Labaran Kannywood

Ban ga laifin abin da Safara’u ke aikatawa ba, inji Yahanasu Sani

Ban ga laifin abin da Safara’u ke aikatawa ba inji Yahanasu Sani

 

Jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hajiya Yahanasu Sani ta ce ita ba ta ga laifi ba ga abin da Safiya Yusuf da aka fi sani da Safara’u Kwana Casa’in ke yi ba a sabon salon wakokinta.

 

Safara’u Kwana Casa’in dai ta koma wakoki irin na zamani tare da mawaki Mr 442, inda wasu ke ganin kamar ta saba wa addini da al’adun Hausawa.

 

A hirarta da BBC Hausa, Yahanasu Sani ta ce mutane da dama na yawan yi mata magana kan don me za ta ki yi wa Safara’u fada ba a kan abin da ake ganin tana aikatawa a wakokinta.

 

Ita fa harkar rayuwa, kowane da ‘system’ din da ya dauko wanda zai yi masa. Duniya fa yanzu ta zama wani iri. Duniya babu taimako. Sai hassada, sai makirci. Idan mutum ya fara wani abu da ke taimaka masa, idan aka ce wannan abin ya kubuce masa, zai iya shiga wani hali”.

 

Ni gaskiya Allah Ya sani, ban ga laifin Safara’u ba don ta koma wakarta, Allah Ya ba ta nasara, Allah Ya ba ta abin da take nema. An ce tana shigar da ba ta da kyau, to Allah Ya sa ta bari ta gyara. Amma dai ina mata adu’ar Allah Ya ba ta nasara. “Inji Yahanasu Sani”.

 

A cikin hirar da DCL Hausa ta bibiya, an jiyo Yahanasu Sani na shawarartar matan da ke son shiga Kannywood da su rike mutuncinsu domin su zama abin kwatance.

 

Sannan Yahanasu Sani ta ce ta fi son danwake a nau’in abinci. Sannan tana da ‘ya’ya hudu amma daya ta rasu, yanzu saura uku.

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button