GOJE

GOJE 19 and 20

Da jan ido ya kallesu, da fadin.” *Ni! ne zan kawo karshen ta’addancinsa! *GOJE!!* *Nake mai maganin wani takadiri! Nayi tawa! nayi ta wasu! wannan haka yake! ba’a zubawa dani a kwashe lafiya! *Billahil-lazi hurramanu!* nayi wa kaina alkawarin ganin bayansah”! Yanda yake maganar yana zazzare ido shi tabbatar da abinda yake cikin zuciyarsa hakan yake babu ‘karya!

Shar’bebiyar wukar dake rataye a kafad’arsa ya fizgo! daga gidanta, wani masifaffan ihu! ya kurma!!! kafin ya fara dadura! wukar a wuyansa!!
Tashin hankali kenan! gabad’aya gurin ya kacame! dan yaran sa ma manyan wukake! suka fito dashi suna gurzawa a kowane sassa na jikinsu! . shi kuwa a wuyansa yasa wukar ya zage karfi sosai! yake gurzawa.!

kuka wiwi! ta dinga yi tana kallon badakalar dake afkuwa, ita tsoronta kada su kashe kansu, ta rasa ya za tayi da rayuwarta a cikin wannan mashahurin dajin!

Tana kuka na fitar hayyaci ta karasa inda yake gabanta na lugudan duka! hannu na karkarwa take kokarin rike damtsan hannunsa, “Ka bari don Allah! ka daina! ka umarci yaranka su daina kada ku kashe kanku.”!!
Ko sauraranta beyi ba ya cigaba da abinda yake, jikinta na wani irin rawa ta rumgumeshi tsam! tana kuka tare da dukan bayanshi. wannan ya janyo sadudarsa! ya cake! wukar! a gurin tare da danneta da tafin hannunsa!
Numfarfashi kawai yake gumi na yankowa daga kowane sassa na jikinsa!

Tsit! gurin yayi sakamakon umarnin da ya basu, suka mayar da wukaken jikin jikinsu.

Har yanzu tana manne a kirjinsa ta kam’kamshi shi da yayi wani motsi zata kai masa duka! kuma bata fasan kukan ba.

Hannu yasa ya d’ago fuskarta, suka tsirawa juna ido! ya jima yana kallonta kafin yasa hannu ya goge mata hawayen da suke ta zuba! yayi namijin kokarin cireta daga jikinsa! ta sake kokarin rungumeshi! duk a kokarinta na hanashi aikata wani abun.
Hannu ya daga mata da ido! ya gargade ta, sai ta sunkuyar da kai! amma har yanzu bata dawo daidai ba.

Ya kalli Alba da fadin.” Bani abun rubutu.”

Da sauri ya fito da takarda da biro! ya mika masa.
A takaice ya rubuta.”

(KA SHIRYA YAKI DA MAKASHINKA!!!)

Wanda yake da d’an sauran kuzari ya mikawa takardar da fadin.” Sa’kona ne wannan kana isa ka bashi, cewa daga ni MAKASHIN MAZA!

Da kyar! ya mike ya kama hanya yana tafiya tare da waiwayen d’an uwanshi dake kwance cikin halin rai da rayuwa!

Koda ya karanta wasikar sai kawai ya fashe! da wata mahaukaciyar dariya! da mike tsaye tare da dukan! girkakken dutsen dake gabansa!

Hannuwansa yasa ya tallefe ‘keyarsa! tare da sunkuyar da kanshi kasa!

Ya jima a haka kafin ya d’ago yana kallon yaranshi dake kewaye dashi, gabad’ayansu suma jikinsu yayi sanyi da wannan al’amarin.

Ya kalli Nuhu dake rakube! gabadaya kammaninsa sun sauya saboda wuyar da yasha, ranshi ya sake ‘baci! kawai ba tare da kowa ya ankara ba, ya fille wuka! tana! walwali a wuya ya burma masa! a take ya fara shure-shure a gurin jini sai tsartuwa yake, kafin wani lokaci rai yayi halinsa!

Ya juyo kansu a sukwane! yana kallonsu da kwala-kwalan idanuwansa! Sun tsorata mutuka gaya da ganin tashin hankalin maigidansu.

“Cike da cin laya yace.”Kamar yanda na soke! wuyan wannan shashashan! to haka zan soke! wuyan wannan marakunyar yaron daya tunkari inda nake! Ni! nayiwa kaina wannan alkawari!! saboda haka zamuyi kwankwance! kafin mu afka inda suke da yak’i.”

Suka hada baki gurin fadin.”Yanda kayi shine daidai maigida muna goyon bayanka ako wane yanayi.”


Tun bayan tafiyar Nuhu! babu wani abu daya gilma, hakan besa sun saki jikinsu a gurin ba, sai da duhun dare ya shiga sannan suka fara neman abinda za su ci.

Ita dai ‘ya’yan itacuwa kad’ai ta iyaci, tana zaune tana kallonsu sun tada wuta sai gashe-gashe sukeyi da kallon ikon Allah! da kudirarsa, ace wai mutum ya gasa majici gafiya da sauran dabbobi marasa kyau yana ci a cikinsa.

K’auri da karni! duk ya cika gurin! dole ta tashi domin sauya gurin zama, domin mutukar tana shak’ar hayaki da kaurin dake tashi agurin zata iya amayar da abinda taci.

Ido ya bita dashi! be dauke ba har sai da ta samu guri ta zauna can nesa dasu, inda Allah ya takaita akwai hasken farin wata a gurin.

Ta jima a zaune a gurin tana sakawa da kwancewa! sai yanzu ta san ya rayuwa take, ta taso cikin kulawa da gata da komai na jin dadin rayuwa, tunda take bata ta’ba tsammanin cewa akwai ranar da za tayi rayuwa mai muni irin wannan ba! babban tashin hankalinta rayuwa da d’an ta’addah! irin wannan, duk abinda yake a kanta bai janyo masa ‘kima da mutunci ba, domin kuwa shine mutum na farko wanda yayi sanadiyar tagayyara rayuwarta, hakika ta tsorota da rayuwa da duniyar ma gabad’aya, A yanzu babban burinta ta samu ku’bta daga cikin wannan dajin, sannan tayi wa kanta al’kawarin ganin ta jefa rayuwarsa cikin kunci da tashin hankali kwantankwacin yanda yayi mata.

Saukar wani abu taji saman wuyanta, da sauri tasa hannu ta buge! ta mike tsaye! wata lafceciyar tsutsa ce ta fado daga saman bishiya.

Rintse ido! tayi tana kiran sunan Allah! kafin taji zirrrrrr a kan kafarta, tayi tsalle ta matsa gefe tana kallon gurin, ashe gabadaya gurin tsutsutsine suke yawo.

Jiki na wani irin rawa ta bar gurin, tana isa inda suke ta iske sunyi shimfida sun gatange gurin da itacuwa tare da rufe gurin da Net!

Tsayawa tayi a gurin ta kasa shiga, domin gabad’ayansu mugun haushinsu takeji! daga nesa ta hangoshi ya nufo gurin, d’auke kanta tayi tare da jan tsaki a cikin zuciyarta.

Koda ya iso gurin bece mata komai ba, ya kama hannunta! kallonshi tayi kamar za tayi magana sai dai tayi shuru, jan hannunta yayi suka shiga gurin.

Guri guda ya zaunar da ita, muryar rarrashi da kwantar da hankali ya aro yace.” Ki kwanta anan gurin nayi miki alkawai cewa babu abinda zan bari ya sami rayuwarki.”

A maimakon hakan ya faranta mata sai kawai taja masa tsaki! ta kawar da kanta tana zumbura baki!

Hakan da tayi ya bata masa rai amma sai ya danne! be dauki mataki ba ya fara kokarin barin gurin, ta bude baki da fadin.” Mamugunci! insha Allah sai naga karshenka.”

Maganar ta bashi mamaki mutuka! sai ya juyo da wani irin murmushi a fuskarsa ya nuna kirjinsa da fadin.” Me yasa kike so ki kaga bayana.”?

Ta zabura! da fadin.” Saboda kai din azzalimi ne macuci.!!

Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta” Saboda kai din azzalimi ne macuci.”! to wai shin da take kiransa da wannan sunayen wane irin zalinci yayi mata tun farkon had’uwarsu?

Still murmushin ya sake kafin ya furzar da iskar bakinshi, cikin gaggawa ya fita ya bata guri domin yana ji idan ya kara second a gurun zai iya nakastata.

Ya jima yana fesar da hayaki kafin ya samu sassauci a zuciyarsa, zazzafar ajiyar zuciya ya sauke! yana me sake jin sautin muryarta na amsa kuwwa! a kunnanta a cikin kunnuwansa, tunda ya taso lokacin kuruciya da girma gwargwamaya yake da Maza! bai ta’ba sanya mata a cikin al’amuranshi ba, saboda sanin hallayarsu! yana da tausayi mussaman akansu amma baya yarda da raini daga garesu, mace daya ce yake jinta a cikin zuciyarsa, domin duk ta tara abinda yake da bukata, hankali nutsuwa ilimi tarbiya da sauransu, ita kad’ai! yake ji a zuciyarsa zai rayuwa mai tsayi da ita, ya kai ma’kura a gurin iskancin da yarinyar nan take masa, yana tausaya mata amma ya lura ita bata gani ta daukeshi a matsayin macuci! to yana ganin zai fita daga harkata domin ya samu zaman lafiya. tare da gudanar da aikin dake gabanshi.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button