GUDAN UNCLE 44
*G.U*
Janye jikinta tayi daga nasa a hankali sai yanzu ta sami qwarin gwiwar bude baki a sanyaye cikin sarewa da
sallamawa farin ciki tace “kishiya zakayimin Uncle me nayi maka meyasa bazaka bamu damar gyara aurenmu da tsarkakeshi ba sai ka zabi kawo wata cikin rayuwarmu a lkcn da mukafi buqatar kusanci da juna ko badon komai ba don rayuwar yarmu bazance maka kada kayi aure ba Uncle amma ka sani tunda na taso a zuri’ar mu banga gdan da ake zaune da mace sama da daya ba wayyoh ni Umaimatu meyasa qaddarorina suke da tsauri ne….”
Saurin rufe Mata baki yayi da nasa ta tureshi da sauri saboda jitayi kamar ya sanya mata garwashin wuta a lebanta ta qarasa gaban Shurafah da taketa wasan ruwa ta dauki sabu ta fara sabawa yarinyar batare da tana ganin komai ba saboda zuciyarta da tayi mata nauyi.
Da sauri ya qaraso ya janyeta saboda yaga neman kashe yarinyar takeyi ya qarasa mata wankan lkcn daya fito tana hada kayanta a trolly ya tsaya sake da baki yana kallonta bata dago ta kalleshi ba har saida ta gama ta miqa masa hanu domin ya bata yarinyar amma yaqi haushi ne yasata jan akwatinta zata fice yayi saurin riqeta yace “kina hauka ne Babyn Uncle Ina zaki da safennan”
Dagowa tayi da idanunta da suka dade da canza kala zuwa jajaye ta watsa masa wani mugun kallo tace “gda zani Abdulhameed idan naci gaba da zama dakai a qasar nan sai ka kasheni kayiwa Aunty Jameelah asara don na tabbata ita kadai keda asarar rashina” tana fadin haka ta figi jakar kayanta ya kuma fincikota jikinsa na rawa yace “kiyiwa girman Allah ki tsaya ki fahimceni Umaimah wlh nima bason auren nan nakeyi ba bansan meyasa nakasa cewa aa ba plz Umaimah ki yarda dani ki karbi aurannan a matsayin qaddara ki amince dani wlh bazan taba cutar dake…..”
Marin data daukeshi dashine yasashi hadiye mgnrsa bata damu da yanayinsa ba ta dora da cewa “ ya isa haka Abdulhameed qaryar nan taka ta isheni so nawa ka cuceni cuta ta nawa kakeson yimin Hameed ka lalatamin quruciya ta wajan jarabarka ka yaudareni da kalamanka na qarya na sabawa ubangijina kayimin cikin zina na haifa ina kallon Shurafah a matsayin ciwon da bazai taba warkewa a rayuwata ba sannan yanzu kazomin da mgnr aure auren ma bana yarinya me qarancin shekaru kamar ni ba na guzuma sa’arka saar yayata sannan guzumar ma ka rasa wadda zaka hadani da ita sai Salmah Hameed Salman da babu wanda baisan tambari da kirarin gdansu ba ba kishiya ba dan miji babu uwar miji wannan shine kirarin da akewa uwarta Hameed tun ina qanqanuwata nasan da wannan kirarin sannan yanzu kazo saboda tsabar kai dan akuya ne qaramin mara kunya kacemin wai mutuniyar arziki ce ok na yarda a gurinka tunda idanunka sun rufe Salmah mutuniyar arziki ce amma ni a gurina bata isa na hada miji da ita ba wlh na hqr dakai Hameed nabar mata kai….”
Kamata yayi da sauri ya rufe bakinta a duniya babu kalmar daya tsana kamar yaji tana furucin ta hqr dashi.
Girgiza mata kai yayi yace “na…naji duk naji Umaimah amma ya zanyi wlh jinake kamar idan ban auri Salmah ba mutuwa zanyi kamar yanda nakejin idan na rabu dake zan mutu don Allah ki bani hadin kai Umaimah…” Kokowa suka rinqayi sosai ta akan saita fita inda shikuma ya dage akan bazata fita ba daga qarshe cillata yayi saman gadon ya fice ya kulleta ta waje.
Kifa kanta tayi a saman pillow ta rinqa kuka kamar ranta zai fita tanajin dama mutuwa tayi ta huta indai mutuwar hutu ce a gareta Shurafah ce ta rarrafo ta kwanta a jikinta itama tasa kukan miqewa tayi ta dauki yarinyar tana kuka tasa mata kaya ta bata nono tasha ta sake komawa ta kwanta tanajin zuciyarta kamar tayi tsalle ta fito.
Abin na Hameed kamar wasa saida suka qara kwanaki goma a Saudi babu wata mgn dake shiga tsakaninsu saidai kawai idan zai fita da safe ya kulle qofar parlourn idan ya dawo ya bude ya shiga yayi abinda yaga dama duk yanda yaso yaga ya shawo kanta taqi shawuwa takai ta kawo ma basa hada daki indai yananan to ita kuma zata kulle kanta a daki ta yini bata fito ba yasha tashi cikin dare yana buqatarta yayita dukan qofar yanayi mata magiya amma kamar batama san yanayi ba.
Hakanan a daddafe sukayi kwanaki goman suka dauki hanyar 9ja taso batace masa qala ba har suka isa katafaran gdan daya gina a tudun yola me part biyu har ciki dan taxi din ya shiga dasu suka fita ya sallameshi ya nufi wata qofa ya bude suka shiga tabi parlourn da kallo yayi kyau sosai sai qafar benen ya nufa tana riqe a hannunsa Shurafah tana daya hannun ya bude wata qofa yajata suka shiga ya sauke Shurafah dake bacci a wani qaramin gado dake gefe ya mayar da qofar ya danna Mata key ya tako zuwa gabanta yakai hanu zai ruqota ta zille da sauri yayi murmushi ya fara balle bottle din rigarsa ya balle belt din wandonsa ya zare Shortnicker din jikinsa ya nufota jikinsa na rawa ta janye ya cafkota da qarfi yace.
“Saboda zanyi aure Umaimah sai akace idan mijinki zai qara aure ki qaurace masa ki daina kulawa dashi ki daina sauraron kukansa da buqatarsa hakan shine zaisa yasoki ya fasa abinda Allah ya hukunta masa kada ki mayar da kanki jahila bayan nasani bakin gwargwado iyayenmu sun bamu ilimi kada ki biyewa son zuciya ki cutar damu Umaimah inasonki kina sona kada mu zalumci kanmu qarin aure bashine yake rusa zaman lfy da farin cikin gda ba rashin fahimtar junane ki yarda dani inasonki” yana fadin haka ya janyota jikinsa yaci gaba da famfata da kalamansa masu saurin canza mata tunani duk da haka kuka takeyi hakanan ya rinqa sarrafata tana kukanta tana komai ya rabata da komai na jikinta ya kwantar da ita ya rinqa aika mata da saqonsa yana tsotseta hakanan badon tanajin dadi ba yayi abinda zaiyi ya dagata yaje yayi wanka yana fitowa wayarsa tayi ring ya dauka da sauri jikinsa har rawa yakeyi ya kara a kunnensa yace “hello my love ganinan fitowa” kalmar ba qaramin girgiza nutsuwa da lfyr jikin Umaimah tayi ba ta zuba masa ido yanda yake ta sauri yanasa kayansa baiko bi takanta ba yayi ficewarsa ta miqe daqyar ta leqa ta window taga yanda yake wani gudu² ya shiga motarsa ya fice tana tsaye jikin windown wani malolo ya taso mata a zuciyarta yanzu duk wannan saurin da yakeyi saboda wata mace yakeyi yana ganin halin da take amma ya tsallake ya barta saboda buqatarsa ta biya.
Da wannan tunanin tayi wanka ta fito ta shiga kitchen ta dora tea ta dawo parlour ta zauna tana zama tajiyo kukan Shurafah ta miqe ta haura ta daukota ta dawo ta zauna har lkcn idonta bai daina zubar da ruwa ba daidai lkcn wayarta tayi Ring ta daga da sauri ganin number Aunty Jameelah tace “he… helo aunty yaushe zakizo?” yanda taji muryar yar uwar tata tasan ba lafiya ba tace “yadai meye ya faru Umaimah naji Daddy yace mijinki aure zaiyi saura kwana uku daurin auren hakane?” Ajiyar zuciya tayi tace “hakane Aunty Salman gdan Alh Musa zai aura….” katseta tayi da sauri tace “kutumar ubancan wannan tsinanniyar gantalalliyar yarinyar zai auro miki Umaimah kayyy Innanillahi wa innah ilaihir raji’un wannan wacce irin masifa ce ne Umaimah me kikayi masa haka?”
Cikin kukan da batasan yaushe ta fara ba tace “bansani ba Aunty wlh iyakar sanina banyiwa Abdulhameed komai ba Aunty meyasa rayuwa na zama karfa ne wacce batada rabon farin ciki meyasa kowacce masifa take fadowa kaina ne? Aunty meyasa su mama da Abba suka mutu suka barni Allah da nasan wannan muguwar rayuwar zan riska bayan mutuwarsu dana bisu mun tafi tare”……..
*UMMUH HAIRAN CE…✍????*