GOJE

GOJE 19 and 20

       FREE PEGE

19&20
Cikin tsantsar tashin hankali! da gigita suka gurfana a gabansa kafin su sheda masa abinda yake faruwa…………..”Ya wani mike a fusace! tare da mi’ka tafkaken hannunsa wanda yatsun ke cike da zabban zinare da azirfa! wani irin bahagon mari! ya dinga kifa musu kafin ya sanya kafarsa ya tunkudesu duka suka fadi wanwar! a gurin. gabadaya suka
Sunkuyar da kansu, jikinsu in banda rawa babu abinda yake.

Ya takarkare! da karfi! ya kurma uban ihu!!! lokaci k’ank’ani gabadaya kaf yaransa suka kewayeshi! ya goya hannu a baya yana kai kawo a gurun!

Tsit! gurin yayi babu mai kwak’wk’waran motsi a cikinsu.

Lokacin da yake kai kawo a gurin kallonshi nake ina mamakin muninsa! baki ne sosai gashi gajere dab da kasa, yana da katon kai da tafkekiyar fuska, gabadaya hallitunsa masu girma ne bayan gajartar da yake da ita, bakinsa kato haka nan hancinsa kwala-kwala idonsa kadai ya isa firgita yaro! jajawur! dasu, kasumba tayi kaca-kaca a fuskarsa babu kyawun gani!
kallo guda za kayi masa ka tabbatar da rashin imaninsa.!

Cikin kaushin murya! ya fara magana kamar haka.” A jinin jikina naji cewar akwai ayarin da suka shirya min! Yau tsayin sati guda kenan idan na kwanta bacci nake ganinsu a idona! babu wani shirinsu da zai firgatani! na shiryawa zuwansu! na kuma yiwa kaina alkawari cewa duk yawansu sai naga bayansu! babu wani mahalukin daya isa ya tunkari inda nake ba tare da she’kashi barzahu ba! nafi karfin hukuma! ballanatana wani dan adam! saboda haka dukkunanin ku na umarceku da cewa ku zauna cikin shiri babu wanda zai fita da rai a cikinsu.”! jiki na tsuma! yake maganar yana wani irin huci! gabadaya ya burkice sakamakon jin abin da yazo masa a bazata!


Saboda tsabar kwarjin da yayi musu sam sun kasa hada ido dashi, suna gurfane a gabansa, yayin da shi kuma ke kai kawo a tsakaninsu kafin yaja tunga ya tsaya a gabansu, hannuwansa ya goya a baya, babu wasa ya fara magana kamar haka.” “Ya sunanku.”?
babu wanda yayi magana a cikinsu. Ya sake maimaita maganarsa! uffan basu ce ba.
Ya juya baya yana kallon jama’arsa dake tsatstaye kowanne a cikin shiri.

“Alba bani wannan dorinar.” yafada yana kallonsa.
Da saurin gaske ya ciro bulalar daga cikin gidanta, kaurinta ya isa! nayi imanin za ta iya dauke fatar mutum.

Ya gyara rikonta a hannunsa, cikin wani irin hargagi! wanda yasa gurin amsawa! yace.”Ba zaku bude baki kuyi magana ba ko.”? Duk da sun tsorata da yanayinsa, amma hakan besa sun magantu ba.

Ya zabura! ya juya tare da kiran Alba! yana zuwa ya umarceshi da ya cire musu kayan jikinsu kaf!
Alba yabi umarni!

Ya kai ya kawo ya gurin jikinsa na wani irin karkarwa! tsumin ne ya tashi! ganin haka ya sanya wasu daga cikin yaranshi suka bara buga gangi!!! da bushe-bushe? Ya sake rikicewa! wani irin tafka! yake musu! suna ihu! da birgima a gurin!
Birgima suke a gurin suna gurnani! yana binsu da tafkekiyar dorinar dake hannunsa yana tafka musu, wanda ya janyo tsiyayewar idon daya daga cikinsu.

Hankalinta a masifar tashi taje tana kokarin rike masa hannu kuka take kariris! tana bashi hakuri sunyi bala’in bata tausayi! bata san bashi da imani ba sai yau!

Tureta yayi ta fad’i kasa ta rirrike kafafunsa “Kayi hakuri wannan rashin imani ne, ka zubar masa da ruwan ido ga jini yana fita a jikinsu kada kayi kisan kai.” Wannan maganganun nata besa ya fasa abinda yake ba, ya sanya kafarsa ya taka gwiwar wanda yake kokarin gudu! ya murza da karfin gaske! wani marayan ihu! ya saki kafin ya zube a gurin yana karkarwa jiki yace.” Yi hakuri kada ka kasheni zanyi ma bayani.”

Ba tare da cire kafarsa ba, ya buga musu tsawa! da fadin” Ya sunanka.”? baki na rawa yace.” sunana Yakubu .” Ya kalli dayan da yake matagugu a kwance “Kai fa.”? Yace.” Sunana Sulaiman.”

Kafarsa ya cire yana wani huci! ya barsu a gurin…….Saman wani icce! ya zauna! wasu daga cikin yaranshi suka bishi! da ruwa…

Wasu na masa fifita wasu kuma na kara kambaba darajarsa!

Nad’in kansa ya warware kafin ya sunkuya tare da bada umarnin a zuba masa ruwa a saman kan.

Ya dago kan yana girgije ruwan sumarshi mai laushi tabi ta kwanta tana digar da ruwa. Alba yasa abu yana tsane masa ruwan.

Har yanxu babu sassauci a tare dashi, idonshi na tsaye a inda suke. tana tsaye a gabansu, magana a suke a tsakaninsu amma basa iya jin abinda suke cewa.

Ranshi ya baci da ganin abinda take, yarinyar ta nema ta lalata masa aiki. mikewa yayi da bulalar a hannunsa ya karasa gurin, kallon mara imani take masa, za tayi magana kenan, a zabure! yayi kanta da bulalar!! ta matsa gefe da sauri! gabanta na bugawa! jajayen idanuwansa ya tsira mata cikin mashahuriyar tsawar data kusa sanyata sakin fitsari yace.” Wuce ki bani guri.”! kafafunta na rawa ta bar gurin, bai ta’ba firgitata ba kamar yau.

Ya kallesu kafin yace.” Ku tashi tsaye! suka yunkura da kyar suka tashi! gabadaya jikinsu ya sauya kama saboda duka! yayi musu wani kallo kafin ya juya da basu umarnin bin bayansa.

Ba tare da iya kallon fuskarsa ba ya fara yi magana kamar haka “Aikinmu shine ta’addanci! rai ba abakin komai yake ba a gurunmu, sannan muna tarewa jama’a hanya cikin dare mu farauci dukkanin guzirinsu, muna rabasu da matansu da ‘ya’yansu, mu kwanta dasu, kamar matan auranmu daga ‘karshe mu ‘kona gawarwakinsu ko kuma mu fito dasu kan hanyar mu yasar! duk wanda ya shiga komarmu bama saurara masa muna da muggan makamai kuma muna da daurin gindi daga sama, kamar yanda ka sani cewa masana sunyi hasashen cewa gurin da muke rayuwa akwai albarkar kasa, to tabbas hakane akwai! amma maigidanmu yaci alwashin cewa babu wani mahalukin daya isa ya amfana da albarkar dake wannan guri sai shi da ayarinsa, yawancin mu musulmai ne magoya bayanshi, amma ya haramta mana ibadah! bama sallah bama salati da duk wani abu da ya cancanta, burin mu ako yaushe mu kashe duk wanda yayi yunkurin shiga gonarmu, maigidanmu yaci alwashi mai zafi! akan duk wanda yayi yu’kurin ganin bayan rayuwasa.” Ya k’are maganar tare da sake risinar da kanshi kasa.

Beyi mamakin da jin wannan jawabi ba, hausawa sukace da dan gari akan cin gari, a jawabin da sukayi masa ya fahimci cewa gabadayansu musulmai ne amma suka yarda suka bada goyon bayan ta’addanci a kasa.

Ya girgiza kanshi da fadin.” Yakubu-Sule daku aka hada baki wani wawa! zindiqi! mushiriki! ya addabi! kasa da al’ummar dake cikinta, shin me kuke nema a duniya da har kuka mayar da zubar da jini! abin banza? a matsayinku na Musulmai masu amsa sunayen annabawa! shin ya cancanta ku aikata wannan ta’addanci.”!

Gabadaya suka shiga girgiza, jikinsu yayi wani irin laushi, yaja numfashii ya fesar! kafin ya cigaba da cewa.” Dukkaninku baku cancanta da cigaba da rayuwa a duniya ba domin barin irinku a ban ‘kasa had’ari ne.”!

Jin abinda ke fitowa daga bakinsa ya firgitasu, a tsoroce! suka shiga bashi hakuri suna kiran sun tuba!!

Wani mugun mari! ya kifa wa daya da jikinsu, ‘yar hantsile yayi ya kifa yaci da kasa! tsaye ya mike! yana zagaye a kansu. gabadaya sun tsorata da yanayinsa, su kansu yaran shi basu taba ganinshi a cikin irin wannan yanayin ba, jikinsa in banda tsuma! babu abunda yake, Zinat kuwa addua take a zuciyarta kada Allah yasa ya aikata kisan kai!

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button