GOJE

GOJE 33 and 34

Ad

_____

Tsaf ya fahimci inda maganar ta dosa, murmushin takaici yayi kafin yace.” Banyi mamakin jin wannan maganar ba domin duk mutumin da yake ‘kin ka, to babu irin k’azafin da ba zai yi a kanka ba, Asp wallahi tallahi! da naso keta haddin yarinyar nan da ba zata kai labari a hannuna ba, saboda na samu dama iri-iri a kanta amma sam ba wannan ne a gabana ba, burina shine na kubtar da ita, sai kuma sharri! ya biyo bayan alkairi.”

Yace.” Kwarai kuwa shiyasa a lokacin da take maganar na ‘karyata ta domin na san ba za ka aikata hakan ba, kawai dai tana neman hanyar da zata tozartaka ne.”

Yace.”Shiyasa ai nace kayi tafiyarka kawai Asp wallahi kaji rantsuwar musulmi ba naso na sake ganin fuskar yarinyar nan.”

Yace.” A haba dai kada ka tsananta da yawa abu ne mai sauki wannan ki
‘kiyayyar da kukewa junanku ta rikide ta zama soyayya irin wacce take da wuyar samu hakan na iya faruwa.

Ranshi ya ‘baci da jin haka tevur din dake gabansa ya buga! murya a sama yace.” Allah ya kiyaye Asp bana fatan Allah ya jarrabeni da soyayyar wannan yarinyar, kawai kayi min fatan alkairi ba irin wannan ba.”

Asp din yayi mamakin yanda maganar ta fusata shi, sai ya sassauta murya da fadin.” Colm dwon mana ka samu nutsuwa, wannan maganar dana nake maka a yanzu ba wai nace lallai hakan ya tabbata ba, kawai a jikina nake jin kamar akwai wani abu da zai ratsa tsakaninka da yarinyar domin anyi irin haka ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, kiyayya ce ake wacce tafi wannan daga karshe kuma sai ta rikide ta juya matsananciyar soyayya.”

“Mtsssssw!!!! Yaja wani dogon tsaki kafin ya kashe wayar ya jefar saman tevur tunda ya had’u da Asp bai ta’ba ‘bata masa rai irin yau ba……..Shi kuwa Asp din sakin baki yayi da wayar a hannunsa yana mamakin al’amarin.

Da takaicin maganganun Asp ya isa gida, takalmanshi kawai ya iya kwancewa ya kwanta saman kujera ba tare da ya cire inform din dake jikinsa ba, rungume hannunsa yayi a kirji ya rufe idanuwansa yana hasaso kammanin yarinyar…………. ‘baka ce ba sosai ba, idan be manta ba tana da tsayi gami da cikar kirji da fadin kwankwanso, ‘kirar jikinta kenan, tana da manyan idanu da d’an k’arami hanci wanda ke tsatstsafo da gumi ako da yaushe, wannan sune kad’ai abunda zai iya tunawa a game da ita!

Yaja tsaki! tare da gyara kwanciyarsa, har yanzu maganar ce take cin zuciyarsa! shi kam a rayuwarsa me zai yi da yarinyar da ta nuna masa tsantsar ‘kiyayya irin haka, hanyar jirgi daban ta mota daban.

Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya bude idonshi tare da tsareta dasu, be tashi zaune ba yana daga kwance ya amsa mata, still idonshi na tsaye kanta, sai tace tunda suke bai ta’ba yi mata kallon kurrullah irin haka ba, duk sai ta tsargu dama ta shigo ne domin ta duba taga ya dawo ta kawo masa abinci, jikinta duk sai ya mutu sakamakon kafe ta da yayi da kaifin idanuwansa.

Ad

A sanyaye tace.” Yayana sannu da zuwa ashe ka dawo.”?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yun’kura ya tashi zaune yana kokarin b’alle botiran gaban rigarshi, yace.” Na dawo my dear nagaji ne shiyasa ban leka gurinku ba, ina so nayi wanka na huta tukkuna.”

Cike da kulawa tace.” Sannu ya aikin? bari na had’a ma ruwan wanka ko.”? yana kokarin cire rigar daga jikinshi yace.” Godiya nake Allah yayi miki albarka.” Cike da jin dadi ta amsa, kafin da sauri ta kama hanyar dakinsa, ido ya bita dashi har ta shiga dakin ya girgiza kai a fili yace.” Wannan itace matar aure mai cikakkiyar tarbiya nutsuwa sanin ya kamata yayi imani ko zuria ya had’a da wannan yarinyar ba zaiyi kaico ba.

Ta fito falon ta sameshi daga shi sai vest wacce ta matse shi da gajeran wando domin ya cire gabadaya kayan jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta kunyar had’a ido take dashi, ganin haka yasa yayi murmushi ya tashi ya bar gurin, da sauri ta dauki inform din ta kai masa daki ta rataye masa kafin ta bude wardrobe ta dauko masa ‘kananun kayan shan iska, ta ajiye saman gado da sauri ta fita daga dakin. tana jin wata annushuwa a cikin ranta, yau ta d’an fara ganin alamun sonta acikin ‘kwayar idanuwansa….

Free pege zai ‘kare a pege 40 ga masu bukatar wannan littafin suyi payment domin karanta littafin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kada mugunta!/hassada!/ ganin k’yashi! ya hana ku biya, ku jira na sata ku karanta, wallahi tallahi hakkin wani masifa ne! bala’i ne! muyi kokarin nesanta kanmu da haram! duk kankantarta!

Ad

_____

Previous page 1 2

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button