Labaran Kannywood

“Yar Makaranta Sayyada “Yar Mata: Mutane sun cika da mamaki da ganin Hoton Sayyada da Adam A Zango bayan shekaru da dena jin duriyar ta

” “Yar Makaranta Sayyada “Yar Mata Mai Tarbiyya Sayyada Sannu Autar Mata”

Mutane sun cika da mamaki bayan ganin hoton fitaccen jarumin Kannywood Adam A Zango tare da wata yarinya wadda akayiwa laqabi da Sayyada a wani fim a shekarun baya da suka shude.

Sai dai wasu suna ganin hakan a matsayin girman dan mutum babu wahala.

Wasu kuma na ganin ai haka jarumin yasha wahala da dawainiyar Ummi Rahab daga karshe kuma suka farrake.

Wasu suna ganin ko dai itama yarinyar dawowa Kannywood tayi tunda dai bisa dukkanin alamu hakane domin ga Adam A Zango sanye da kayan “yan sanda.

Haka dai mutane da dama suka cigaba da bayyana ra’ayoyin su akan hoton Sayyada din tare da Adam A Zango.

 

Ba tare da bata lokaci ba zamu sanya muku bidiyon domin ko zaku tuna duba da yawan shekarun da aka kwasa.

Kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su.

Sayyada Yar Makaranta tare da Adam A Zango
Fim din Sayyada,ko kun tuna?

 

Ga bidiyon nan:

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button