GURBIN IDO

GURBIN IDO 24

“Okay okay fine…..zan dawo zanyi packing komai nawa zan bar gidan,but….. please anni,kada kiyi punishing nawa ta wannan hanyar,bazan iya zama da kowacce mace ba anni please” ya fada cikin kwantar da murya,tare da fatan zai shawo kan annin.

   Baki ta tabe daga can,dama tasan za'a rina,tasan halin ja'afar sarai,tasan komai zai iya faruwa,kuma dama bata tarki abun ba sai data shirya masa

“Kaga babu fa wannan zancan,an riga an gama magana da magabantansu,ba zaka maidamu qananan yara ba,kuma ba gidan mukeso ka bari ba,zaman aure mukeso kayi” zaman aure kamar wani mace?, Ya qiyasta hakan cikin ransa

“Anni,ki fahimceni mana,ta yaya za’a auramin mata har biyu bayan babu fahimtar juna a tsakanina da kowaccensu bare azo maganar soyayya wadda already nayi banning dinta”

“Zaku fahimci kawunanku a dakunanku ai” ya zuwa yanzu ranshi ya sake baci fiye da dazun

“Anni!” Ya kirayeta da murya mai kaushi kadan,wanda shi kansa baisan yayi hakan ba
“it will not be possible,ta yaya hakan zai yiwu?”

“Ahap gashinan kuwa?” Da gaske take ba zata fahimceshi ba,saidai ma idan bai wasa ba ta sake tunzurashi,don haka sai kawai ya yanke wayar da sauri,sannan cikin wani irin zafin nama yaja kujera guda daya gabansa ya zauna a kai bayan ya jefa wayar saman table din,baya ko tsoron ta fashe.

  Dukka hannayensa ya cusa cikin gashinsa yana yamutsawa tare da fadin

“No…no,it can’t…..it can’t…..am not ready…..am not ready to face it this challenge” ya fada cikin zafi,sai kuma ya sake miqewa,yana buqatar yayi magana da wani,sai ya janyo wayar yana furzar da zazzafar iska daga bakinsa ya soma laluben number ammansa,gab da zata shiga ya sauya shawara ya kashe,sai ya maida kiran kan jabir

“Where are you?” Ya tambayesa kai tsaye,tsabar bacin rai yama manta inda yace masa zaije,tunda jabir din yaji muryarsa yasan cewa akwai matsala,cikin ransa yake fatan Allah yasa ba depression mode dinsa ne ya motsa ba

“Am on my way,is there a problem?”

“Zaka dauki mintuna nawa?”

“Few” ya amsa masa a taqaice

“Okay,am waiting for you, please don’t stay long” bai jira amsarsa ba ya katse wayar ya sake jefata inda ya dauko,dukka hannayensa ya zura cikin aljihun wandonsa,yahau kai kawo tsakanin wannan bangaren zuwa wancan,wanne irin hukuncine wannan da zasuyi masa?,wannan auren aiko mace a wannan zamanin ba za’ayi mata shi ba,wadanne irin mata ne su kansu da suka dauki kasadar aurensa ba tare da sun gana dashi ba?,kawai sun amince da auren mutumin da bashi ya nema yardarsu ba?,anni tana tunanin akwai macen da zata cike masa GURBIN shaheeda ne?,babu?,sam babu,yanajin cewa daga kanta an gama haifar diya mace a duniyarsa,wadan nan matan data debo GURBIN IDO ne kawai,fanko ne,ba zasu taba zamtowa IDO ba wato shaheedansa,yayi imani da hakan har cikin zuciyarsa.

  Kafin jabir yakai ga isowa ya duba agogo sau babu adadi,a gaban idanunsa cave ta saukeshi,ya fito dauke da niqi niqin siyayya a manyan ledoji,sai a sannan yayi noticing wani abu,kwana biyun jabir fita yake siyayya kusan koda yaushe,kamar wanda ke shirin komawa gida.

     Sai daya shiga gida ya aje kayan sannan ya sake fitowa,kafadarsa ya dafa daga baya

“Meye haka ne man?” Waiwayowa yayi ya dubi jabir,idanunsa a sannan har sun kada sun sauya kala saboda zallar bacin rai,wanda ta nan ake iya gane qurewar bacin ransa

“Yanzu kamar ni?,kamar ni anni zatayi forcing dina akan aure?” Tuntuni ya shanshano komai,don yasan da komai din,ya samu labari,saidai baiyi gangancin shaidawa ja’afar din ba,ya zuba idanu yaga ya caftar zata kaya.

  Dubansa sosai jabir yayi

“That’s right….” Sosai maganar ta baiwa ja’afar mamaki,ta kuma sake qular dashi

“Like how? what are you trying to say jabir?” Ajiyar zuciya ya sauke,shima ya maida hannayensa aljihunsa

“Ja’afar,ka gaza nutsuwa ka karbi qaddarar rayuwarka kayi moving forward yadda ya dace…..”

“Yanzu qoqarin me nake?” Ya fada da zafinsa

“Yes,naga canji,kanata qoqarin maida harkokinka yadda ya dace,amma bata iya wannan fannin kawai ya kamata ka maida kai ba wajen gyarawa,ya kamata ka sake building a new family da zasu debe maka kewa,su sake maidaka cikakken mutum,abinda kai ka gaza yi anni ta tayaka ginashi,so bai kamata ka zargeta ko kaji haushi ba,a shawarce ka tsaya ka nutsu,ka yiwa abun kallo na fahimta,don’t upset please”

“Okay na gane,kaima kana goyon bayan abinda tayimin kenan?, wait…..waima wa yace musu a yanzun ina sa buqatar wata mace cikin rayuwata?,dolen sai na rayu da wata,a barni nayi rayuwata a haka mana,me na ragu dashi” jabir zai sake cewa wani abu ja’afar din yaja tsaki ya daukin wayarsa a fusace ya wuce cikin gida da sassarfarsa.
[

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button