GIDAN UNCLE 45
*G.U*
Daqyar Jameelah ta iya rarrashin Umaimah saboda yanda take kukan bilhaqqi da gsky tace “babu komai Umaimah ki kwantar da hankalinki kici gaba dayi masa biyayya
kima kiyi hqr da duk abinda zakiji ko ki gani Umaimah da hqr da rashinsa taqinsu kadanne idan kuma kikayi hqr zaayi dake kuma shi zalinci baya tabbata indai Hameed yayi aurene ne saboda ya zalinceki da sannu zakiga sakayya batare da kinje ko inaba yauwa kuma nasan kinsan komai game da gdansu kishiyarki basu zama da kishiya balle ke da duk inda Hameed ya zauna bashi da zance sai naki bashida hira sai taki sannan ko badon wannan ba saboda kyawunki da quruciyarki Salma zata zafafa kishinta akanki to ke kiyi qasa da naki duk da kowa ma ya sani namu na gadone bama iya control dinsa idan ya motsa amma ki rinqa daurewa kina dagewa kina basarwa kada ki yarda mijinki da kishiyarki su gane raunin ki ta wajen kishi musamman kishiya Umaimah kada kiyi kuskuren nuna Mata ke raguwa ce sannan ki riqe Allah ki cire kasala ki rinqa tashin tsakar dare kina fadawa Allah damuwarki lkcn da kowa yake bacci da sannu Allah zai kawo miki mafita Umaimah wlh daga Daddy har Hajiya babu wanda yayi ammanna da auren nan kawai dai don babu yanda zasuyi dashi ne kinsan mijinki da murdadden hali akan raayinsa saboda haka ko kadan kada kiga laifinsu kuma kada kiga laifinsa shima ina zargin bayin kansa bane saboda nasan tarihin soyayyarsu da Salma tun zamanin quruciya ma baisota ba balle yanzu data zama abinda ta zama”
Kukanta take qoqarin tsayarwa tace “amma Aunty haka zanci gaba da zama dashi banida wani amfani a gurinsa sai lkcn biyan buqatarsa idan naqi ya gwadamin qarfi babu ruwansa da halin da zan shiga kawai shidai buqatarsa ta biya anya Hameed yana sona kuwa Aunty kamar yanda kike tunani?” Ajiyar numfashi Jameelah tayi tace “karki damu da wannan Umaimah nidai alfarma daya zan nema a gurinki duk rintsi kada ki yarda karatunki ya salwanta ki tsaya kaida fata wajen ganin kin gama karatunki ki fitar dashi daga zuciyarki Umaimah inada tabbacin duk ma inda yaje zai dawo gareki saboda kedin is naturally kinada qualities din da baduk mace ba”
Da wadannan kalaman ta rinqa rarrashin qanwar tata harta tursasa ta akan taje tayi masa girki batayi musu ba tana ajiye wayar ta tashi ta shiga kitchen ta fara shirya masa dinner tare da kunna karatun qur’ani saboda ragewa kanta quncin zuciyar da take ciki bayan ta gama ta shiga wani daki a qasan abin yaso bata dariya dakin guda kayan wasan Shurafah ne ajiyeta tayi a ciki ta nufi sama tayi wankanta tayi kwalliyarta me kyau tsari ta dawo parlourn ta zauna tare da daukowa Shurafah motar wasanta taci gaba da zagayawa a parlourn tanata debewa uwarta kewa sunata dariyarsu saidai idan lkcn sallah yayi ta tashi tayi ta dawo ta zauna haka har lkc yaja ta tashi ta shiga dakinta ta sake shiryawa cikin kayan baccinta tana tsaka da fesa turare ya shigo gdan yaga yanda ta gyara ko ina sai abin ya burgeshi Umaimah akwai tsafta komai nata kaf-kaf cikin tsari yunwa yakeji sosai saboda shi iya wuya bai yarda yaci abinci a waje ba indai ba qasar ya bari ba.
Dinning table ya nufa ya zauna yana bude abincin qamshi ya dakeshi ya lumshe idonsa ya bude tare da fara zuba abincin daidai lkcn ita kuma ta gama lallaba Shurafah ta sauko da gudu²n ta domin daukar wayarta tun tana saman ya qura mata ido yanajin wata muguwar faduwar gaba yarinyar komai nata daukar hankalinsa yake towai shi mene ma yaja raayinsa ga Salma har yake sha’awar aurenta ita ba kyau na azo a gani ba ita ba diri ba nagarta ba ita ba komai ba amma yanajin kamar zai zauce akanta amma dai ya sani koma me yakeji akan Salma baikai wanda yakeji akan Umaimah ba saboda duk inda yake a fadin duniya indai a cikin hayyacinsa yake to ita kadai yake tunawa.
Baiji qarasowarta ba saida yaji sautin sassanyar muryarta tace “sannu da zuwa” firgigit ya dawo hayyacinsa ya sakar mata murmushin sa me tsada ya lumshe idonsa tare da budewa daidai lkcn data bar gurin ta matsa kusada center table din ta dauki wayarta ta juya zata wucce ta tsinkayo muryarsa yana fadin “Hearty” tsayawa tayi cak ya taso a hankali ya sanya hanunsa ya tallafo faffadan hips dinta daya baje cikin blue din rigar baccin jikinta iya gwiwa yaja numfashi me qarfi yace “bazaki tambayeni meyasa naje nakai dare ban dawo ba” wani mugun yawu me zafi ta hadiye tare da kada kai tayi gaba zata tafi saboda batajin zata iya furta masa kalma daya me dadi a yanda takejin zuciyarta na tafasa idan ta ganshi sake ruqota yayi yace “naje gurin Salma ne akan tsare²n yanda bikin zai kasance so abin yazo unexpected babu wani shiri bazan samu damar yimata lefe ba shine tace na bata million daya da rabi tasai kayan fitar biki so naje na cira na bata shine nakeson kema ki fadamin abinda kikeso nayi miki?”
Yamutsa fuska tayi ta hadiye wani yawu me daci tace “na gde” daga haka bata kuma cemasa komai ba ta juya zata tafi ya sake ruqo hanunta yace “kamar kina sauri Babyn Uncle wai bakyason gani nane kome?” da sauri ta daga masa kai tace “eh hakane Abu Shurafah wlh banason ganinka jinake kamar na kashek….” da sauri ya hade bakinsu ya matseta a jikinsa sosai qirjinsa yana bugawa da sauri².
Sosai take kiciniyar qwacewa amma yawi qyaleta yaqi sakin mata baki saida yasha iya shansa sannan ya saki wasu hawaye masu zafi suka zubo masa yace “wannan kalmar ita Hajiya ta fadamin yanzun nan kema kuma kika sake maimaita min Umaimah nima wlh bansan meyasa nakeson auran nan ba nasani babu wata mace da nakeso da sha’awar kasancewa da ita a duk fadin duniya data wucceki ki yarda dani Umaimah aure na qaddara ce kuma kece kika jayo nasani badan kin gujeni ba da qila bazan hadu da Salma ba balle naji inason aurent…..”
Daga masa hanu tayi tace “ya isa haka Abu Shurafah nasani kuma naji auranka qaddara ce kona yarda ko kar na yarda ba fasawa zakayi ba saboda haka yardata batada wani amfani amma nidai nidai nasan auranka ba qaddara bace son zuciyarka ne duk da haka inayi maka fatan alkhairi ka matsamin na wucce inada abinda yafi wannan surutun muhimmanci” tana gamawa ta fincike hanunta ta haura saman da gudu²nta bin bayanta yayi da kallo yana hadiyar yawu mace iyakar mace.
Daga murya yayi ya kira sunanta amma Ina ta shige dakinta ta datse yaja wani gwauron numfashi ya sauke ya koma gurin abincin ya rinqa turawa daqyar danma yanajin yunwa ne kawai Umaimah ta riga ta rikita masa lissafi ba dafaffan abinci yakeso ba danye yakeso kuma na jikinta, da wannan tunanin ya gama ya tashi ya shige dakinsa yayi wanka ya dauki remote control din qofar dakin nata ya fita ya nufi dakin ya bude ya shiga a saman sallaya ya sameta tayi sujjada tana kuka tana roqon Allah cikin larabcinsu na shuwa kuka takeyi sosai tana roqon Allah ya kawo mata dauki ya rabata da qaddararren auransa.
Miqewa yayi da sauri ya dagota zuciyarsa na tafasa baisan meyasa kowa ya juya masa baya akan auran Salma ne koda yake dama yasan haka zata faru amma baitaba tunanin zafin kishin Umaimah yakai haka ba baitaba tunanin zata nemi rabuwa dashi akan wannan qaramin dalilin ba……….
*UMMUH HAIRAN CE…✍????*