Labarai

Masu Canjin Kudi Sun Fara Kin Karbar Kudaden Kasar Waje A Yola





Masu canjin kudi a jihar Adamawa na kin amincewa da kudaden kasashen waje daga kwastomomi saboda rashin tabbas da ake samu a kasuwar kama-da-wane.

 

Wasu daga cikin ‘yan canjin kudi da Zuma Times ta zanta da su a Kasuwar Zamani ta Jimeta da ke Yola, sun ce sun shiga cikin fargaba kwatsam da kuma ci gaba da faduwar dala, lamarin da ya janyo tabarbarewar kasuwan.

 

Shugaban kungiyar dillalan canji a jihar Adamawa, Lawan Mai Yasin, ya ce ‘yan kasuwar sun tafka asara sosai bayan da suka sayi dala kan Naira 870 daga hannun ‘yan kasuwa kafin nan take ta fadi zuwa N680




Related Articles

Leave a Reply

Back to top button