GURBIN IDO

GURBIN IDO 23

Ta tambayi kanta Wanne tsinannen ne yake fitar mata da sirri haka?,anya ba daadar himu bace?,babu shiri ta kwashi takalmanta a hannu ta fice don anni ta fara daga mata murya.

Abinda ya sake kada mata hanji kuma shine kallon banzan da daadar himu ta watsa mata sanda sukayi kacibus a tsakar gidan,saita qarasa daburcewa,ko taji abinda yake tafe da ita ne?,don haka ta hadiye gaisuwarta tayi waje,don ta soma zargin daadar cikin ranta,saboda tasan kaf fadin karkarar ita kadai tasan da wannan maganganun.

Tunda ta idar da sallar asuba tana zaune bata koma ba,lokaci lokaci idanunta suna kan gaje daketa sharbar bacci abinta,babu shiri ko niyyar tashi tare da ita bare ta sauke farali,har yanzu halindai ashe yana nan ta raya hakan cikin ranta.

Haka kawai tayi sha’awar tashi tayi irin ayyukan data saba yi a baya,don haka ta miqe a hankali,ta zura hannunta inda ta cusa takalmanta watannin baya sanda zata bar gidan,cikin sa’a ta samesu,murmushi ta sake,duk da sun ratattake,suna tuna mata da abubuwa masu yawan gaske da suka gabata,saita miqe dogayen qafafunta da a yanzun suka qara haske suka kuma yi luwai luwai ta zura su,sannan tayo waje.

Tana fitowa jauro na dawowa daga salla,ta gaidashi cikin girmamawa ya amsa mata cikin kulawa yana tsokanarta kan yau ta tuna kwanan ruga,tana murmushi ta soma aikin gidan,sai gashi ya fito yana tambayarta inda fureran taje

“Ban sani ba kawu,yanzu nima na futo” sai ya jinjina kai,har yayi gaba ya dawo yace mata ta aje aikin ta koma ta kwanta

“Ba komai kawu,hakan yana min dadi” kansa ya jinjina cikin tausayi da qaunar yarinyar,ya shige dakinsa,babu jimawa ya fito da koren hirami na maza jikinsa daya yafa,ya wuce dakinsu,tana jinsa yana rafkar gaje kan ta tashi tayi sallah,kana yayo waje yana ce mata zaije ya dawo,tayi masa a dawo lafiya tana ci gaba da ayyukanta,saidai har ta gams gaje bata futo ba.

Ganin ta gama saita wuce kanta tsaye zuwa haggo,tun daga nesa take kallon dabbobin cikin kewa da shauqi,tayi matuqar kewarsu ba kadan ba,amma abinda yadan taba ranta ya kuma bata mamaki,yadda yawansu kyau da tsaftarsu suka ragu sosai,taga sabbin fuskoki dake nuna an hayayyafa,to amma indai hakane me ya hana su qara yawa?.

A nutse taje ta kwance wadanda suke daure,ta zari sandar data gani a jingine a wajen,ta kuma soma korasu cikin nutsuwa da tsohuwar qwarewa zuwa makiyaya.

Kusan za’a iya cewa kallo ne ya koma sama,duk inda ta wuce dai ta kwashi fiye da rabin hankalin mutanen wajen,wasu da yawa basu ganeta ba,suna mata kallon baquwar fuska,don atamfa ce a jikinta dinkin doguwar riga,ba kayan saqi ba.

Dukka wajen data saba ta’ammali dashi a wancan lokacin sai data tsaya a wajen tana tuna komai daya wuce,daga qarshe ta dangana da qasan bishiyarta,wadda a yanzun ta qara yawa da rassa,tana shirin zama taji sallama da muryar da ta kasance sananniya a wajenta.

A nutse ta daga kai tana amsa sallamar,bafullatanin saurayin nan daya taimaki rayuwarta a shekarun baya,himu,shine yau tsaye a gabanta bayan shudewar wasu watannu masu tsaho,yana nan a yadda ta sanshi,saidai kuma yayi rama ba kamar a baya ba da yake da cikar jiki…..Ya tsinke sosai ya qara tsaho,har yanzu wannan murmushin nasa yana nan saman fuskarsa,sai ya tako daura da inda take zaune,ya zauna saman dutsen daya saba zama shima

“Maimunatu….’yammatan birni” maganar data sanya siririn murmushi kubuce mata,ta kuma soma gaidashi,ya amsa mata cikin matuqar kulawa

“Tafiya haka katsam babu bankwana maimunatu?,saidai na laluba naji wayam babu ke?” Har yanzu himu nada wata kima da daraja a ranta,yana kuma cikin jerin mutane masu muhimmanci a rayuwarta

“Kayi haquri,haka tafiyar nima tazomin,kuma a sannan bansan inda zan ganka ba” kai ya gyada,shima yasan da wannan

“Hakane,to yaya bayan rabuwa?,duk da alamu sun nuna komai yana tafiyar miki yadda ya kamata” ya fada kansa tsaye yana hango canji qarara daga wajenta,canjin da yasa ya saare,ya sake kuma sallamawa bayan kunnuwansa sunji ana zancan aurenta da wani.

        Mintuna kadan ya miqe bayan zaman shuru da sukayi shi da ita

“Sallama nazo muyi,saboda nasan ba lallai bane na sake samun dama irin wannan,ban taba kawowa a raina zan rasaki ba,sai gashi qaddara ta wanzar mana da hakan,duk da zuciyata ta soki matuqar so,bazanyi jayayya ba,saboda bansan me Allah ke nufi da hakan ba,kin cancanci samun kyakkyawar rayuwa fiye da wadda nake miki tanadi,ina miki fatan alkhairi a dukka rayuwarki maimunatu” daga haka ya juya ya soma barin wajen.

       "Na gode sosai" abinda ta iya gaya masa kenan tana bin bayansa da kallo,tausayinsa da kuma wani irin yanayi na cika mata zuciya,har ya bacewa ganinta.

     Ko awa guda bata rufa ba inna furera ta aiko kan ta tattaro mata dabbobinta ta dawo mata dasu,tayi hakanne saboda tsoron daya cika zuciyarta kan kada ta rasa dabbobin data qwallafa rai a kansu,fitar da maimunatun tayi dasu sai take ganin kamar wani shiri ne.

[

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button