NOVELSUncategorized

GIDAN UNCLE 62

*GU*

Wani abune yaji ya caki zuciyarsa ya juyo da sauri yace “aure kuma wa zaka aura habadai wlh tun lkc be qure maka ba ka kama gabanka Umaimah ba matarka bace nayi mata miji”
tsayawa Sulaiman yayi sororo har Hameed ya shige parlourn yana zuwa ya fara dukan dakin na Umaimah yana cewa “aure fah yace Umaimah aure? Wlh qarya yakeyi ya aureki” Daddy dake zaune ya miqe ya haye sama.
Ita kuwa tanajinsa taqi budewa muryar Hajiya taji tanayi masa mgnr ya juya ya fara sababi yana cewa ai duk ke kika daure mata gindin tacimin mutunci harni wani zai tara yacemin wai auren matata zaiyi wlh bazai yuwu ba kasheni kukeso kuyi” Hajiya ce ta haushi da bala’in da yafi nasa dole yayi qus sai zafin zuciya da sharar hawaye da yakeyi.
Tana zaune a dakin wayarta tayi qara tana dagawa taga Dr sunan da tayi saved din number Sulaiman da ita ta daga tace “ina fatan ranka bai baci da abinda bloody yayi maka ba” gabansa ne ya fadi yace “ bloody kuma wifey Hameed fah kenan?” 
Ajiyar zuciya tayi tace “hakane shine mijina na farko shine Abu Shurafah Dr qaddara ce ta rabani dashi nasani yana Sona kuma yana kishina so wannan dalilin yasa nake boyeka gareshi saboda nasani bloody baya da juriya akan duk abinda ya shafeni nasan baqin kishinsa kuma nasan matsalarsa yanada matsalar heart attack shiyasa banason abinda zai taba lfyrsa ko banza yayana ne shine ya riqeni tun bayan mutuwar iyayena kuma uban yayana ne….” 
Numfashi yaja me qarfi yace “ya  isa Umaimah pls ya isa haka don Allah ki gabatar dani a gdanku wlh da gaske nakeyi inason yin aure nagaji da kadaici sweet inason nima naga yayana abokaina daga me yaya biyu sai me uku nima yakamata ace yanzu inada iyalina wlh ko bakya sona zan hqr na rayu dake sweet please” murmushi tayi tace “to yanzu ya kakeso ayi Dr?” numfashi ya sauke yace “ki bani dama na shigo gdanku na gabatar da kaina iyayena suzo ayi mgnr aurenmu Allah ni idan son samuna ayi bikinmu da wuri saboda a matse nake sosai inason naji abinda akeji”
 Ta bude baki zatayi mgn taji Hajiya na cewa “Baby kizo Daddynku yana kiranki” amsawa tayi da to ta miqe tace “afwan D.S zanje Daddy yana kirana” amsawa yayi da “babu matsala amma don Allah ki duba buqatata Ummuh Shurafah” ajiye wayar tayi ta dauki mayafinta ta yafa ta fito saida gabanta ya fadi ganinsa kwance a parlourn ta raba ta gefensa zata wucce ya riqo hanunta ta juyo da sauri ta zuba idonta cikin nasa ya miqe zaune ko riga babu a jikinsa ya janyota da qarfi ta fada jikinsa ya matseta a qirjinsa yana goga mata gashin qirjinsa yace “kasheni kikeson kiyi ko Umaimah saboda kinga inasonki shine har kika dauko wani banza kika kawosh…” Daga masa hanu tayi ta janye jikinta daga nasa ta hade rai sosai tace “banaso kada ka qara zagarmin mijin da zan aura Hameed duk yanda nake mutunta ka da baka haqqinka a matsayinka na yayana hakan baiyi maka ba saika shiga rayuwata to gaskiya banas….” bai barta ta ida fadi ba ya dora lips dinsa saman nata ya riqe qugunta sosai yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya qoqarin qwacewa take yaqi bata dama neman zura hanunsa yakeyi a rigarta ta qanqame jikinta ta saki kuka daidai lkcn Hajiya da Daddy suka sauko daga saman turus suka tsaya Hajiya tayi saurin rintse idonta ganin yanda suke kokawa bilhaqqi yana neman balle bottle din rigarta Daddy ne ya daka masa wata uwar tsawa hakanne yasashi dakatawa da abin da yake shirin aikatawa ya hada kansa da kujerar yana mayar da numfashi ita kuma ta miqe da gudu tana kuka ta qanqame Hajiya wani takaici ya cika zuciyar Hajiya tace.
“Kin fara biye masa ko to wlh baku isa ku cusa mana baqin cikin da kuka qunsa mana a baya ba saboda haka Daddy yau dai ka ganshi da idonka wannan shaidanin yaron ko Umaimah bata bashi hadin kai ba ana kwana ana tashi saiya yaudareta balle itama qwaryar sama ce ke dukan ta qasa haline yazo daya harijan banza da wofi to wlh ki fito da miji kiyi aure duk kwartancinsa ai baya biki gdan mijinki ba ko” kuka takeyi sosai tace “wlh Hajiya ba gurinsa nazo ba Kiran da kikace Daddy yanayi min shine ya fito dani shi kuma ya tsayar dani” Daddy ne ya kamo hanunta yace “waye yazo gurinki dazu?” “malami nane Daddy” “meye ya kawoshi ance ba zuwansa na farko kenan ba ko?” Dagakai tayi tace “eh zuwansa na uku kenan wai aurena yakeson yi” murmushi yayi yace “alhmdllh anzo gurin to ke ya kika gani kina son sa?” Kallon Hameed tayi daya dago kansa da sauri ya zuba idonsa akanta yanason yaji me zatace sake maimaita tambayar Daddy yayi yana kallon Hameed din cikin in…ina tace “aa.. eh Daddy” murmushi yayi yace “amsa daya nakeso ki bani eh ko aa” kawar da kanta tayi da sauri tace “eh Daddy” tana fadin haka ta kwasa da gudu ta fada dakinta shima miqewa yayi da sauri yace “haba Daddy meye hakan wanne irin tanasonshi yanzu aura masa ita zakayi Daddy kada kuyimin haka ku bakwa kishina ne wlh duk ranar da kuka daurawa Umaimah aure da wani nama mutu na gama na kwanta da ita wani ya kwanta da ita…”Bige masa baki Hajiya tayi tace “to ai matsalar tace tanasonshi saboda haka ka shafawa kanka lfy ka nemi mata ka aura ka huta da kwana kai daya kana fama da azumi kullum” Daddy ne yace “idan kin shiga kice da ita nace ta turomin shi gobe inason ganinsa” amsawa tayi da “karkaji komai Daddy Sulaiman mutumin kirki ne kullum yazo gurinta saiya aikomin da gaisuwa yanzu Umaimah zatayi aure me yanci” maganganun iyayen nasa mugun caccakar zuciyarsa sukeyi yaja qafa daqyar ya shige dakinsa ya fada saman gadon zuciyarsa na tafasa ya miqe da sauri ya dauki magungunansa yasha ya koma ya dauki wayarsa ya kira number Umaimah amma sai yaji user busy ya sake kira haka a qarshe dole ya hqr ya qyaleta.

A ranar da Daddy yace yanason ganin Sulaiman washe gari yazo suka zauna da Daddy sukayi mgn bai fada Mata yanda sukayi ba washegari Hajiya ta aiketa gdan Aunty Zarah  a ranar magabatan Sulaiman sukazo gdansu suka kawo kudin aurenta dubu dari biyu da hamsin aka tsayar da lkcn biki wata daya masu zuwa  washegari dake juma’a Hajiya ta cire Shuraif daga nono itadai batayi mgn ba kuma bata tambaya ba sai bayan kwana biyu Sulaiman yake tsegumta mata cewa an kawo kudin aurensu har anci kwanaki uku.
Batayi wani farin ciki ba sukayi sallama ta ajiye wayar hakanan Hajiya ta rinqa gyarata ta kowanne bangare gyaran jiki gyaran sama da qasa babu inda Hajiya bata yiwa gyara irin nasu na shuwa ba.Shi kuwa Hameed tun ranar da aka kawo kudin auren Umaimah yake wani mugun zazzabi da ciwon qirji fushi yakeyi da Daddy sosai musamman da Daddy yace shine zai karbi waliccin auren Umaimah…… *UMMUH HAIRAN CE…✍????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button