GURBIN IDO

GURBIN IDO 23

Safiyyatulkiram: 23

Sallamar jauro ita ta kubutar damaimunatu daga tulin tambayoyin inna furera,shikam karon farko ya gane maimunatun,yayin data miqe kamar yadda ta saba a baya tana masa sannu da zuwa gami da karbar ledar hannunsa.

Yana shirin xama ta duqa har qas ta gaidashi,ya amsa cikin nuna kulawa,tamkar diyarsa gaje

“Baki tafi gida kin kwanta ba?” Wani kallo inna furera ta jefeshi dashi a fakaice

“Akwai inda yafi nan ne?,naga dai nan dinne gidan”

“Qwarai kuwa”

“Tun daxun ma nake tsimayin shigowarka…”

“Eh nadan tsaya ne muna magana da labaran,ashe bidar alkhairi ne ya kawosu garin ma” sosai inna furera ta bada hankalinta ga jauro

“Kamar yaya kenan?” Huffijen qafarsa ya cire,ya zauna sosai yana tanqwashe qafafunsa

“Wato Allah ne kadai yasan alkhairi dake tattare da yarinyar nan,uwar dakinta hajiya anni,ita tazo ta shaida mana cewa,suna so mu basu dama zasu turo a nemawa jikanta auren maimunatu”

   Kamar ya dauko qaton qarfe ya doka mata a tsakiyar kai haka inna furera taji,sai taji gaba daya ta daina ganewa,kwanyarta ta dode

“Ban gane abinda kake magana akai ba jauro,kace me?”

“Nace gidan da taje aiki,uwar dakinta tazo nemawa jikanta izinin turo magabatansa neman auren maimunatu” zumbur kamar wadda kunawa ta harba haka nan ta miqe,take ta hada zufa da kuma gumi,zallar tashin hankali yana nuna kansa saman fuskarta

“Wallahi wallahi ba zata sabu ba,aini ba haka mukayi da ita ba,ba kuma abinda na turata yi kenan ba,ni arziqi na turata nema mana bawai aure ba,hasalima ni ban shirya aurar da ita yanzu ba…..”saita waiwaya bangaren da maimunatun take

“Don uwarki don ubanki dama karuwanci kika je yi?,aure nace kije ki samo ba kudi ba?,shegiya mayya,kinje da idanunkin nan kin lashe kurwar dan mutane?” Inna furera ta fada cikin hargowa da fada matuqa

“Ah…..kinga dakata furera,me kikeson kice ne?,…..ke maimunatu,tashi ki wuce daki wajen ‘yaruwarki ki kwanta” ya baiwa maimunatu data cure waje guda saboda tsoro umarni,ta manta da irin wannan rayuwar sam,ta manta rabon da wani ya daga murya a kanta sai yau,sai ta miqe da hanzari ta durfafi dakin gaje,duk da shima batasan me zata taras ba.

   "Zauna furera" jauro ya bata umarni kai tsaye yana dubanta

“Na zauna nayi me?,aini na gama magana,babu uban da ya isa yasa maimunatu tayi aure yanzu ehe” cikin matuqar mamaki yake kallonta

“Awala hankali furera?,wanne irin batu ne na wai maimunatu ba zatayi aure ba?,ina cewa nan tanadin auren gaje kike yi?,sai kuma yanzu zaki ce ita maimunatu ba zatayi aure ba?,…..to……to,na gama fahimtar inda kika saka gaba,tsaf na karanceki,to bari kiji,idan kin saba watangaririya da rayuwar yarinya,idan kin saba saka rayuwar yarinya a gaba kiyi duk yadda kikaso ina zuba miki idanu,to wannan karon tayi qaura,kuma baki isa ba,yadda suka zo neman izinin auren maimunatu zasu sameshi kuwa da yardar Allah,muddin bake kadai kika rage a doron qasa jinin shatu da maimunatu ba” ya miqe cikin tsananin fushin data jima bataga yayi ba,sai tabi bayansa da kallo tana cewa

“Me kake nufi jauro?” Ko tankata baiyi ba,yasa kansa abinda ya wuce dakinsa.

  Komawa tayi jabar ta zauna a wajen tana fidda zazzafar iska daga bakinta,kwanyarta ta cika taf da tunani,mutanen nan koda bataje ta ganewa idanunta ba tabbas tasan masu tarin arziqi da wadata ne,ta yaya maimunatu zata shiga cikin irin wannan ahalin alhalin gaje na zaune a qauye?,duk da babbar sa'a tayi na samun himu cikin qauyen?,shawara ta qarshe da zuciyarta ta bata shine,ta tunkari jauro kai tsaye,ta fayyace masa abinda yake zuciyarta,ai shima gaje diyarsa ce,kuma bazaizo ci gaban maimunatu fiye da diyarsa ta cikinsa ba.

    Wani kallo ya dago ya watsa ma furera sansa ta kammala bayananta

“yanzu na fahimci bayan ciwon mugunta da hassada dake damunki,harda ciwon hauka kadan a kwanyarki,toki sani…..ni ba qaramin mutum bane,yadda suka furta maimunatu babu abinda zai sauya wannan in sha Allah saidai idan sauyin daga wajensu ne” maganar ta sake harzuqa inna furera matuqa,ta miqe cikin masifa

“Nidai bansan ko dakai.akayi cikin maimunatu ba,banda haka,ta yaya ga jininka zaka ajjiyeta kafifita wata bare akanta?”

“Duk yadda rai da zuciyarki ya baki haka ne” abinda jauro yace da ita kenan,don ya fuskanci tayi nisa bata jin kira,ba zata fuskanci duk wani bayani sai abinda zuciyarta da shaidan suka qawata mata.

Yadda maimunatu batayi cikakken bacci ba a daren saboda maganganun da gaje ta dinga gasa mata har zuwa sanda bacci ya dauketa……haka itama inna furera bata runtsa ba,Kuka irin wanda maimunatu ta jima bata yishi ba tun barinta gidan a yau ta yishi,tana cike da tantamar anya inna furera yayar daadarta ce da gaske kuwa?,sam ko daya cewar da tayi ba zata auri jika ga anni ba shine damuwarta ba,a’ah…..yadda a kullum ta bude baki mugunyar kalma ce ke fita daga bakinta a kanta,bata taba ambatar alheri a kansu,daga ita har marigayiyar mahaifiyarta,ta duba ta kuma dubo amma ta gaza gano laifi guda daya tak da suka yiwa inna furera wanda suka cacanci wannan abun daga gareta,bata damu da zantukan gaje ba dama ta saba dasu,amma qiyayyar inna furera tana mugun taba mata ruhi.

Ita kuwa inna furera kaf a daren tunaninta ya tafi ga yarda zata turgude maganar auren maimunatu ne,idan da hali ma ta maida akalar zanca ya koma kan gaje,bata damu da koma wanne irin kallo daadar himun zata yi mata,indai suka haye wannan bigiren shikenan komai yazo qarshe a wajenta.

Shawarar qarshe data yanke da ita ta kwanta,ta kuma miqe tun kiran assalatun farko ta buga sallarta,ta zauna tana dakon kira na biyu ta fice a gidan.

Sanda ta fita din kuwa ko sallamewa daga sallar ba’ayi ba adan masallacin dake tsukin rugar tasu,sai a hanya dab da isarta gidan bappa labaran aka idar,ta kutsa kai gidan babu cikakkiyar sallama saboda bataso daadar tasan tazo,ta nufaci dakin yuuma kanta tsaye.

Dai dai lokacin da yuuma ke tsaye tana shirin zare hijabinta daga jikinta bayan ta idar da salla,yayin da anni ke saman abun salla tana lazumi itama.

Tsorata yuuma tayi da ganin furera a irin wannan lokacin,ta matsa da baya tana amsa sallamarta sanda ta shigo ta yiwa kanta mazauni,tsaf anni ta gane matar,don haka bata katse lazuminta ba sai data cika dari cif sannan ta sauke carbin bayan ta shafa,inna furera ta fara gaidata cikin tsantsar ladabi,anni ta amsa tana dubanta a kaikaice,don tana da tabbacin kome meye ya futo da ita da asussubar fari to ba alkhairi bane.

Rai rai ta fara jerowa anni maganganun da tun a jiyan ta gama shiryawa kanta game da maimunatu,da dukkan wata siga da zatayi baqi a idanunta,anni na kallon ta,bata ce da ita komai ba hakanan bata dakatar da ita ba,har sai data dasa aya

“Kin gama?” Anni ta tambayeta

“Eh….to shine naga gwara na shaida miki,tunda dai kinga amana ce ta hadamu,bai kamata na rufeki ba kada ubangiji ya tuhumeni,ni kaina yarinyar kaffa kaffa nake da ita da kuma neman maganin tsari daga maita,shine fa kikaga mun kawo har warhaka lafiya lau bata taba kowa a cikinmu ba”

    Sosai yuuma dake zaune daga gefe ta cika tayi famm,fata take annin ta bata dama ta wanke furera mara tsoron Allah data iya kaikaicewa ta yankarowa jininta mummunar qazafi da qarya har haka saboda kawai zallar hassada da baqar zuciya

“Yanzu me kikeso ayi kenan?” Anni ta tambayeta cike da gatse,wanda ita furera bata fahinta ba,sai murna data saukar mata,ta kuma karkace ta gabatar mata da gajenta,bayan ta gama kodata

“Kinga dakata baiwar Allah,kiyi ta kanki kinji,banason wannan soki burutsun,banda ma baki da hankali……..idan maimunatu mayya ce ku zaku kubuta ne?,ko ce miki akayi ba wanda yasan alaqarku da ita?” Gumin tashin hankali ne ya yankowa furera,ya akayi wata halitta tasan da wannan?dama kowa kallonta yake kenan?.

“Ai….to,ai dama ita din…..maitarta ta can jikin kakarta ne…..bawai daga ubanmu bane,daga kakarta ne……sai….sai ta tsotsa daga nonon uwarta itama”

“Ke!……ki kiyayeni fa?,wallahi tallahi ina sake jadda miki kiyi ta kanki,yo banda tambadewa irin taki,ina ake irin haka?,to bari kiji na gaya miki,ki kama.kanki,idan ba haka ba in na tashi tafiya billahuwallazi kaf garken maimunatu da uwarta da kika danne kike qafafa dasu sai nasa anyi awon gaba dasu,gwara ki.saita kanki aci gaba da tafiya ahaka,wata shari’ar sai a lahira” sosai jikin inna furere ya dauki bari jin ana shirin yi mata bankada.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button