Labaran Kannywood

Gaskiya ta bayyana… Ba fim ne ke kawo mana kudi ba – Asiri ya tonu yanzu-yanzu

 

Domin har na haɗu da ubangida cikin manyan mutane a nan Arewacin Najeriya, kuma ya zama komai nawa.

 

Ni na san jarumai da yawa waɗanda don kar sunan su ya yi kasa a mance su, damarmaki su dinga tsallake su ya sa su ke Fim, ba don abun da za a ba su ba.

 

An sha kiran Ali Nuhu, Adam A. Zango, Sani Danja, Yakubu Muhammad, Sadiq Sani, Zahraddeen Sani, Baballe Hayatu, Hadiza Gabon, Jamila Nagudu, Ibro, Daushe, Nuhu Abdullahi, Fati Washa, su zo su yi aiki, su taka rawa a Fim, amma su tafi ba tare da an ba su ko sisin kwabo ba.

 

Saboda kawai mai Fim ɗin wataƙila zai yi don neman kasuwa ne ko kuma saboda kusancin da ke tsakani. Musamman Ali Nuhu da Sani Danja da Zango, sun fi kowa yi wa Daraktoci da Furodusoshi wannan abun.

 

Don ban san sau nawa Ali ke karɓar aikin Fim, ba tare da an yi ciniki da shi ba, sai an gama sai ya ce da mai Fim ɗin Allah ya kawo kasuwa. Ya bar kuɗin, ya yi masa a matsayin gudummowar sa.

 

Akwai manyan jaruman nan da dama, irin su Hajarah Usman, Saratu Daso, Marigayiya Mai Aya, Asma’u Sani da Ladidi Fagge da su Bashir Nayaya, idan ba ka da ko sisi ma, ka same su ka yi musu bayani, wallahi tsaf, za su yi maka aiki kuma ba tare da sun damu ba. Meye a ciki?

 

Don haka kamar yadda na faɗa a sama, ba Fim ke bawa ƴan Fim kuɗi ba. Harkokin da su ke yi waje dalilin sanuwar fuskar su, akan doron wannan alfarmar su ke rayuwa. Kuma nima na ci wannan gajiyar ba kaɗan ba, har yanzu kuma ina kan cin ta.

 

Game da jarumai mata kuwa, duk da ba zan bada shaida akan abun da ban sani ko gani ba, amma a ƙaramin misali, ko budurwa ce a unguwar ku (kai mai karatu) kai ko ma a gidan ku ne, aka ce Samari na zuwa zance wajen ta, akwai yiyuwar wani a ƙoƙarin neman Soyayyar ta, zai iya saya mata waya, sutura, kayan kwalliya, yi mata Anko, ba ta kuɗi da sauran su.

 

Kuma ko da akwai wata alaƙa ko wata manufa ce da shi, amma dai ya na yi mata. To, ƴar unguwar ku ma kenan, da iya yankin ku, a garin ku kawai aka santa.

 

Ina ga Hadiza Gabon, Jamila Nagudu, Fati Washa, Maryan Babban Yaro, Zeepretty, Ummi Rahab, Bilkisu Shema, Bilkisu Abdullahi,Nafisa Abdullahi da sauran su? Wani haka kawai saboda ya na son wata jarumar Fim ko tana burge shi, ba ma a Najeriya ya ke ba, zai kira ka ya nemi ka isar mata da wani saƙo.

 

Idan ya jefe ta da wata kyautar, sai ka rasa ta in da ma zaka fara bayar da labarin. Ka rabu kuma da NAMIJI akan abun da ya ke so da ƙauna. Babu abun da ba zai iya yi a kai ba. Mu maza mun san wannan, musamman idan ka na da wadata.

 

Akwai da dama wallahi cikin ƴan matan Fim ɗin nan, da masoyan su ke musu kyautar motoci ko wasu abubuwa ko kuɗaɗe ba tare da sun taɓa ganin su ba, kuma daga mata da maza.

 

Ni nan, na shirya fina-finai da dama sun kai 6, wanda babu wanda na taɓa kashe kuɗin da ya kai dubu 500 a kan su.

 

Na ƙarshen nan, shine A DALILIN WASA. Wanda jarumai manya ne a cikin sa, amma gaba ɗaya ban kashe dubu 200 ba.

 

Girman ka a fagen harkar sana’a ko aiki da sanuwar ka, shine ke auna mizanin alheri da damarmakin ka.

 

Kuma kuɗin da ka ke samu, ka na da ƴan uwa da iyalai da dangi, kai ma za ka ji da su ne, ko kuma za ka yi ta kashewa wasu don ku na harka ɗaya da su?

 

Akwai abun da sadaukarwa da sha’awa da ra’ayi ne a cikin sa, ba wai zallar kuɗin da za a biya ka ba.

 

Akwai da yawa a cikin ƴan Fim da na sani waɗanda ta sanadin harkar Fim su ka samu damarmakin da su ka bunkasa da gawurta, su ka samu alheri, wanda kuma harkar ta daina yi da su saboda zamanin su ya wuce. Amma sai su ka yi amfani da wadatar su wajen dawowa fagen don dai a ci gaba da jin amon su.

 

Akwai waɗanda ma a cikin su, da in sun ji za a yi wani babban Fim da zai yi motsi sosai, su su ke biyan masu Fim ɗin ma don a ba su gurbi a ciki.

 

Ko kuma idan su ka ga Furodusa mai ƙaramin ƙarfi ne kuma ya taso da nasibi, sai su saka hannu a kan shi, su yi amfani da kuɗin aljihun su da su ke samu daga wasu harkokin, su tallafa masa ya mike don ya ci gaba da yi da su. Mata da maza su na yin hakan kuma.

 

Kai hatta wasu a cikin mawaƙan mu ma, su na yin haka. Musamman a cikin irin shirye-shiryen nan masu dogon zango na manyan gidajen Talabijin ɗin nan.

 

Don haka a masana’antar Kannywood, gudun yada ƙanin wani ake yi. Kowa ƙoƙari ya ke yi, ya yi abun da zai samu ya tsira don ya rayu cikin rufin asiri. Kowa kan sa ya ke nemawa. Fafutukar da ake yi kullum kenan shine ta yaya za a samu kusanci da shiga cikin sabgogin da za a samu a rabauta da wani abu.

 

Wannan ya sa kusan duk wani mai sananniyar fuska, ya na da wani ɗan Siyasa da ya ke jingine da shi a matsayin mai gida ko wanda ya ke tallata manufofin sa.

 

Wanda kuma wannan ya sa yanzu da dama cikin ƴan Fim da mawaƙa su ke samun damarmakin naɗa su akan wasu mukamai daga matakin Jiha har Tarayya. Ashe in da ba ka dage akan aikin ka, an ji ka, an san ka ba, da babu wanda zai damu da kai balle har a dinga damawa da kai ba.

 

Daga ƙarshe, ko ba a biya Ladin Cima kuɗin aikin fitowa a Fim ba, akwai kuma kuɗaɗe ta dalilin Fim ne ta same su, wanda ƴan Fim ɗin ne su ka ba ta, ko kuma su ka yi mata sanadin samun su. Ciki kuwa har da Hadiza Gabon da ta bata kyautar 250K a wajen ɗaukar shirin Gidan Badamasi.

 

Da kuma gidan da mawaƙi Kamilu Koko ya bata akan ta zauna har ƙarshen rayuwar ta, kamin daga bisani, ta dai dalilin Fim ɗin ta samu na ta muhallin na kan ta, ta fita daga na shi. Rarara ya taɓa bata kyautar kuɗi dubu 100.

 

Suna na Adamu Hassan Nagudu

 

Mawaƙi

Furodusa

Marubuci

Ɗan Jarida

Ƙwararre A Kan Harkokin Yanar Gizo

 

10-02-2022

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button