KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 1 to 10

💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹

                    NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 

(Mrs nura kuriga)

                    1to5

Sorry my fans najin banci gaba dayi muku posting ba hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiya da nayi gashi yanzu na fara daka farko thx

Bismillahir rahmanir rahiim, godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sake bani dama na rubuta wani littafi, Allah ya bani ikon gamawa lafiya, 

         KIRA GA MASU CANZA MIN NOVEL

Duk wanda ya kara canza min novel koya cire suna na ban yafe ba, Allah ya isa,

Tana zaune a cikin daya daka cikin jerun manya manyan kujerun falon wanda ya sha ado da kayan more rayuwa, idonta na kan tv, tana kallon tashar channel, amma gaba daya tunaninta baya wajan, inka ganta zaka rantse hankalinta na kan Jin sauraran news din da akeyi ne, gaba daya Kiran da kanwarta ta Mata a waya taji tana kuka shine ya d’aga Mata hankali, toh maiya sameta data ki fada Mata, tace sai tazo, ta danyi ajiyan zuciya tare da fadin nasan dai tatsuniyar gizo bata wuce koki, bari tazo inji koma miye. 

Hauwa ta shigo cikin falon gidan tana kuka, ganin haka yasa hajiya salma ta tashi tana fadin Hauwa maiya faru haka? Tun dazu kinsa na kasa sukuni, Hauwa bata kulata ba sai kukan ta da taci gaba dayi, ganin haka hajiya salma yasa ta zauna ta gefenta tare da fadin Hauwa miye amfanin wannan kukan, kina ganin shine zaiyi miki maganin matsalanki? 

Lokaci daya ta kurama hajiya salma ido, kaman mai son gano wani abu, tace salma anya ni dake uwarmu daya kuwa? Hajiya salma da mamaki tace Hauwa mai kike fada haka, anya kina cikin hayyacinki kuwa, karfa ki manta uwarmu daya uban mu daya, dan mai yasa zaki dinga tantama, bayan kin san mu biyu ma suka mallaka iyayenmu, 

Hauwa dai kallonta kawai take, lokaci daya tace salma mai yasa bakya son nima inji dadi irin yanda kike ji, mai yasa bakya son ganin farin ciki na, mai yasa ba zaki sa nima na zama tauraruwa wajan mijina ba, kaman yanda kike a wajan mijinki, indai ko ciki daya muka fito zaki soni da wannan abubuwan, salma tace Hauwa bani da wani buri a kullum shine inga farin cikin ki, wlh Hauwa ina shiga damuwa fiye da yanda kike zato duk ranan da naji kin samu matsala da mijinki ko kuma na tuna irin rayuwar da kuke yi, bakin ciki na daya shine babu abun da zan iyayi a kai, sai dai in tayaki da Addu’a duk da kema kina da naki laifin…..  Dan Allah niba wannan nake son jiba salma, nidai kawai ki hadani da malaminki yamin aiki ko zan dace, “Salma tace Hauwa wani irin malami kuma, Hauwa ta Mata kallon rainin wayau tare da furta in baki gane ba ina nufin bokan ki wanda ya mallake miki mahmud baya ganin kowa sai ke,” Salma tace amma Hauwa kin ban mamaki wlh ke har zaki iya furta min wannan maganan, bayan kinfi kowa sanin koni wacece, wlh Hauwa ban taba zuwa wajan boka ba ko wani malami ba…  Dan Allah ya isa haka nifa ba yarinya bace yanzu nasan komai, kuma wannan maganan da kike fada kin San ko mahaukaci bazai kama ba balle ni da hankali na, duk matar da mahmud ya aura saita bar miki gidan nan, sannan duk abunda kika cemai shi zai miki, sannan kice wai bakya bin malami, kima daina wani boye2 domin nasan komai, tana fadin haka ta tashi tare dayin tsaki ni zan wuce in kinki hadani da malamin zan nemo wani, tayi fuuuuu ta fita cikin fushi, salma ta girgiza kai cikin takaici yanzu itama Hauwa ta yarda ina bin boka, tace wai mai yasa ake samun irin wannan matsalan ne musamman a kasar hausa, indai miji zai nuna miki so toh za’a ce kin mallake shi, amma idan yau za’aga Kuna fada zaki ji bamai cewa komai sai dai ma a sami masu muku dariya, na rasa mai yasa Mata da yawa suka yarda da bin boka ba, wanda a dan nazarin da nayi, duk mace mai bin boka bata cikin kwanciyan hankali domin kullum tana cikin fargaba kar abun data kulla ya warware, na rasa mai yasa mutane ke zargina akan ina bin malamai ba, shin laifi ne dan mahmud yaso ni a matsayina na matarshi? Tayi dan shuru domin bata da amsa kuma bata damai bata, ganin tunanin bashi da amfani yasa tayi kitchen dan daura dinner, 

Ya fito daka office, yana irin tafiyar nan tashi na kasaita, gefe kuma masu bashi tsaro ne suke biye dashi, yazo zai shiga mota sukai ido biyu dashi wanda wajan kwana biyu kenan yana ganinta, kaman zai Mata magana saiya share kuma, ya shige motar security ya rufe, sannan suka wuce tunanin yarinyar daya gani yake tayi wanda yau shine rana na biyu daya taba ganinta, tabbas yarinyar nan akwai abun da take nema, daka gani tana neman taimako, har suka shiga gida ya fito yayi ciki, wani kamshin turare ya bigi hancin shi, ta fito da sauri cikin English wear tayi hugging dinshi lokaci daya duk yaji ya manta da damuwar shi, salma tana da kyau wanda duk wani namiji zaiso ya mallake ta, uwa uba ga biyayya sai yasa mahmud baya ganin ko wace mace sai ita, duk da irin miskilanci irin nashi inka ganshi wajan salma da yanda yake mata sai kayi mamaki, ya kuma janyo ta tare da kara rungumeta yana Jin kamshin jikinta wanda ako da yaushe yake son ji, salati sukaji tare da tafi duka suka waiga dan Jin muryan hajiya binta maman mahmud, fuskanta babu alaman wasa ta kalli Salma wanda tayi kasa dakai gabanta na fadi dan tasan yau akwai rigima domin zuwan hajiya binta gidan ba alkairi bane, cikin sanyin murya ta gaidata amma bata amsa ba, ta kalli mahmud tace dole ka like mata bayan sihirin data maka harda karuwanci, toh wlh bari kaji indai nice uwarka kuma nono na kasha inaso ka kara aure koh naga jikana domin na gaji da jira,wannan karan ma sai nasa anyi min Addu’a sosai domin a barka da wacce zaka aura karta kuma koranta, kuma wlh wata uku na baka indai ya wuce haka zaka ga fushi na, tana gama fadin haka tayi waje, gaba daya jikin mahmud yayi sanyi tare da tausaya ma Salma ya rasa mai yasa zuri’anshi suka tsaneta sunbi sun damu akan bata haiyuwa wanda ni nasan na Allah ne kuma komai lokaci ne, Salma duk da irin tashin hankalin data shiga, ganin mijin nata yayi shuru yasa ta matsa gareshi tare da hura mishi kunne, yayi firgit ya kalleta ta sakar mai murmushi tare da fadin baby ba tunani zaka tsaya yiba yanzu kazo mu zauna musan miye mafuta kafin nan da wata daya ka nemo min kanwata nasan hajiya za tayi farin ciki, nima hakan zaisa inji dadi, yace salma bani da wacce nake so Sai ke wlh salma bazan iya auren wata mace ba, domin nasan bazan iyayin adalci ba, domin ke daban ce a cikin rayuwa na, tabbas tasan mahmud na santa itama tana sonshi tana bala’in kishin shi, amma dole ta daure tayi hakuri a wannan karon ma ya kara aure, duk da tasan abune mai wuya ya dade da matar, lokaci daya taji wani azababban kishi. 

Hajiya binta rai bace ta shiga gida, taga zaliha a falo zaune da alama ta dade da zuwa,kanwar hajiya binta ce, tace a’ah zaliha yaushe kika zo tace tun dazu, ina kika je da wannan yamman haka, tace gidan mahmud mana, yaro matarshi duk ta shanye shi baya ganin kowa sai ita, zaliha tayi murmushi domin an tabo Mata inda yake Mata kaikayi, tace aini hajiya wlh da zaki dauki shawara na da anyi yar gida shida fauziya hala ma itace keda rabo dashi, nan hajiya binta ta washe baki tace aiko kin kawo shawara amma fah kin San wannan matar tashi a tsaye take dan muma sai mun tashi tsaye, zaliha tace kar ki damu ni zanyi maganinta yanzu dai saiki fada mishi dan nasan bazai miki musu ba tace babu damuwa, zaliha tayi wani murmushi wanda ita kadai tasan na miye……. 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button