NOVELSUncategorized

GIDAN UNCLE 42

*GIDAN UNCLE*

*PAGE FOURTY TWO*

Kuka ta sake saki me ciwo tana girgizawa Aunty Jameelah kai, sake Mata hanu tayi tace “bazanyi miki dole ba kamar yanda Daddy yayi alqawarin bazaiyi miki dole ki yarda ki auri
Hameed ba amma ina tausayawa rayuwarki a gdan wani ba Hameed ba domin shine mahadinki shine abokin rayuwarki kuma shine qaddararki ko ki yarda ko kada ki yarda Hameed nakine kema tasace kamar yanda yasha fadamin danshi kadai aka halicceki saboda haka kiyi gaggawar dawowa hayyacinki kafin kiyi abinda zai zame miki ciwo har qarshen rayuwarki”Tana fadin haka ta dauke Shurafah a jikin Umaimah ta cire mata Pampers tayi mata tsarki  karbarta Umaimah tayi ta  fita zuwa dakin Hajiya ta bude ta shiga da sallamarta tasa kai ta shiga turus taja ta tsaya ganin Hajiya zaune gefen gado ta hada kai da gwiwa tanata gursheqen kuka.
Jiki a matuqar sanyaye ta qarasa ta tsugunna a gabanta ta kwantar da kanta a cinyar Hajiya kawai itama ta saki kukan da sauri Hajiya dago tace.“Ke meye hakan Umaimah?” Cikin kuka tace “kiyi hqr don Allah Hajiya insha Allahu Uncle zai samu lfy zai warke kuma zaici gaba da rayuwa cikin farin ciki kamar baya don Allah Hajiya ki daina kukannan banaso ya kikeso muyi keda zaki rarrashemu” shafa bayanta Hajiya tayi tace “na fidda rai da rayuwar yaronnan Umaimah koda ya farfado idan yaji hukuncin da kika yanke na bazaki qara rayuwa dashi ba zaiyi mutuwar dungurungum saboda nasani kece zuciyarsa Umaimah bazai iya rayuwa babu keba…” Zamowa Hajiya tayi tayi knilling a gaban Umaimah ta ruqo hanunta tace “Don Allah badon niba Umaimah ki taimakeni ki yarda ki rayu da dana kece cikon farin cikinsa Umaimah zan rasashi idan kikaqishi don…..”  Saurin rufewa Hajiya baki tayi cikin kuka tace.“Kada ki qara hadani da Allah Hajiya ko baki hadani da Allah ba nasani kuma na amince Yayana Abdulhameed mahadin rayuwata ne bazan iya rayuwa babu shiba bansan inason Uncle ba kuma bansan ciwonsa nawa ne ba sai yau dana ganshi Hajiya na shirya sake komawa qarqashin inuwar auran Uncle Hameed indai wannan shine zaisa yaci gaba da wanzuwa cikin farin ciki….” Wata runguma Hajiya tayi mata tana kukan dariya tace “na gde miki yata Allah yayi muku albarka Allah yabawa dan’uwanki lfy kuci gaba da qawatamu da salon qaunarku mai ban sha’awa” murmushi tayi tace “ina Daddy Hajiya?” Ajiyar zuciya tayi tace “yana Riyadh gurin Hameed shida Yusuf” Sunkuyar da kanta tayi tare da qurawa Shurafah idon har yanzu idan ta kalli Shurafah sai taji tsanar Hameed a ranta amma tayi alqawarin kankareta a zuciyarta saboda cikar farin cikin iyayensu miqewa tayi a salube ta kwantar da Shurafah tace “na kawo miki ita ta tayaki hira inason zuwa harami ne Hajiya” murmushi tayi ta matsa kusa da Shurafah tace “ja’ira mekan qwanqwalati bata da aiki sai bacci kamar kasa nidai bansan ina kika debo ragwanta ba iyayenki duk ba ragwaye bane” murmushi Umaimah tayi tace “kun daifi kusa ta kwana tana maki waqa” itama dariya Hajiya tayi tace “to ya zanyi hausawa sunce abin cikin qwai yafi qwai dadi ai Allah ya taimaka saikun dawo” Amsawa tayi da amin sannan ta fice taje ta tarar da  Aunty Jameelah har ta shirya suka fito da qafa suka tattaka har masallacin harami suka fara gabatar da ibadarsu kamar kowanne musulmi itadai Umaimah rasa abin da zata roqi Allah tayi banda abu uku yafiya, samun lfyr yayanta da kuma shiriyar yarta Shurafah basu sukabar harami ba saida sukayi sallar asuba da yake tun kwanaki sha biyar da haihuwarta ta tsarkaka sai ciwon dinkin da tasha da har yanzu bai warkeba har zuwa wannan lkcn dingisa qafarta takeyi bata taketa sosai ba.Haka sukaci gaba da gabatar da ibadarsu cikin rashin nutsuwar zuciya saboda itadai Umaimah hankalin ta yaqi kwantawa saboda rashin sanin halin da Hameed din yake ciki ranar da sukayi sati biyu a qasar Saudia ne ranar Daddy ya samu Umaimah a dakinsu shida Hajiya ya dubeta yace. “Uwar masu gida Hajiya ta sameni da wata mgn a baya kinyi furucin bazaki sake rayuwar aure da Hameed ba kuma yanzu naji kince kin janye hakane?”Jinjina masa kai tayi cikin kunya  yayi murmushi yace “amma dai ina fatan ba wanine ya takuraki ya canza miki raayi ba?” Sake daga masa kai tayi yayi ajiyar zuciya yace “naji dadin hakan kuma nayi farin ciki da faruwar hakan Umaimah Allah yayi muku albarka ya shiga cikin lamarinku a gobe idan Allah ya kaimu zanje harami a mayar muku da auranku jibi saiku wucce Istanbul zuwa lkcn da zaku dawo komai yayi Normal da izinin Allah”Dagowa tayi da sauri tace “aa Daddy nikam na fasa zuwa Istanbul dinnan ba” kallonta yayi da sauri yace “meyasa?” Qasa tayi da kanta tace “Daddy hankalina bazai kwanta ba ana zuwa yawon shaqatawa ne saboda nishadi toni nawa farin cikin yana asibiti baisan wake akansa ba wlh Daddy koda na tafi hankalina bazai taba kwanciya ba kayimin hqr bazan iya tafiya bansan halin da Abdulhameed yake ciki ba”…….. *UMMUH HAIRAN CE…✍????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button