Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf✨

Wattpad@ummuashraf22

Bismillahir rahmanir raheem….

01

Budurwa ce da bazata wuce 17 years ba a kitchen da katon bowl me daukeda kayan miya a gabanta sai jujjuyasu kawai take da sunan gyarawa,wata dattijuwa dake kokarin sauke tukunya a kan gas ta juyo tana kallon kayan miyan tace “oh ni hauwa!yanxu Layla gyaran kayan miyan ne har yanxu sai kace wadda bata da lfy?Wanda ta Kira da Layla ta turo baki tace to ba na kusa gamawaba mama hauwa wanki na uku fa kenan nake musu,hauwa bata sake cewa komai ba ta juya tacigaba da aikinta,,ko minti biyu batai da juyawan ba Layla ta fasa wani uban ihu tana tsalle tana yarfe hannu tace wayyo na shiga uku Mama hauwa ya shigan min idona wlh wayyo Allah daddynaaa..da sauri wani matashi ya shigo kitchen a guje dagashi sai singlet da three quatre ya kamo Layla da sauri yace menene?Mama hauwa na kokarin yi masa bayani kawai taga ya dauketa cak yayi part dinshi da ita sai tsala ihu take,tai murmushi kawai ta dauki kayan miyan zata karasa da gyarawa wata dattijuwan Mata ta shigo kitchen din tanasanyeda hijab a gigice tace hauwa meke faruwane Ina sallah naji ihun Layla,lafiya kuwa?hauwa tai murmushi tace wlh lafiya qalou hajiya,gyaran kayan miyan da aka sata nefa tun dazu takeyi sai kawai ihunta naji wai yaji ya shigan mata ido,matar ta dafa goshi tai salati snn tace yanzu duk wnn uban ihun da naji na yaji ne kawai?mama ta sake murmusawa tace wlh shine hajiya,to ynxu tana Ina?ta tambaya tana waigawa ko zata ganta a kitchen din,Mama hauwa tace babanta ya dauketa yayi bangarensa da ita,matar da jijjiga Kai kawai ta fita tana mita”dama shi yake lalata ta wlh,inba don iskanci ba meye yaji a ido Allah na tuba da zata dagama mutane hankali haka zataci ubanta sai nayi maganinsu daga ita har uban nata wlh”itadai hauwa dariya kawai tayi tacigaba da aikinta.

Suna shiga part dinshi direct bathroom ya wuce da ita ya ajiyeta gaban sink snn ya kunna tap ya shiga wanke mata fuskan da hanunshi,har yanxu bata bar kuka ba ta rike hanunshi tace daddy da zafi kayimin a hankali pls,ba musu ya dinga shafa fuskan a hankali kmr yana wanke kwai,seda ya gama snn yace oya open up mu gani ko yq fita,ta bude idon a hankali sai Kuma ta sake buga wani ihun tana rukunkumeshi tace wlh har yanxu akwai zafi daddy bai fitaba wlh,,ya janyeta a jikinshi ya sake wanke mata fuskan snn yace bude muga,ta shiga bude idon a hankali har ta budeshi fess tana kallonshi tace ya fita,baice komai ba ya kama hanunta zuwa bedroom dinshi,gefen gado ya zaunar da ita shima ya zauna snn yace “tell me garin ya kikasa yaji a idon?ta wani marairaice tace daddy ummi ce tace wai saina taya Mama hauwa aiki a kitchen wai ban iya komaiba sai sangarta,shine Mama hauwa tace in gyara Mata kayn miya shine Ina cikin yi kawai yaji ya shigan min ido,kallonta kawai yake yanda take mgn kana ganinta dama zakasan shagwababbiya ce ta bugawa a jarida,ya kamo hanunta yace yanxu baby sbd yajin shine zaki cika mana gida da ihu haka,kinji yanda hankalina ya tashi kuwa?I was thinking ko konewa kikayi ko wani abu,,ta kwanta a kirjinshi tace to kayi hakuri bazan karaba Amma Allah yajin da akwai zafi,ya lumshe ido Yana shafa kanta can kasan makoshi yace it’s okay ya wuce but next time ki ringa kula sosae idan an saki gyara kayan miyan kinji,ta daga mishi Kai a hankali tace toh daddy”Good yanxu tashi muje in tayaki ki gyara kayan miy…bai karasaba ta Mike tana kallonshi a marairaice tace don Allah daddy kayi hakuri ni baccima nakeji kuma har yanxu idon be dena yin zafi ba,,murmushi kawai yai yace alright ki kwanta abinki bari inje in samu ummin,ta rungumeshi tace yawwa daddyna I love u,,I love u too ya fada yana pecking dinta a forehead snn ya fita,ita Kuma ta dauko iPad dinta data bari nan dakinshi daxu ta koma kan gadon tana dariya tace haka kawai inje yanxu nasan mukayi ido hudu da ummi to me rabata Dani sai Allah.

Yana shiga bai samu ummi a parlor ba don haka ya wuce bedroom dinta,tana zaune gefen gado waya kare a kunnenta fuska ba walwala take mgn,a hankali ya karaso ya zauna kusada ita sai yaji tana fadin”saboda Allah Aisha wnn ba iskanchi bane,ace wai kamar Layla me shekara 17 common gyaran kayan miya bazata iyaba,kinji yanda ta kurma ihu wlh ni da farko ma na dauka karyewa tayi,shi Kuma uban ya dauketa xuwa sashensa sbd sangarta,to gsky kija masa kunne ya dena sangartamin jika ya barta ta koyi abinda ya kamata don ba zama zatai Babu aure kamar yanda shima yake zaune Babu auren ba,,a daya bangaren matar tayi dariya tace inshaAllah zanyi masa mgn yaya,kiyi hakuri,tace to shknn sai anjima,ta ajiye wayarta gefe ta daure fuska kmr bata ganshi ba,yai murmushi ya matsa jikinta sosae bai kaiga yin mgn ba wayarshi dake hanunshi ya fara ringing”Ummata”shine sunan dake kan screen din still Yana murmushi ya daga wayan yakai kunne yace barka da rana Ummata,wadda ya kirada umman ta amsa mai da barka dai son ya aiki,yace alhamdulillah ya kano,tace kano gata muna cinkinta son yanxu umminku ta kawomin kararka,ya Dan saci kallon ummin da har ynxu bata kalli inda yakeba yace to me Kuma nayi umma?tace wai kana sangarta ‘yarka baka bari a koya mata aikin gida,yai Dan murmushi yace to zaa gyara umma InshaAllah,umma tace yawwa ayi kokari don Allah Kuma har gori tayimin wai ba zama zatayi ba aure kmr yanda kake zaune ba,don Allah son ka daure kayi auren nan ko bakason hankulan mu su kwanta ne?yace inaso umma,then why bazakayi auren nn ba tunda shine abinda mukeso muga kayi?ya sake kwantar da murya yace zaayi umma InshaAllah lokacine beyiba,umma tace to shknn Allah ya nuna mana lokacin ya amsa da ameen snn sukai hanging wayar,,ya ajiye wayar tashi a gefe ya kamo hanun ummi daketa kauda Kai ya kwantar da murya kmr wani karamin yaro yace ummi am so sorry plss,ta sake dauke Kai batace komai ba,ya saki hanun nata ya durkusa gabanta ya hada hannaye yace plss ummi kiyi hakuri,nida baby bamu kyauta ba Amma bazamu karaba plss,ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannayen nashi cikeda kulawa tace bakajin mgn Taheer gashi Layla itama ka fara koya mata irin wnn halin naka,yace we’re sorry ummi,ta jijjiga tace shknn ya wuce Amma gsky ya kamata ka ringa bari ana koya mata aiyukan gida mace cefa ita Kuma nan gaba kadan aure zatayi,yace toh ummi,ta mikar dashi ya zauna gefenta tana fuskantarshi tace Taheer,ya amsha da naam ummi snn tacigaba”sbd kaga na damu kayi aure shine kakemin haka?ya girgiza Kai da sauri yace wlh ba haka bane umm…ta katseshi da fadin inba don haka bane to meye dalili,kana da kudi kanada ilmi kanada lfy snn Kuma kanada kirar da ba kowacce mace ce zata kalleji bataji ka kwanta mata a rai ba then why bazakayi auren ba?ya shafa Kai yace ummi lokacin…bai gamaba ta sake katseshi da fadin dont tell me lokacine beyiba Kaine dai bakaga daman yiba Taheer Ina sane da matan dake binka kana wulakantasu kodai bakada lfy ne?ya girgiza Kai a hankali yace aah,
To meyasa bazakayi ba sai ka fadamin dalili Ina sauraronka,yai shiru kawai don bashida amsa,
Ay dama nasan bazakace komai ba Taheer Amma inaso ka sani ko mahaifinka da yanada rai bazaiji dadin wnn zaman da kakeyi ba aure ba Taheer lokaci Kara tafiya yakeyi yanxu shekara arba’in zakayi wnn watan meyasa bazakayi auren nan ba ko don hankalinmu ya kwanta,,ya kama hanunta cikin sigan lallashi yace InshaAllah zanyi ummi nan bada dadewa ba don Allah ki dena damun kanki akan mgnr nn pls,,,idan kanaso in dena damuwa then kayi aure,sa’anninka da kannenka duk sunyi aurensu with kids Kai Kuma kana nan ko auren ma bakayi ba,yanxu kalli nafeesa,kawarka ce Taheer shekara biyu ka bata Amma gata nan da yara hudu Kai har ynxu kana nan a matsayin saurayi u better wake up wlh wnn zaman ba inda zai kaika,yai Dan murmushi jin mgnrta na karshe yace InshaAllah kwanan nn ummi zakiji good news I promise u this,tace better in Kuma baso kake diyartaka ta rigaka yin auren ba,shidai baice komai ba sai dariyar yake da yayi,,ya mike a hankali yace ummi zan wuce clinic yanxu akwai patients din dake jirana,tace to saika dawo Allah ya kiyaye hanya ya amsada ameen Yana gab da fita dakin tace ita Kuma waccan data makale a sashenka saika turomin Ina nemanta,ya amsa da

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button