FARHATAL-QALB

FARHATAL-QALB 8

PG:8

        ××××.      ××××.     ××××. 

Da yaa amsa sunan gidah, Gidane na yan boko da tsantsar aqidar musulunci. Babu batun kyamata ko tsangwama irin na wasu masu hannu da shuni. Suna da temako da kuma kyautatawa marasa karfi. Farfesa Adams Nasser shine mai gidan na su. Matan sa biyu kamar yadda ta gaya mana. Kishiyar tata ita aikin alkalanci take. Kuma itace matar sa ta fari. Tanada yara biyar: Basher, Saani,. Abubakher ,. Sai mata guda biyu da Jannat da Yasmin . Ita kuma Hajia Hameedah wadda mukaje wajenta tanada yara hudu: Zayn shine na fari, Sai Nadra da Nassem sai autan ta Muhammad. Suna ce da shi Moha ai kunji ma ta fada. Suna da gida a Abuja su kanje can suyi hutu su kan kuma futa zuwa wata kasar. Dama can a baya a kasar wajen suke daga baya suka dawo nan din. Kusan dukkanin iyalin nasu ma suna ketare. ….” Cewar Indo dake labarta musu komai.

“Ah lalle Masha Allah! Tabbas sun san darajar mutane. Dan mungani da idanun mu. Gaskia batada matsala matar nan. Gata ba bahaushiya ba kuma .” Najan isubu ta fada tana jinjina kai.

“Gaskia babu kam. Allah ya kara daukaka, Aamin ” Inji Umma Hadiza

“Aamin dai. Toh kunga dai yadda unguwar tasu take ma, Su ba shigaa harkar makota suke ba ma. Bare akai musu gulma da munafurci. Shekara ta nawa da su. Wallahi ‘daga murya wannan basu taba mun ba. Daga ita har abokiyar zaman ta ta. Kuma mijin nasu ma wallahi bakuga kirki ba. Allah ni dai haduwa ta da su. Bazan iya kasafce muku alkhairin dana samu a tattare da su ba. Shi mijin na su dan Sudan ne shi da matar tasa ta farko. Ita kuma Hajia yar masar ce me suke ce mata a turance. Wannan. Kinji sunan. Ya yake ma? Yauwa ijif (Egypt) To shi…”

“Ki ce du larabawa ne?” Najan Isubu ta katse Indo.

“Ina kai ku. Ai bangama ba.”

“Ai yo ho… Yi hakuri. Cigaba .”

“Yauwa shi mai gidan na su. Mahaifiya ta sa bahaushiya ce. Mahaifin sa kuma balarabe. Hajian tacemun usuli. Mahaifin nasa ne aka turo shi ofishin jakadanci da ke nan reshen najeriya. To anan Allah ya yi auren sa da mahaifiyar ta sa. Su kaita hayayyafa. Har shima dan na su ya auro yar Sudan. Wai sun hada jini ma da matar tasa ta farko. Sai kuma Hajia da ya kara a ta biyu yar ijif (Egypt)…”

“Masha Allahu! Kai arziki yayi. Ubangiji Allah ya wadata mu da shi Aamin.”

“Aamin Yaa Rabbi. Kuma gwanin ban sha’awa ma sai kunje auren dangin su.”

“Haba dai? Ganima kala kala ko?” Cewar najan Isubu tana hasaso yanayin a zuciar ta

“Habawa haduwar ma ta karshe. Dangin su gwanin ban sha’awa wallahi. Kuma auren da suke yi auren junan su suke. Ma’ana auren zumunci.”

“Yo ai dole. Yadda suke da tushe me kyau ga su labarawa ai dama ba zasu iya auro wani tsatson ba “

“Gaskia Masha Allahu. Auren gidah suke yi. Harta bukukuwan du irin na larabawa dinnan suke yi. Harda su shayi ake rarrabawa. Ke fa da mun jima a gun Hajia shayi zakuga tazo ta babbamu. Shayin me wani irin gard’i da dad’i. Wani irin kamshi na larabawa yakeyi. Kai arziki yayi “

“Habawa. Bari Indo, Ai bakiga yadda idanuwana ke hasaso dukkanin abubuwan da kike fada ba. Allah ubangiji yasa arzikin ki ne yazo Hadiza “

“Aamin Najaatu. Tare da ku baki daya. Nagode muku. Allah ya saka da alkhairi Amin.”

“Tabbas inde kika rike gaskia da amana zaki ji dadin zama da Hajia wallahi. Dan kinganni nan yadda kukasan yar dangin su wallahi haka suka dauke ni. Kowa ya sanni. Lamarin sai godiar mai sama. Ai shi yasa da Naja ta gayamun halayen ki nace to Alhamdulillah komai yazo a dai dai.”

“Nagode Indo. Ubangiji Allah ya saka da alkhairi. Allah ya biya muku dukkanin bukatun ku aamin Aamin.”

“Aamin Hadiza . Amin”

Cigaba da hira sukayi suna tafiya, Indo da ke gidan ta abayan unguwar su take ta gangaren makabarta. Hanya daban tabi bayan sunyi sallama. Hadiza ta sake mata godia har Indon ta bace daga ganin su.

“Naja nagode. Nagode Allah ubangiji ya buda muku kofofin alkhairin sa. Nagode kwarai. Wallahi na rasa yadda zan muku godiar ma.”

“Kayya Hadiza. Da girman Allah ki dena godiar nan haka. Wallahi ta isa. Ko ba ta kanmu ba wallahi idan Allah yayi kinada rabo da su dole zaki je gidan. Haka Allah ya rubuta ya kuma tsara. Dan haka ki bar godiar nan haka.”

“Toh ungo wannan kara akan naki.” Umma hadiza ta shigaa kiciniyar kunce ledar ta.”

“Mts! Wallahi Hadiza idan kikai wani abun yadda kikasan a hau ki da duka wallahi. Meye hakan fisabilillahi da girman ki? “

“Naja kar muyi haka da ke.” Cewar Umma hadiza cikin karshen gaskiyar ta.

“Sai kiyi tayi kuma.” Tayi gaba abunta. Umma hadiza ta bita da sauri .

“Naji na dena tsaya dan Allah.”

“Yauwa yanzu kika yi magana. Muje ki sayi mai da su magi ki dafe muku kazar nan Hadiza. Kuci da biredi ko ki dafe muku taliya ku na ci kuna yagar naman.”

“Insha Allahu Naja.”

“Sannan inason jan kunnen ki dama. Don nasan ke zuciyar ki daya zaki saki baki ki gaya musu komai “

“Insha Allahu Naja. Ina sauraron ki”

“Yauwa. Karki soma fada musu yadda kukayi da Hajia. Kya iya ce musu dai tafiya zasuyi sai sun dawo zaki fara aikin.”

“Tam insha Allahu. “

“Yauwa. Sai kuma karki soma gaya musu adadin kudin aikin da za’a dinga biyan ki. Daga ke sai su kamal kawai. “

“Insha Allahu haka za’ai.”

“Yauwa. Kin fini sani dai sarai halin surukar ki da kishiyar ki . Muddin suka ji zancen kudin aikin ki kema kinsan abunda zai biyo baya . Bayan kin zamar musu saniyar tatse. Dan kuwa kema kinsan ke zasu barwa dawainiyar komai nasu… Dan haka ki shiru da bakin ki. Dan abunda kika samu idan kinyi niyya kya iya ba su. Shine zancen da zan ja ki da shi dama.”

“Insha Allahu haka za’ai……”

Suka jera suka nufi wajen mai sayarda mai da kayan abinci. Dake najan Isubu mijinta na da dan rufin asiri. Da zai tafi ya saya musu komai sai dan abunda ba a rasa ba. Don haka magi kawai ta saya da curry. Umma Hadiza kuma ta sai su man kulli da magi da curry da sauran spices.

Suka yiwa juna sallama. Umma hadiza ta shigaa gidah. Yayinda Najan Isubu tayi hanyar gidan ta….

ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button