hakkin aikin sa?

 

Idan abu ba sana’a ko harkar ka ba ce, kar ka kutsa ciki ka na bayan fage ka kama hukunci ko alƙalanci a cikin ta.

 

Don haka a masana’antar Kannywood, ana iya shirya Fim sukutum da guda akan Naira dubu 200 kacal.

 

Kuma ka ga manyan jarumai a ciki, kuma ya fita ya shiga kowane saƙo da loko na duniyar Bahaushe. Kuma ya na ɗauke saƙo mai girma da taɓa zuciya.

 

Wani zai ce to, nawa ake biyan kowa kenan kuma a kan wannan kuɗin kuma Fim ɗin ya fita da labari mai ƙarfi da jarumai manya? To, amsar ita ce ba kowa ake biya a cikin duk waɗanda aka ga bayyanar fuskokin su a cikin Fim ba. Ko kuma a cikin ma’aikatan bayan fage ba.

 

Me yasa hakan to? Ko kuma me ke jawo hakan? Kuma meye ribar su kenan in dai ba za a biya su ba? Akwai!

 

Duk wani jarumi ko jaruma da ka gani ko wani cikin ma’aikatan Fim da katon gida ko ƙatuwar mota da shiga ta alfarma, ba kuɗin Fim ba ne.

 

Dukan su kuwa! Ina nufin ba kuɗin da ake biyan su a Fim ne suke tarawa har ya yi yawan da za su sayi wasu abubuwan jin daɗin rayuwa ba.

 

Wani zai ce, “To, daga ina su ke samo kuɗin da su ke facaka da su da ake gani kenan, Ahmad?”

 

Babban abun da harkar Fim ke gadarwa mai yin sa shine, SHUHURA, ƊAUKAKA, SANUWA da yaɗuwar fuska ko sunan mai yin harkar, walau jarumi ko ma’aikacin bayan fage.

 

A dalilin wannan SHUHURA da ɗaukakar, ya kan samu dimbin masoya, masu ƙaunar sa a dalilin rawar da ya ke takawa a cikin fina-finan.

 

Masoyan nan kuma, su kan zama daga cikin dukkan rukunonin mutane a cikin duniya gaba ɗaya.

 

Kama daga mata, maza, yara, manya manyan mutane, attajirai, masu mulki, shugabanni, sarakuna, ƴan kasuwa, ƴan siyasa da sauran su.

 

Wannan Soyayya ko burge su da ɗan Fim ɗin ya ke yi, sakamakon ganin shi da su ke yi a cikin wannan Fim ɗin dubu 600 ɗin nan, shi zai sa su nemi gani ko haɗuwa ko sanin sa ko kiran shi ma har gidajen su don su nuna jin daɗi da gamsuwar su kan wani abu da ya ke yi da ke ƙayatar da su.

 

Kuma babu yadda dai, irin waɗannan mutanen za su kira ɗan Fim ko mawaƙi zuwa gare su, ya fito haka nan hannu rabbana ba tare da wani ƙunshi ko dunkulin girma ba.

 

Wanda a dalilin hakan sai ka ga, duk wanda ya yi wa wani ɗan Fim ko mawaƙi wata gagarumar kyauta, automatically sai ka ga ya zama ubangida ko uwargijiyar wannan jarumi, jaruma ko mawaƙin.

 

Ta yadda duk wani abu na shi idan ya tashi sai ka ga an gayyaci wannan ɗan Fim ɗin. Kuma duk wata hidima da ta tashi, ta su, sai ka ga wannan ɗan Fim ɗin cikin sabgogin su.

 

Ba ka ankara ba, sai ka ga waɗannan mutanen sun zama kamar ƴan uwan ka, ta yadda kai ma duk wata hidima taka da ta tashi, su ma za su jiɓanci lamurran ka.

 

Kuma babu wani fitaccen ɗan Fim da ba shi da irin wannan (iyayen gidan) cikin rukunin mutane da na zayyana a sama. Kuma ubangida ko uwargidan ma ba ɗaya ko biyu ba. Saboda yawan masoyan su.

 

Wani bai ma taɓa gani ko haɗuwa da wanda ya ke so ɗin ba, amma idan ya dunƙulo wata kyautar ya turo masa, sai ka ga kamar rabon gado aka yi ya turo masa na shi kason.

 

Shi ya sa za ka ga rana tsaka mutum ya canja kamar juya bayan tafin hannu daga gaba zuwa baya.

 

Don haka alfarmar da ke cikin harkar Fim ta na da matuƙar yawa. Kuma hakan ma ya danganta da karɓuwa da yaɗuwar da ka yi kan wata rawa da ka ke takawa a fina-finan.

 

Akwai misalai da yawa da mu ka sani cikin ƴan uwan mu, ƴan Fim waɗanda aka yi wa irin waɗannan abubuwan na alfarma dalilin kasancewar su ƴan Fim.

 

Akwai jarumin da wata mata da bai taɓa gani ba, ta aiko direba har Kano ya kawo masa kyautar mota ƴar uban su, da bakin shi ya ce wallahi bai taɓa ganin ta ba. Wannan ɗaya ne kawai.

 

Sannan daga yanayin rawar da ka ke takawa a cikin ayyukan ka da yawan zancen ka da ake a gari, ya kan ja hankalin wasu Kamfanoni, Gwamnatoci, Ƴan Siyasa, Ƙungiyoyi Masu Zaman Kan su na cikin gida da na waje, Hukumomi daban-daban, su kan nemi jaruma, jarumi ko mawaƙi ta hanyar Furodusa ko Darakta don su yi amfani da suna ko fuskar sa wajen yaɗa manufofin su.

 

Ga nan misalai nan da yawa a cikin ƴan Fim da mawaƙan nan na mu.

 

To, wannan ya sa kowa ke dagewa wajen yin ayyuka da motsi don a ji shi a gan shi, don ya samu wannan recognition ɗin daga wajen wasu da za su iya ba shi aikin da ba na Fim ba.

 

Kuma ban ware ba, babu wani jarumi da ke Kannywood a yanzu da sunan shi ke amo wanda in ya samu wata dama, ba ya assasa wani abun da zai dinga kawo masa kuɗin shiga a wajen Kannywood ɗin ba. Kenan ita harkar sila ce kawai, amma ba ita ke kawo maka kuɗin ba.

 

Misali ni a yanzu, ta dalilin Social Media na haɗu da mutanen da su ka ba ni ayyukan da na samu alherin da tsakani na da harkar sai dai son barka.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button