GURBIN IDO

GURBIN IDO 36-40

“Kinyi qoqari sosai,ma sha Allah,wannan ne karonki na farko fa?” Ya fada cikin nuna qwarin gwiwa da kuma qarfafata,maganar tazo mata a ba zata,ta kuma bata mamaki,sannan kuma taji dadi gaki da sake samun qwarin gwiwa.

      Ta zaci gidan abbi zai kaita,sai taga ya wuce da ita gidanta,bata tambayi dalili ba,bayan ya aje ta tayi masa godiya,ta kuma bashi saqon gaisuwa wajensu anni,tare da roqonsa a kawo mata amna.

     Gyare gyare ta shiga yi,irin na mutumin da ya kwan biyu baya waje,sai data gama komai sannan ta sake wanka,ta kuma wuce kitchen ganin azahar har ta gota don ta samawa kanta abinda zataci.

     Har zata shiga ta tuna da unaisa,sai taga bai dace tana cikin gida ba amma batasan da dawowarta ba,ko banza ta girme meta a shekaru,wannan tunanin yasa ta karkata akalarta zuwa sashen unaisan.

      Knocking biyu aka tambayi waye,kai tsaye ta amsa da itace maimunatu,sai da aka dauki mintuna sannan ta bata izinin shigowa.

      Zaune take saman doguwar kujerar falon nata,ta miqe qafafunta akai tana shan lemon fata,da alama tun dazun a hakan take a zaune,kawai dai batayi niyyar bata izinin shigowar bane,kallo daya tayi mata ta canza fuska ta kuma kau da kanta taci gaba da kallonta ga tv.

      Koda ta gaisheta sama sama ta amsa

“Na dawo,nace bari na shigo na sanar miki” wata dariya ce ta zowa unaisa,ya tabbata ja’afar din mugun dan rainin hankali ne,hakazalika da biyu ya dauki yarinyar ya kaita makarantar kwana saboda ya raina ajinta da kwanyarta,to amma hakan yayi mata ita din,tunda ko banza kawo yanzun tana dan samun wasu sauye sauyen,duk da cewa ko sau daya bau taba hada dakin kwana da ita ba

“To yayi” tace mata kawai taci gaba da shan lemonta tana kada qafa gami da ci gaba da kallonta,ganin babu wani magana data sake hadasu sai maimunatun ta miqe zata fita

“Agwai” ta kirayeta da sunan da maimunatun tafita sanin me sunan yake nufi,sunan yadan sosa ranta,amma bata nuna ba ta waiwayo tana dubanta

“Am please idan kin tashi girkinki,ki dinga yi iya cikinki,wanda naci a baya ma shahada nayi,don ba abinci kowanne irin mutum nake ci ba,so ina da masu aiki,zasu dinga yin komai” kai ta gyada sannan tayo gaba tana bar mata dakinta.

      Ga mamakinta sai taji maganganun unaisa sun dan sosa ranta kadan,abinda tun tasowarta da irin cin zarafin data gamu dashi a rayuwa bata taba jinsa akan kowa ba,ko hakan yana da nasaba da zama dasu afra?,hakan na nufin ta fara sanin kanta da kuma sanin mene ne rayuwa?. Muje zuwa dai.

      Tunda ta dawo gidan bataga koda gilmawar J ba,abinda ko sau daya bai ɗaɗata da ƙasa ba,sau tari mancewa take dashi kwata kwata cikin rayuwarta,tasa litattafanta a gaba tana ta haddar hadisan data daukarwa malamin islamiyyarsu alqawarin zata kawo masa su kafin a koma hutu,da kuma izifin data diba shima zata daw da haddarsa,don hatta haddar qur'aninta bata bari ta tsaya ba,tana ganin wannan damar ta roqa alfarma,yake mata qari kuma tana kawo masa.

     Ta fannin boko ma litattafan da zasu sake inganta mata koyo da gane turancinta ta karba aro masu yawa daga library din makaranta ta taho dasu,wadan nan abubuwa sune abokan hirarta,kewar da tayi fama da ita zamanta na baya a gidan yanzu duka babu,mantawa ma take da inda take,wani lokaci ma idan tayi breakfast bata sake neman abinci saina dare,batajin yunwa sam idan ta duqufa karatunta,bare kuma ba wani motsi zatayi me yawa ba bare ya zazzage mata cikinta ya jawo mata yunwar ba,tana daki kwance,saman gado idan ta gaji ta dawo falo saman kujera,ba kasafai take shiga kitchen din ba,dalilin da yasa har zuwa sannan batasan ma kalar 'yan aikin da unaisa ke maganar ta kawo ba,don sanda zata shiga da safe basu soma nasu aikin ba,lokacin da zata sake komawa kuma dare yayi sun gama nasu aikin sun bar kitchen din.

     To da wannan damar data samu yasa tayi karatu me yawan gaske,wanda ita kanta batasan ta yishi ba,hutun da akazo gida don yinsa nata hutun kadanne.



    Randa tayi sati a gidan,tana daga bakin window dinta ne taji cewa ja'afar din tafiya yayi ashe,ta bakin unaisan sanda tayi baqi take rakasu zuwa parking lot na gidan xasu shiga motarsu,saita janye zuwa ciki,ta bude shafin gaba na littafinta taci gaba da karatunta.

      Sai da tayi kwana takwas da dawowa sannan su fa'iza suka zo mata,harda amnanta,ranar kamar sallah haka ta jita,sun sameta anata sana'ar wato karatu,amna na jikinta ta dauketa zuwa kitchen don ta sama musu abun sha,kafin tayi tunanin me zata girka musu.

    Sanda suka shiga amnan nata mata tambayoyi da zuba mata surutu,tabbacin yarinyar tayi kewarta matuqa,bata lura da unaisa dake tsaye riqe da cup da yoghurt a hannunta ba har sai data kirayi sunan yarinyar,tare suka waiwaya zuwa gareta ita da maimunatun,maimunatun ta dubi yarinyar data zubawa unaisa idanu tana kallonta,duba na rashin sani da kuma rashin sabo

“come-on baby,new mom dinki ce” unaisa ta fada tana murmushi gami da miqawa yarinyar hannu,karon farko da yaro ya burgeta,kasancewarta ba ma’abociyar son yara ba,tsantsar kamanninta da silly mahaifinta din nan ya bayyana,tana fatan batayo miskilanci irin nasa ba.

    Kamar kuwa yarinyar tasan me take rayawa a zuciyarta,sai ta noqe kafada tana ci gaba da kallonta

“Zo mu gaisa mana,haba amna,nace miki new mon dinki ce” ta sake maimaitawa dai,sai ta sake maqale mata kafada,wannan karon kallon fuskar maimunatu dake duba lemon da zata dauko musu tayi

“Wannan ce new mom dina,ke ban sanki ba” ba unaisa da yarinyar ta fadawa maganar ba,ita kanta maimunatu taji mamakin maganar,ta dago kanta tana duban fuskarta,waye ya gaya mata itace new mom dinta?,ya akayi ta fahimci haka?,duk da dai yarinyar nada wata muguwar kwanya da kaifin basira,wanda maimunatu tafi tsammanin daga wajen mahaifinta ta gajeta.

    Sauke amnan tayi qasa tana dubanta

“Itama new momma ce,kije ki gaisheta kinji” saita gyada kai,duk da bata sake jikinta ba amma haka ta nufi unaisan,abun ya yuma unaisan ciwo sosai,yarinyar ma ba zata zo wajenta ba sai wannan agwai din ta yarje mata,ta kuma yi mata umarni?,ta zabgawa maimunatu harara sanda ta riqe hannun amna,hararar da maimunatun bata ma san tana yinta ba,da hilata ta samu ta janye amnan zuwa part dinta,saidai suna tsaka da hira sai ga daya daga cikin masu aikin unaisan sun dawo da amnan,idanu fici fici da alama rigima ko ma kuka tayi musu.

     To hutun kwata kwata na sati hudu ne,suna gama satittikansu suka sake diba suka koma makaranta,maimunatu ta sake dasa yaqin neman karatu,babu ji babu gani,bakin rai bakin fama,su kansu su afrah sunyi mamakin yadda qwaqwalwar maimunatun ta sake budewa daga zuwanta hutu zuwa dawowarta,ta dings musu dariya ganin yadda dukka suke mata duban mamaki,a wani yammaci suna hanyar zuwa islamiyya,bayan ta bada amsar wata tambaya cikin subject din math,shi kansa malamin sai data burgeshi yadda ta amsa question din a gaban allo.

    To bata qarasa basu mamaki ba sai da sukaje islamiyyan,duka ta zubewa malaminsu haddar hadisan data yo,a washegari kuma zai karba na qur'ani,wannan yana daya daga cikin abinda ya sake zaburar dasu suma,sannan kuma farat daya sunan maimunatun ya fara tambari cikin makarantar,tun daga juniors dinsu zuwa seniors,cikin watanni shida kacal ta fara zama sananniya,duk wanda kacewa maimunatu abubakar muhammad zaiyi wuya yace maka bai santa ba,dalibai maza da kuma mata,saboda zuwan da tayi da tarin baiwarwarki a lokaci qalilan,kyakkyawar bafulatar usul,wadda ke dauke da wani irin kyau mejan hankali,musamman da a yanzun take zaman makarata,daga dakunan kwanansu sai ajujuwansu na boko sai kuma masallacin makarantar inda a nan suke gudanar da islamiyyarsu,fatarta ta sake wani irin haske,kamar zata tabata jini ya fito,jajayen labbanta da bata sanya musu komai sun sake ja,hakanan idanunta masu wani irin kyau da suke dauke da golden din qwayar idanu,ita kanta takan jima gaban mudubi tana kallon kanta,tare da tambayar kanta ita dince kuwa?,itace maimunatun rugar ummaru?,itace maimunatun inna furera?tabbas ta canza,canji me nisan tazara kuwa.

     Duk da cewa gayu da wasu dabi'u nasu afrah sun ratsata,har sun zame mata jiki itama ba tare data sani ba,amma hakan bai hanata yin takatsantsan da kanta ba,qwarai ta sani cewa ba daya suke dasu ba,ita din akwai auren wani a kanta,zuwa yanxu ta sake samun ilimi sani da kuma wayewa kan muhimmancin aure da girman matsayinsa saman kan kowacce diya mace,duk da cewa takan manta sosai da cewa ita din matar wani ce,don shi kansa wanda aka daura mata igiyar ta sanadinsa ba ganinsa take ba,wani lokaci sai taje hutunta har ta dawo baifi su hadu sau daya cikinn gidan ba,idan an samu akasi ne suke haduwa biyu,gaisuwa kusan itace maganar da take gilmawa tsakaninsu,har yau har gobe basu taba wata magana data gota babin gaisuwa da amsa ba.

         Tana qoqarin tunawa kanta cewa ita din me aure ce,bawai don damuwa ko soyayya ba,haka kawai cikin ranta takeji bai kwanta mata ba ko kadan,me yasa bai dauko halin hisham ba?,hisham din mutum ne da take matuqar ganin kima mutunci da kuma martabarsa,bata ga alama koda ta kuskure da zata nuna maka yana mu'amala da wani abun maye ko shaye shaye ba,sabanin shi da tun ranar data fara ganinsa tasan cewa mazuqin taba sigari ne,sauran abinda kuma yake sha wannann Allah ne kadai ya barwa kansa sani,tunda ita a nata hasashen,duk wanda yake shan sigari to yana shan komai ma na kayan maye.

   Abu na biyu hisham din mutum ne me kimanta dan adam da darajtashi,koda yaushe yana faran faran da ita dama sauran qannansa,a gu daya take ganin kamewarshi da nashi salon miskilancin shima,idan ya fita cikin mutanen da suke ba ahali a garesa ba,ko kuma baqin fuska,a duk sanda zai dawo da ita makaranta ko kuma zai maidata,hira ce me tsafta take wanzuwa a tsakaninsu,yakan bata shawarwari da qarin haske akan karatunta,labarai da suke da nasaba da karatu,kamar labarin lokacin da yake dalibin secondary kamar ta,takan iya sakin jiki dashi kadan yanxu,wannan baquntar da take masa a da yanzu ta ragu sosai,yayin da shi kuma yake girmamata kamar yadda zai girmama dan uwansa,har wani lokaci yakan bata kunya ainun,ganin cewa ya girme mata nesa ba kusa ba,ita yafi cancanta ta bashi wannan girman.

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 40

Da hannu daya yake driving din,cikin jin wata irin kasala a jikinsa,kai tsaye masallaci da yake sallah idan sallar ya riskeshi akan hanya irin haka ya nufa,ya samu jam’i,ya bada faralin sallar azahar,sannan ya sake fitowa,ya wuce eatery din da yakanci abinci time to time,yayi order din dinner,ya tsaya acan ya tsakura ya biyasu sannan ya wuce kai tsaye zuwa makarantar yana duba lokaci gami da jan tsaki,a yadda jikinsa yayi masa weak a yau,ya tabbatar komai nasa ya rushe,saidai ya barwa gobe kuma,ya fuskanci wani lalaci ne yakeson kamashi a yan satittikan nan,ko zuciyarsa na la’akari da achievements din daya samu take ganin kamar it’s time for her to get some rest wanda shi kuma bai shiryawa hakan ba.

    Karo na uku kenan dame kula da dakunan kwanansu idan sun tafi hutu ta sake leqowa tana tambaya

“Bai iso ba har yanzu”

“Gashi office din principal din shima a kulle yake,duk dakunan da za’ayi kiran suma a rufe suke” cikin qarfin hali tayi murmushi

“Kada ki damu mr Rebecca,nan da minti goma idan bai iso ba,saiki taimakin mu fidda kayan na samu okada na hau” kai ta jinjina

“Shikenan ba damuwa,fata dai kawai Allah yasa lafiya”

“Ameen” maimunatu ta amsa tana son danne rauninta da fargabarta,tunda ta fara makarantar itace ta farko da take rigasu afrah tafiya gida,ko sau daya hisham bai taba delay na zuwa daukarta ko kawota ba,dalili kenan da yasa yau din da suke mata dariyan zasu rigata tafiya gida bata damu ba,tace musu tasan yana hanya,qila ma kafin su gama ficewa a makarantar ya iso,wannan dalilin yasa suka tafi suka barta,don dukkansu sunsan himmar hisham din wajen daukota,sai gashi abun mamaki duka makarantar an fashe,sai ita daya data rage.

      Baya ga fargabar abinda ya riqe hisham din,harda zazzabi da tun jiya takejin somi somin alamun zuwansa,zuwa yanzu kuwa ya fara hade mata har da ciwon kai,abinda yasa ta sake laushi sosai,jimawa kadan sai ga hawaye sun fara layi saman kuncinta tana daukesu,tun ba yau ba dama tasan ita din gwanace wajen saurin kuka,sai gashi dabi'ar tata tana son dawowa,tun tana zaune sai data koma saman gadon afrah ta cure waje daya,tana jin jikinta kamar ana sassara mata shi,hakanan kanta da jikinta kamar an dora mata dutse.

      Sanda mr Rebecca ta turo qofar take shaida mata anzo daukarta sama sama take jinta,amma cikin qarfin hali ta amsa mata da to,wani sashe na zuciyarta tana jin ya sake,ta samu sauqin tunanin wani abu me muni ne ya samu hisham din,mr rebacca ce ta dauka wasu kayan tace bari ta fitar mata dasu,ita kuma ta lallaba ta miqe a hankali,saita koma ta zauna,saboda jinta da tayi kamar tana yawo kan iska,ta dafe kanta da hannunta tana jin kamar zai fado

“Kamar yana sauri ne,zan fita miki da sauran kayan,kiyi ki fito” tafadi ba tare data lura da yanayinta ba tana daukan jakarta data rage ta fice.

      Agogon gaban motar ya kalla,mintuna kusan hudu kenan yana jiranta?,me ta tsaya yi ya tambayi kansa a zafafe,baya son xaman jira ko qanqani,dabi'ar da yafi tsana kenan,sai ya daga kansa don duba hanyar da zata sadaka da dakunan kwanan nasu,dai dai sanda take fitowa,tana takawa ne a hankali cike da takatsantsan saboda yadda takejin jikinta kamar ba nata ba,iska kuma nason wasa da ita daga hagu zuwa dama,fuskarta tadan tasa kadan wala'alla zafi zazzabi ya sanya hakan,lokaci bayan lokaci tana sanya tafin hannunta tana dafe kuncinta,har yanzu baby face dinta tana nan,saidai ta fara cika,ta kuma fara sauyawa,fuskar shaheeda ce ta fado masa at her age,a irin wannan lokacin datake dalibar secondary kamar haka,a wata rana da yayi mata surprise,yazo daukarta daga makaranta ranar daya samu cikar burinsa a sannan,ranar da ya zama samu shaidar zama cikakken matuqin jirgin sama me lasisi,irin murna da d'oki da ya gani saman fuskarta a sannan

“Ban zaci ganinka ba,har kazo da kanka daukana?” Shine abinda shaheeda tace

“Saboda me?” Ya tambayeta kai tsaye,shuru ta danyi still tana murmushi,da alama tana masa kaara ne akan abinda zata fada

“Uhmmm,say it,say your mind” murmushi ta sakeyi ta girgiza kanta

“Ka barshi kawai”
“Saikin fada…..koni na ari bakinki naci miki albasa….mutum ne kai mai wahalar fahimta,me tsaurin ra’ayi,mara sakewa da mutane mara alqibla” baki ta rufe tana dariya,matsalarta dashi kenan,he can say her mind daga kallon qwayar idanunta kawai,yana da wannan baiwar sosai,shi yasa duk sanda ya dage saita kalleshi ido cikin ido ba kasafai ta fiya yadda ba,baya ga dafi da zai barwa gangar jiki da zuciyarta kuma sai ya karanto sirrinta

“Nidai ban fada ba”
“Ni kuma na fada,with all these lapses ma cancanci a bani soyayya….. I don’t know what to say…mafi qarancin abinda zance shine, thank you for opening my eyes and showing me the way, thank you for loving me” kalamansa sun mata dadi sosai,kuma ta sake tabbatar da cewa lallai mahaqurci mawadaci ne.

        A daddafe take qarasowa cikin wata tafiya da tayi kama da takun isa ko yanga,wanda sam babu daya daga cikin abu biyun illa ciwon da takeji a dukka gabbanta,tun daga nesa idanunta ya sauka akan rolls Royce ghost din,tana da yaqinin ba motar hisham bace,ba kuma tasan me motar ba,don bata taba ganinta ba,don haka koda ta isa sai taja ta tsaya tana dan duba gefenta ko xata hangi motar hisham,wala'alla wanna motar ba ita tazo dauka ba.

     Idanununsa ya bude a hankali daga dogon tunanin da ya tafi jin shuru har yanzu ba ita ba alamarta,kai tsaye a kanta suka sauka sanda take dube duben,sai ya sanya hannunsa saman hon na motar ya danneshi ba tare daya dauke dubansa daga gareta ba.

      Wani irin firgewa tayi saboda yadda qarar ya saukar mata a bazata,baqaqen gilasai ne,bata tsammaci ma kwata kwata da mutum cikin motar ba,qafafunta ne gaba daya sukayi wani irin laushin da bazasu iya daukarta ba,tilas ta sulale a wajen tana dafe da kunnuwanta,jikinta na wani irin rawa.

      A hankali ya bude murfin motar ya fito,ya fara takawa zuwa inda ta sulale din,tana tsugune a wajen ta cure waje guda,yaga yadda ta tsorata din ta cikin mudubin motar

“Get up” ya fada a taqaice yana duban ginin makarantar cikin yanayi na nazari,yayin da sautin muryarsa ya sake sanya maimunatun qara dimaucewa,tsoronsa ya sake shigarta.

      Idanunsa ya sauke akanta jin bata motsa ba,bata kuma ce komai ba kamar bata wajen,sai ya lura da yadda jikinta yake rawa,da gasken tsoratar tayi sosai?,kafin ya sake cewa komai miss rebacca dake goye da jakarta ta iso wajen

“What’s happening?,sir…kamar bata da lafiya sosai fa,ko jikin ne?” Ta fada tana qarasa kusa da maimunatu ta kama kafadarta tana tambayarta,sannan ta fara qoqarin dagota

“Sir….jikinta da zafi sosai,clinic sun rufe suma,saidai idan kun fita ku samu wani a waje a samo mata magani” ta fada cikin girmamawa bayan ta raka maimunatu cikin mota ta zaunar da ita

“Thank you” ya fada a taqaice,sannan ya taka zuwa motar ya shiga ya tada ita,saidai can deep inside him yana jin wani ba dadi a cikin ran nasa.

      Tunda suka fara tafiya qwaqwqwaran motsi batayi ba cikin motar,sai ma sake takurewa da tayi saboda yadda uwar ac din daya balbalawa motar take barazanar hallakata,mugun sanyi takeji kamar me,ga na zazzabi ga na sanyin ac,abinda ya sake galabaitar da ita kenan,sanda take shirin ta bude murfin motar tana shirin fitowa wani zazzafan amai ya kubce mata,duk yadda taso kada tayishi cikin motar amma yaci qarfinta,take ta wanke jikinta zuwa qasan motar,sai ya zare seatbelt dinsa yana fitowa daga cikin motar.

    Zagayowa yayi,yayi tsaye a inda take aman yanayin fuskarsa na sauyawa

“Why J,why?” Ya samu kansa da tuhumar kansa da kansa,yadda take ta yunqurin aman ya isa gaya maka tana jin ba dadi sosai a dukka jikinta,baisan kuma yadda zai taimaka mata ba,sai ya dan tura mata murfin motar ta sake dafeshi kuwa sosai taci gaba da kelaya amanta.

      Ruwan roba ya fidda a motar ya miqa mata sanda ta gama aman,a galabaice ta karba,sai data kusa minti biyu sannan ta iya kuskure bakinta ta zubar,yasa hannunsa ya rufe motar,sannan ga zagaya seat dinsa ya sake shiga ya tashi motar a hankali yana yiwa mai gadi hon ya dage masa qofar suka sake ficewa daga gidan ba tare da ko ciki sun shiga ba.

      Ganin yadda take rawar sanyi sai yasa hannu ya kashe ac din,tuqi yake a hankali yana tunanin wanne asibiti zai kaita?,daga qarshe dai ya samu kansa da yiwa kansa jagora zuwa asibitin da marigayiya shaheeda ke ganin likita.

        Sun dan sha fama kafin a gano file din nata,idanunsa akan sunan dake jikin file din,sai ya janyeshi gefe yana gayawa receptionist din,su maida wannan a bude sabo da wani sunan daban.

“Me sunan da za’a zaka?” Ya tambayeshi

“Maimun…..maimun ja’afar” bakinsa ya subuce kawai yaji ya furta hakan,sai ya maida kansa ga wayarsa yana juya sunan a cikin ransa.

       Bayan likita ya gama ganinta dole yasa aka bata daki saboda yadda take sake galabaita,tana ta aman,yasa kuma aka jona mata ruwa bayan ya mata allurai,cikin lokaci qanqani bacci ya dauketa saman gadon.

      Idanunsa yadan kai kanta,fuskarta har tadan yi fayau akan ganin da yayi mata dazun,wani abu me kama da tausayinta ya tsarga masa,yana ganin kamar hon din daya danqara mata shi yayi silar ta'azzarar ciwon,don likitan ya fada,akwai abinda kamar ya razanata,dubansa yakai ga hijabin dake wuyanta tun dazun,wanda dashi akasha gwagwarmayar aman,akwai buqatar a cire mata shi,to amma bazai iya tabata ba,agogo ya kalla,baisan yaushe zaa sallamesu ba,uwa uba ma likitan yace sai yadda yaga jikin nata,sannan shi kansa drip din kadan kadan yake diga,bazaiyiwu yayita zama ba yabar duk aikin dake gabansa,don haka ya fidda wayarsa ya soma duba number anni.

      Har zai kirata ya fasa,ya duba number baba tabawa,Allah ya taimaka kuwa ya ganta,ya cilla mata kiran,ya kuma gaya mata driver ya daukota yanzu ya kawota asibitin,dai dai lokacin suna tare da anni tana hada mata kwadon zogale,sai ta dubeta

“Manya ne ya kirani,wai Doma,doma hospital” cikin mamaki anni ta kalleta

“Waye kuma ba lafiya?”

“Baice komai ba haj anni,kinsan hali dai”

“Ko shine?” Yadda annin tayi maganar cikin damuwa ma sai yadan baiwa baba tabawa dariya

“Kai haba dai,shi dinne bashi da lafiya zai kirani?,kamar ma kin manta halin mutuminki?,shi da ko sanda yana matashinsa ma saidai yayi ciwonsa a daki yagama ba wanda ya sani,saidai idan anga fuskarsa ta sauya?” Kai anni ta gyada,ta tuna mata kam abinda ta sha’afa

“Kamomin shi a wayar taki” bata musa ba ta koma kiran nass,dab da zata tsinke ya daga,kafin yace komai sallamar anni ta cika kunnansa

“Ka kira tabawa kace tazo asibiti,sannan kuma bakayi cikakken bayani ba,waye ne ba lafiya?” Shuru ya danyi kadan,yana rarraba hankalinsa kan sunan da zaya kirayeta dashi,a hankali ya furta…….
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 38

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button