GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 31-40

31*
Arewabooks@Mamuhgee
Sake Shan jinin jikinsu dukkaninsu sukayi Jin cm yace sufito atafi gida Nan suka sake tabbatarda ba lafiyaba
Amma Kuma bilyamin qanin Anty Hafsat ya tabbatar musu da an daura aure,
To Kuma menene matsalar?
Sudai koma menene suna ganin da sauki idan har andaura auren Inayah da Dr Abdul dinta.

Ita kanta Inayah data dawo hayyacinta tuntuni zaune take tana jiran ta Inda labarin halinda aurenta yake ciki zai bullo.

Lokacinda bilyamin ya sanar dasu cewa andaura auren wani irin Al’amari taji atattare da ita shi ba farin cikiba hakama ba baqin cikiba
Tadaisan jikinta ya mutune kawai Dan haka daqyar ta iya sauya Kaya kaman yanda su Anty Hafsat suka takura Mata sbd Ango na tafe da jama’arsa suyi hotuna takuma gaisa da abokansa da zasu bi jirgi a ranar su koma.

Tafiyar su Anty Hafsat shine ya fara daga hankalin umma yaganah harma da Inayah Dan haka da kanta ta Kira cm din a waya tace Inayah tace Dan Allah abar Mata Hafsat da Safnah har zuwa anjima.

Bai Musa ba yabar Anty Hafsat da Safnah Dan haka gidan yayi tsit daga umma yaganah sai Anty Hafsat da Safnah da Neesah
Dr farhat ma ta tafi gida sai zaa wuce da Inayah din tace akirata.

Babu Mai wata doguwar walwala acikinsu sbd sudai anbarsu a duhu basusan meyake faruwaba sai jiran tsammanin zuwan Ango da jama’arsa suke Amma basuga alamar hakan Zata faruba ga wayarsa da Inayah ke Kira kaman zata zare Amma batama shiga kwata kwata.

Sanin Abbi yadawo yasa ta miqe jiki mace ta nufa gefensa tana sake trying din Abdul.

Kodata Isa knocking daya tayi tabude kofar tashiga daukeda sallama Mara sauti sosai.

Baya Palo da alama Yana bedroom dinsa Dan haka ta zauna kan kujera tana sake trying din Abdul.

Tunanin Kiran ummansane ya shigota ta nema numbern umman aikuwa tafara ringing.

Harta katse baa dagaba Dan haka ta fara rubutawa Abdul text.

Kofar bedroom dinsace ta bude Dan haka ta dakata rubutun tareda dagowa tana kallon kofar.

Sanye yake da ash Lululemon wears navy blue dasuka fidda hasken fatarsa sosai da alama wanka yayi ya shiryo cikin kayan Dan samun nutsuwa,
Qamshinsane ya gauraye palon take ya qaraso da yimata kallo daya yanajin wata qululuwar damuwar auren da aka daura Yana dawo Masa.

Cikin boye damuwarta da Yar sakakiyar murya tace”

Abbi kadawo Ashe tun dazu?
Abbi Ina Heart ya….kasa qarasawa tanajin nauyin qarasa zancen sbd ita wani lokacin mantawa takeyi da kunyar fadan wani zancen.

Dan juyowa yayi kadan ya kalleta ganin damuwa a tattare da ita cikin dan yanayin kawar da zancen Kai tsaye yace”

Abdul na asibiti ya Dan samu attack ne aka wuce dashi asibiti.

Zaro ido tayi cikin tashin hankali da firgici Amma ganin ba fuskar Kuma wata tambayar agurin Abbi yasata miqewa ta silale Takoma.

Koda ta Isa a tsattsaye ta taddasu kowanne ba acikin cikakken hayyacinsaba,
Tashin hankali da firgicin data gani ataredasu duka yasata bude Baki da qarfi cikin firgici tace”

Badai Heart wani abun yasamaba kuma daga asibiti???

Umma yaganah kanta yakasa daukan abinda CM yafadawa Hafsat a taqaice na cewa A MAJEED shine mijin da aka daurawa Inayah aure dashi yau.

Wani irin zufa takeyi tanajin kaman iskar dake gurin Bata isarta Dan haka da sauri Neesah ma dake cikin tsananin shock ta Kama umma yaganah sukai daki taqara Mata AC tareda bude suka windows tana cewa”

breath, just breath kada ki Bari Jan numfashi ya tsaya Miki kiyi kokari kijasa.

Kasawa umma yaganah tayi Saida Inayah tashigo dakin tana kallonsu a haukace tana cewa”

Dan Allah ku fadan abinda yake faruwa,
Wane tashin hankali ne zaisaka umma wannan halin?
Anty Hafsat is crying,
Kema Neesah sai zare Ido kikeyi Kun kasa fadamun komai,

Kuka ta fashe dashi tana cewa”

Idan Heart ne ya rasu Dan Allah ku fadamun.

Kasa riqe maganar bakinta Neesah tayi cikin mamaki da qin yarda da abinda sukaji tace”

Inayah Abbi ne fa ya aureki,
Dashi aka daura auren wai,
Shine mijinki yanzu,
Dama akwai aure tsakanin uba da ‘ya??….

A jere take Watso kalaman sbd takai kololuwar kasa danne mamakin firgicin dake ransu ita nata kalaman ne suka Riga na kowa fitowa a hargitse.

Kallon rashin fahimta Inayah ke Mata kafin ta kalli umma yaganah da duk tayi wani iri Dan kuwa CM bazai musu qaryaba,
hakama tafi kowa sanin MAJEED ba jahili bane bakuma mahaukaci bane da iliminsa
Idan harya auri Inayah hakan na nufin bashine ya haifetaba kenan tun asali….to wannan wane irin masifa ce Zata sakasa auran yarinyarda take matsayin ‘yarsa Koda ba shine ya haifeta ba tasan Dole ba auran dadin Rai ne yayiwa Inayah ba.

Anty Hafsat ce tashigo tana sake samun tabbaci daga uban mijinta Alhaji babbah cewa Inayah dai ba ‘yar MAJEED bace Kuma shine dai mijin daya aureta yau Dan haka suyi kokarin ganin sun tausar da ita batareda taqara Masa tension ba akan Wanda yake ciki yanzu.

Da rikitaccen yanayi Inayah ta maida kallonta kan Anty Hafsat data shigo dakin cikin kosawa tace”

Anty Hafsat meke faruwa dan Allah?Bazan iya daukan wannan shirun da kowa kemun ba,
Maganar Neesah ma Ni Sam bangane itama me take nufiba.

Ahankali Anty Hafsat takama hannunta suka nufi Inda umma yaganah take ta zaunar da ita itama ta zauna suka sakata tsakiya itada umma yaganah ahankali ta kalleta cikin sanyin murya tafara cewa”

Inayah bamusan komai dayasaba kokuma yazama sanadi komai for now Amma dai abinda yake gaskiyar zance shine aurenki da Abdulsamad Bai yiyuba Amma aure kam kaman yanda aka sanar Mana tabbas andaura Miki aure da…

Dan shiru tayi tareda kallon umma yaganah dake saurarenta itama Dan Hafsat din tafisu sani da fahimtar komai da kyau tunda itace tayi waya da mijinta yayi Mata bayanin komai hakama Alhaji babbah yayi Mata bayanin komai qarshema yanzu driver na hanyar zuwa daukansu su duka zuwa gurin Alhaji babbah din Dan shine kadai zai iya yiwa Inayah bayaninda kila Zata fahimta.

Kaman daga sama sukaji Inayah din tace”

Da aka fasa aurena da heart sai aka daura mun da Abbi???
Right?
Shine abinda kikeson fada mun?

Shigowar zubbi da sakon isowar driver daga can family house yasa Anty Hafsat dojewa amsa tambayar Inayah din Dan haka ba Bata lokaci takama hannun Inayah din Umma ba Bata jira komaiba ta sauko gadon tareda miqewa ta zari mayafi suka fito Dan kowa matse yake da a wayar Masa da Kai akan wannan sauyin lamari Mai wuyar ganewa.

Koda suka Isa gidan Alhaji babbah na masallaci sallar la’asar Dan haka Saida suka jira ya dawo a babban Palo Haj mama na sake yimusu nasiha a fakaice Dan ita saima taji tafi jin dadin MAJEED daya aure Inayah Dan kuwa da tun farkoma sun San bashine ya haifetaba baida alaqar Jini tako Ina da ita da tuni sun matsanta Masa ya aureta yafi fashe fashen aurenta da akaita Yi shima Kuma ga lokaci yaja Bai taba aureba ace haryanzu matsayin saurayi yake Dan haka Kai tsaye ya bayyanarda farin cikinta ana fada saidai Kuma ta tausayawa Inayah sosai ta yanda Rana tsaka Zata karbi zamanta ba ‘yar mahaifintaba datake tsananin so da kauna amatsayin ubanta ita daya.

Kusan Banda Inayah data kasa fahimta bare yarda har lokacin
Sun Gama fahimtar dai Abbi bashine ya Haifa Inayah ba Kuma shine mijinta a yanzu.

Duk sun gane wannan abinda basu ganeba shine meya Hana a daura auren da Abdulsamad.

Alhaji babbah na dawowa daga masallaci suka dunguma palonsa lokacin har CM ma ya iso Yana gidan.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button