GIDAN UNCLE 64
*_GU_*
Kuka takeyi sosai tana shigewa jikinsa shima yana qara matseta yanajin ninkin sonta da tausayinta ya yarda so halitta ne duk kyansa da kwarjininsa
amma Umaimah kuka takeyi saboda an daura aurenta dashi wasu hawaye masu zaffi suka zubo masa suka diga a dokin wuyanta yace “kiyi hqr Sweet da zan iya halatta miki Hameed dana halatta miki shi saboda nasani shine burinki” saurin dago da kanta tayi tace “wlh ba hakanne yake sani kuka ba tunanin halin da yake ciki shine yafi dagamin hankali D.S aman jini fah yakeyi…”
Rufe mata baki yayi da nasa ya lumshe idonsa a hankali yanajin wani farin ciki na mamayar zuciyarsa yau da Umaimansa zai kwana a hankali ya janye bakinsa daga nata yace “zamu hadu anjima kiyi hqr ki cire komai a ranki ki barwa Allah ikonsa zan tayaki da addu’a Allah ya sassauta miki son mijin daba naki ba kiso mijinki me qaunarki” murmushi yayi mata ya daga Mata hannu yace “mu hadu a matakin qarshe” ya juya ya fice da sauri batasan sanda tayi murmushi ba sanyi Halin Sulaiman yana burgeta a hankali ta daga hanunta tace “Allah ka cusamin son mijina Allah kabani ikon yimasa biyayya Allah kada ka jarabceni da jarabta irin ta gdan Uncle Hameed”
Haka ta yini a kwance tana juyi Saudat Alfah da Sa’ud da Sarah sune suka zama amarorin bikin suna tausayin Umaimah suna tausayawa Sulaiman da irin rawar qafar da yakeyi akan Umaimah dashi aka zage akayi aikin shirya gdan bai iya barin masu decorations din su kadai ba abokansa sai tsiya sukeyi masa wai ba sabon ba wasu suna cewa dashi wai Allah yasa ba auran kisan wuta tayi dashi ba da haka har magrib tayi aunty Jameela Zarah da Hajiya da Hajiya Kaka sune suka sanyata a gaba suna yi mata nasiha akan ta riqe mijinta amana kada ta cutar dashi domin shi da zuciya daya yake sonta kuma ya yarda zai rayu da ita duk da kasancewarsa saurayi sannan yan’uwansa basu nuna mata wani hali na tur ba mahaifiyar mijinta kamar ta goyata tanata godewa Allah daya nuna mata lkcn auran dan nata sama da shekara talatin da uku amma ko zancen budurwa akayi masa sai ya kama fushi da mutane yau gashi shima yayi mata saidai fatan zaman lfy.
Sosai Hajiya tayi mata nasiha me shiga jiki tare da fitowa ta fada mata bazata taba yafe mataba idan tayi qoqarin kashe aurenta saboda Hameed ta sake fada Mata maganganun da mutane sukeyi akan cewa auren kisan wuta tayi amma D.S ya toshe kunnensa yace yaji ya gani.
Haka yan daukar amarya sukazo tana kuka mecin zuciya wai yau ita Umaimah zaa dauka akai gdan wani a sunan mata? Tana tuna haka ta sake rushewa da kuka hakanan uwar mijinta ta ruqota a jikinta tanata bata hqr da sanya mata albarka Hajiya Sa’adatu mahaifiyar Sulaiman cewa tayi dakanta zata daukowa danta amaryarsa aikuwa haka ta sanyata a mota ta kwantar da ita a jikinta tace “kiyi hqr Umaimatu wlh na tayaki murna kin samu miji saidai fatan dorewar zaman lfy bawai yabon kai ba bakuma dan Sulaiman dana bane nasani zakiyi hamdala kiyiwa Allah gdy yayi miki sauyi na alkhairi na jima Ina fadawa Allah yayiwa junior zabi na qwarai kuma na yarda yayi masa”
Da wadannan kalaman motocin sukayi parking sauran mutanen suka firfito suna ta guda gabanta ya sake faduwa Hajiya Sa’adatu ta kama hanunta Aunty Zarah ta kama dayan suka nufi gdan wata waqa me sanyin sauti yana tashi sunan Umaimah ne da Sulaiman yake tashi a cikin waqar haka suka ratsa har cikin parlourn saida Hajiya Sa’adatu tace “kiyi addu’a kafin ki zauna a bakin gadonki cikin aminci” saida tayi addu’ar sannan ta zauna Hajiya Sa’adatu tayi murmushi tace “alhmdllh yau ubana ya angwance Allah na gde maka Allah yasa bani na dauki jikoki na” murmushi Aunty Zarah da Aunty Jameelah sukayi suka amsa da “amin” sannan suka fara zamewa suna guduwa ya rage gdan daga ita sai Sa’ud da Sarah Saudat Alfah mijinta yazo sun tafi tashi sukayi suka fara gyara mata gdan saida suka gama tsaf sannan suka koma haushi da takaici ya cika Sa’ud tace.
“Nifa kukannan ya isheni Umaimah wlh ko lahira aka kaiki yau yakamata ace kin hqr da kukannan mijinki yana sonki kuma kece kika kawoshi kikace kinaso saboda haka kiyi hqr ki karbeshi kiyi masa duk abinda ya dace” Sarah ce ta cafe zancen da cewa “manta da yar banza anjima kadan lbrn zakiji ya canza…” Bugun qofar ne yasasu yin shiru suka juya da sauri bude qofar yayi ya shigo da sallamarsa ya sauke idonsa akan ya sauke ajiyar zuciya yace.
“Kuyi hqr na katseku ko bari na baku guri” saurin amshewa Sarah tayi da cewa “aa Yallabai ai kayi mana kara ma muma tafiya zamuyi gdajenmu kaima ka huta” murmushi yayi yace “ok kuzo ku gaisa da baqi a waje yana mgnr yana matsawa kusa da ita hanunsa yasa ya bude fuskarta yana murmushi yace “masha Allah wannan rana da girma take” kamo hanunta yayi ya miqar da ita yajata ya hadata da jikinsa suka fita ihu mutanen dake parlourn suka dauka yayi dariya ya zaunar da ita sukayi ya zaunar da ita a saman kujera sukayi raharsu sukayi musu sallama suka tafi tare suka tafi dasu Sa’ud ya rakasu ya dawo ya kulle qofar parlourn ya qarasa ya dagota yana sauke ajiyar zuciya ya riqo hanunta suka nufi dakin yana maqale da ita a jikinsa yace “banyi tunanin zuwan wannan ranar kwana kusa ba Sweet wlh yau Ina cikin farin ciki wanda bazan iya misaltashi ba muje muyi alwala muyi sallah mu godewa buwayi gagara misali”
*UMMUH HAIRAN CE…✍????*