NOVELSUncategorized

DIYAM 28

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twenty Eight: Destiny

Kafin mu cigaba please let us all take a moment and pray for Maryam Sanda and then pray for ourselves. Allah ya
sa wannan hukuncin da aka yanke mata ya zamar mata alkhairi a duniya da kuma a lahirar ta, mu kuma Allah ya kare mu daga mummunar kaddara, Allah ya kare mu daga sharrin shaidan da sharrin zuciya, Allah yasa mu fi karfin zukatan mu a kodayaushe.

Bayan haka ina kira ga matan aure manyan mu da kananan mu, please idan kin tabbatar your marriage is not working, idan kin tabbatar kin je limit dinki na hakuri a gidan auren ki, please walk out of the marriage. Allah ya halatta saki for a reason, wani lokacin rabiwar tafi alkhairi akan cigaba da zaman. It is better a kiraki da bazawara then ki kasance in maryam sanda’s shoes.

Sannan iyayen mu dan Allah ku dube mu da idon rahama, ku tausaya mana, dan Allah idan yarinya tazo gida tace ta gaji da zaman auren ta please ku bincika sosai, idan tana da gaskiya kuyi supporting dinta, kar ku tura yarku ga halaka, karku tura yarku zuwa wuta. 

Now, let’s continue with labarin Diyam maybe anan ma da akwai darasin da zamu dauka.

Da mamaki karara fuskarsa yake kallona, maybe bai taba tsammanin zan iya mayar masa da magana haka ba. Yace “ke? Kin san dawa kike magana kuwa? Ni din ne ma kike cewa za’a makala miki?” Na cigaba da kallon sa cikin ido duk a cikin kokari na na nuna masa cewa bana jin tsoronsa, amma zuciyata in banda lugude babu abinda take yi. Ya daga hannu da niyyar wanka min mari sai kuma ya kalli gidan inda hayaniya take fitowa daga tagogin sama, ya fahimci yana dukana zan tara masa jama’a dan haka sai ya dunkule hannunsa sannan ya sauke, ya nuna ni da dan yatsa yace “in kika sake kika shigo gidan nan sai na karya ki” na fusge hijab dina daga hannunsa nace “not today, kuma ni bani zan shiga gidan ka ba sai dai a shigo dani dan dole” na juya na tafi na barshi anan ina jin dadi a zuciyata, ashe dai Sadauki bai tafi da dukkan Strength din nawa ba, ko kuma maybe a time din wannan hug din ne yayi passing some of his strength and courage to me.

Muna komawa gida na wuce direct zuwa dakin inna, na gaisheta tana ta washe baki tace “kun dawo? Ya gidan?” Na tashi ina ninke hijab din dana cire nace “lfy lau” tace “lfy lau? Shikenan abinda zaki ce? Bayanin gidan zaki yi min inji dame dame aka saka kuma menene ba’a saka ba” nace “Inna ban sani ba nikam, ban shiga ciki ba a waje na zauna” nan fa takama fada, ni kuma nayi shiru har saida ta gama sannan nace “Inna yace inna shiga gidan sa sai ya kashe ni” sai ta girgiza kai tace “fada kawai yake yi, shima fushi yake yi saboda an matsa masa akan maganar nan, daga ke har shi ba kwaso amma abinda mu iyayenku muka hango ku ba zaku hango shi yanzu ba sai nan gaba zaku fahimta”.

Washegari ina kwance kamar kullum sai ga aike wai ana kiran Inna, ta tashi ta tafi can kuma ta dawo sai naga cards a hannunta. Ta miko min tana kallon fuskata har na karba na karanta. Katin daurin aure ne, sunana da sunan Saghir, date din kuma nan da kwana uku. Na ajiye su akan cinyata ina jin dan kuzarin dana samu jiya yana draining kawai sai hawaye na ya fara zuba akan cards din. Na tuno abinda Sadauki ya gaya min “how litres of hawaye zaki zubar ne acikin wata daya?” “Be strong” he said, sai na kara karfin kuka na, wanne Strength ne dani kuma bayan bani da gata? Bayan ana so ayi amfani dafarinciki na gurin faranta wa wanda yake da gata? Saboda namiji ne shi nikuma mace? Ko saboda yana da uba a duniya ni bani da? Sai Inna ta zauna a kusa dani ta kwantar da kaina a kafadarta tace “Alhaji yace za’a hada daurin auren da addu’ar kwanaki arba’in din baffan ku, sai bayan daurin aure da sati daya sannan zaki tare, saboda ki samu damar gayyatar kawayenki da sauran shirye shirye”. Na dago kai ina sake kallon date din, sai nayi realizing shine date din da za’a yi resuming school.

Tun daga lokacin taste din abinci ya dauke daga bakina, nayi kuka kamar idona zai cire har bana gani sosai, nayi addu’a na gaya wa Allah, kullum kuma sai na gaya wa Inna “Inna bana son auren Saghir” amma kamar busa sarewa nake yi, babu wanda ya dube ni, babu wanda ya mayar da damuwa ta wani abu mai muhimmanci ba kowa sai yace “zata daina ne, daga anyi auren shikenan ai ita mace mai rauni ce” ni kuwa jinsu kawai nake yi dan bana tunanin akwai ranar da zata zo wadda zan ji ina son Saghir.

Ranar Lahadi, 28 September aka daura aure na da Saghir. Ranar tun dana tashi da assuba na shiga toilet na rufe kaina na kwanta kan tiles nake kuka har aka gama daurin auren ban fito ba. Sai da Mama tazo sannan da kyar na bude mata kofar toilet din ta shigo ta fito dani, ta kori duk wadanda suke dakin ta zaunar dani akan gado ta bani Alqur’ani tace “kiyi ta karantawa zaki ji sauki a zuciyarki. Kiyi ta ambaton innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah zai sanyaya miki zuciyarki kuma yasa hakan ya zamo abu mafi alkhairi a gare ki” itama sai ta dauko Alqur’ani ta zauna muke karantawa tare, har sai da hawayen fuskata ya tsaya. Ranar daga ni sai ita muka zauna a dakin, ta saka ni a dole naci abinci duk da cewa da kyar yake sauka cikina. Sai kuma na cigaba da karatun ina jin nutsuwa tana samu na, ina jin karfin guiwar karbar kaddara ta, sannan kuma na gabatar da adduoi ga Baffa da Ummah, sannan na yiwa Sadauki addu’ar fatan alkhairi a duk inda yake. Na kuma samu kaina da tambayar kaina ko ya sani? Ko ya san an daura min aure da Saghir yau?

Kwanakin da suka biyo bayan nan shirye shirye ne kawai akeyi na biki. Hajiya Babba baki har kunne sai shiga take yi tana fita tana ta tsare tsare. Inna babu abinda take yi, gaba-daya tayi wani irin shiru da ita sai dai ta saka ni a gaba tayi ta kallo. Ni kuma na zama kamar mutum mutumi, bana kuka amma bana uhm bana uhm uhm. Mama ce tazo ta debi wasu daga cikin kayan lefe na ta kai aka dinka min, sannan ta yiwa Asma’u itama dinkuna tare dasu Rufaida. Sai tace min “Diyam babu wani abin da zaki shirya ne? Ko yar walima haka ke da kawayenki?” Ban kalle ta ba nace “Mama kawayena ai duk sun koma makaranta, ss1 zasu shiga, ni kuma gidan miji zan shiga, waye zai bar karatunsa yazo bikina?” 

Sai tayi shiru bata bani amsa ba amma tana komawa gida sai ga yaya Mukhtar ya kawo Rumaisa, Rufaida da Muhsina sun taho da kayansu zasu zauna har sai an gama bikin. Hajiya Yalwati ta saka aka ware mana daki saboda yan uwan mu da zasu zo daga Kollere zasu sauka a dakin Inna. Ranar Rumaisa ta kawo min waɗansu littattafai guda biyu ‘rayuwar aure a musulunci’ na daya dana biyu tace “ki karanta zaki samu idea akan zaman aure” na karba kawai nace “Nagode” sai kuma tayi dariya tace “ni ban san me kike yiwa fushi haka ba. Mijinki kyakykyawa, kinsan da ina da crush akan hamma Saghir amma yanzu na hakura tunda ya zama mijinki” na tabe baki kawai a raina ina cewa ina ma dai zamu iya chanjen place da ita? Ita ta zama matar tasa ni in koma ita?

Ana gobe kamu Aunty Fatima tazo da mai kunshi zata yi mana, ranar sunga taurin kaina dan da kyar na zauna akayi min dan haka duk wanda baisan bana son auren ba sai daya sani a ranar. Ana gama wa kuma na saka hannu da gangan duk na damalmala kunshin ya chabe. Aunty Fatima kamar ta rufeni da duka dan haushi amma a haka ta kyale ni. Da daddare tace muje saloon sai na saka mata kuka a dole ta kyale ni kar in tara mata jama’a. 

Ranar kamu sai da inna tazo ta sakani a gaba sannan na tsaya akayi min kyalliya. Mun zo zamu tafi gurin da aka shirya dan yin kamun kenan naji wata tayi comment “kunga amaryar kuwa? Yar mitsitsiya” ai kuwa ina jin haka na juya na koma daki a dole sai mai kamun ce ta bini dakin ta kama ni a can. Ranar yini kuwa ni wuni nayi da zazzabi dan haka suka dai suka sha bidirin su. 

Washegari kai amarya, tunda safe Mama tazo, yau ne kadai na ganta tun da aka fara bikin. Tana zuwa yau ma duk ta kori su Rumaisa da dama duk sun addabeni, ta saka ni a gaba yau ma muka yi ta karatu kamar ranar nan, tare muka ci abinci mukayi sallah tare kuma sam bata yi min wata magana data danganci aure ba har magrib tayi sannan ta saka ni nayi wanka ta dauko min wani lace fari tas tace in saka. Ta gyara min fuskata simple make up sannan ta saka min sarka da dan kunne tayafa min farin mayafi ta kuma feshe ni da turare. Na zauna a bakin gado ta rufe min fuskata da mayafin sannan ta mike zata fita, na rike rigarta nayi mata tambayar da ta jima tana yawo a zuciyata, nace “Mama Sadauki ya sani? Ya san an daura min aure?” Ta dauke kai tace “ban sani ba Diyam, na kira layinsa baya shiga maybe ya chanza layi ne” sai ta fita, an jima suka dawo tare da wata matar dana fahimci daga baya cewa kanwar Hajiya Babba ce. 

Tana zuwa ta bude fuskata tace “Masha Allah. Tubarkallah. Lallai Sagjir yayi dace da kyakykyawar mata. Allah ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka, Allah ya baku zuri’a ta gari” Mama tace “ameen”. Sai suka kamani a tare suka fita dani. Sam ji nayi zuciya ta dake bana jin wani kuka kuma. Muka shiga dakin Inna anan na tarar da ita tana kwance ashe wai bata da lafiya tun safe. Na durkusa a gabanta tace “Allah yayi miki albarka Halima, biyayyar da kika yiwa iyayen ki Allah yasa kema naki yayan suyi miki. Allah yasa wannan auren shine mafi alkhairi” muka ce ameen muka tashi. Zamu tafi part din Alhaji Babba aka ce mana wai baya nan ya fita tun safe. A raina sai naji ina kewar Baffa, ba zai taba fita ba ranar da yasan zan bar gida in tafi gidan miji. Gidan kawu Isa muka shiga yayi min fada shima, sannan muka shiga mota muka tafi sauran motocin suna biye damu.

Har muka je gidan banyi kuka ba. Muka shiga ciki sannan naji mun fara gawa stairs sannan muka shiga wani palo sai kuma wani daki. Aka zaunar dani akan gado Mama ta rufo kofa tazo ta zauna a kusa dani ta rike hannuna ta fara magana a hankali

“Diyam ki saurare ni sosai kiji abinda zan gaya miki. Yanzu kin zama matar aure, kin bar karkashin iyayenki kin koma karkashin mijinki haka zalika aljannar ki ta koma karkashin mijinki. Bauta zakiyi, amma ki saka a ranki cewa ba Saghir zaki bautawa ba Allah zaki bautawa. Auren Saghir shine kaddararki, shine jarabawarki. Biyayyar Saghir a yanzu ita ce gaba da komai a gurinki in banda addinin ki. Na sami cewa ba’ayi miki adalci ba, na sani cewa iyayen Saghir basu kyauta ba sun kasa tankwara yaron su tun yana danye har sai daya bushe tukunna sannan kuma suka dora hakkin tankwara shi a kanki, duk da kasancewarki mai kankantar shekaru amma ni nasan zaki iya, in dai har zaki yi masa biyayya, ki kula da cikinsa da shimfidarsa, ki kasance mai tsafta mai hakuri da juriya da kawar da kai a lamuransa, to kuwa duk girman kansa sai kin mayar dashi tamkar rakumi da akala musamman tunda kina da kyau kuma shine abinda aza da yawa a yanzu suke so”.

Ta jima tana yi min nasihohin hanyoyin da take ganin zan bi in jawo hankalin Saghir ya soni, ni kuma sai nayi wa kaina tambayar “ta yaya zan saka wanda bana so ya soni? Biyayya ga abinda baka so is extra hard right?”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button