GURBIN IDO

GURBIN IDO 46-50

48

Sai daya jima da barin wajen sannan ta tashi ta wuce dakinta,ruwa ta hada tayi wanka,sai taji dadin jikinta,kaya ta saka marasa nauyi cotton wanda bazasu takurata ba,komai takeyi cikin kasala take jinta,sai kawai ta haye gadonta,ta lumshe idanunta.

Fuskarsa da qamshinsa ne suka fara bijiro mata,the way daya dinga treating dinta,yana kuma watsa mata nauyin idanuwansa da suke da wani irin magnet a cikinsu me qarfi,wani juyi tayi,wanda cikin rashin sani ya sanyata danne hannunta dake dan zugi har yanzu,sai data ce wash Allah.

“Wai meye haka?” Ta jefi kanta da kanta da wannan tambayar,sai taja qaramin tsaki,ta miqa hannunta ta dauko wayarta dake saman kanta,videos din data dauko ta shiga,ta zaba drama daya ta kunna ta fara kalla.

Bata dauki dogon lokaci ba ta fahimci zaa buga soyayya sosai,abinda yasa ta tattara hankalinta akai,tana kuma biye dasu,lokaci lokaci tana sakin murmushi,a qalla tayi kusan awa uku sannan barci ya soma fusgarta,babu jimawa kuwa ya dauketa gaba daya daga duniyar nan zuwa tasa duniyar.

Sau biyu baba tabawa na leqota don taga ko lafiya?,duk sanda ta leqo din sai taga wayarta tana yi,sai ta koma ga zatonta idanunta biyu,kallo kawai takeyi.

Tunda ya fita yana masallacin,ya kuma samu gaba kamar yadda yakeso,a gabansa liman ya iso,ya gabatar da kuduba aka kuma tayar da sallar,sanda aka idar ya samu ganin abbi,saidai kuma yana ta fama da mutane,don haka ya masa sallama yace sa hadu a gida.

A harabar masallacin ya suka gamu da jabir,abinda ya sake tsaidashi kenan,ganin maganar tasu ba zata qare ba,sai ya kira driver dinsa yace yazo ya dauki motar suka wuce a motar jabir din.

Gidan mahaifin jabir qanin abbi suka fara zuwa,suka gaida uncle usman da matarshi,sun jima suna hira dashi kafin su baro gidan,suka wuce gidan abbi dr marwan.

Kamar ko yushe sassan ammansa ya fara shiga suka gaisa,ya taras da amna ta tashi a bacci,tana ta taba rigimarta,ganinsa yasa ta watsar da komai ta dafeshi tana fadin xata bishi,yarinyar nason binsa,shima kuma a duniya yafi kowa son kasancewa da ita a muhalli guda,to amma kuma idan yace zai dauketa wa zai kaiwa ita?,wa zai kula masa d ita?,ya tabbatar ba zata taba samun kwatankwacin kulawar da take samu ba a wajen su amma,bai amsata ba ya sabeta ya wuce wajen ammi suka gaisa,sannan ya wuce sassan mutuniyar tasa anni yana sabe da amnan yana mata tambayoyi da suka shafi karatun makarantarta,tana ta bashi amsa dai dai,abinda yayi matuqar faranta masa.

Da sallama a bakinsa ya shiga sashen,mutum uku ne zaune,anni jabir da ya riga shi yo gaba sai kuma hafsat,wadda sallamarsa ta sanyata rudewa gaba daya,ta kuma tattaro dukka nutsuwarta ta dawo da ita jikinta,gami da janye qafafunta data miqe a dazun tana kadasu,ta sanshi ta kuma san halinsa sarai,baya tolerating nonsense,har ya qaraso wajen tana satar kallonsa,tana jin kamar ta hadiyeshi,kishin unaisa da maimunatu yana saukar mata,kada ma unaisa taji labari,don ta samu labarin maimunatu ba mazauniya bace,makaranta take zuwa,bugu da qari tana ganin tayi qanqantar da zata bata wuya wajen shigowa gidan da kuma cimma muradinta.

Cikin salo iyayi da kuma kwainane ta gaidashi,kansa na wani sashen ya amsa mata,abinda yayi matuqar qona ranta kenan,saidai tayi biris taci gaba da zama a wajen ba tare data motsa ba,kunnuwanta duka suna ka maganganunsu su da anni

“Lallai da gaske anni tafison wadan nan guys din,kada ma wannan dan mulkin nata yaji labari” ta fadi a ranta,wanda a zahiran zaka dauka danna waya takeyi

“A zuba muku abinci” gyara zama jabir yayi

“Eh nikam a kawo,don nasan zaiyi wuya na samu idan na koma,don batajin dadi,banson cin kuma na yarinyar da aka kawo matan” sai da anni ta waiwaya ta dubi hafsat tace taje ta hado musu abinci a kitchen,ta kuwa miqe da hanzarinta tana aje wayarta gami da jin dadin wannan aiki da anni ta bata tayi kitchen din,sannan anni ta maido kanta ga jabir

“Jikinne har yanxu?”

“Wlh anni,yau da lafiya gobe babu”

“To Allah ya raba lafiya” murmushi yadan saki yana shafa kansa cikin dan jin nauyin annin,baki ta tabe

“Kaga dan nema,ja’iri,wai yau ni ake jin kunya” dariyar da yake riqewa ya qarasa saki,anni anni?,Allah dai yaja musu kwananta.

      Kamar taa bar zanca sai kuma ta dubu sashen da ja'afar ke zaune,har yanzu amna na saman cinyarsa

“Allah yasa muji irin wannan labarin a gidan wancan kurman,kema yarinya kya samu kiga ‘yan uwanki ko maraici da kewar da kike ciki zata ragu” yi yayi kamar ba dashi ake maganar ba,kamar kuma baiji ba,duk da maganar ta tsaya masa a rai

“Ya jikin maimunatun?” Ta sake zungurarsa da magana ganin baice komai ba,dai dai sanda hafsat ke fitowa a kitchen din dauke da kwanukan abinci,gabanta yadan fadi,tana son jin qarashe zancen,kada dai ace ciki gareta

“Alhmdlh” ya amsa a taqaice

“Inaga kamar ya kamata tabawa ta dawo hakanan,dama tamin magana kan tanason tahowa” baiso annin ta fadi hakan ba yanzu,ko ba komai yana samun abinci kwana biyu yaci ya qoshi hankali kwance,ya rage zuwa eatery neman abinda zaici

“Ba laifi” ya amsawa anni,dai dai sanda ta iso wajen,ta fara ajjiyewa jabir,sannan ta qaraso inda ja’afar din yake,cikin salo ta duqa tana ajje masa nasa abincin,wanda zubin data masa ma daban yake,in a stylish way ta shirya salad din dake saman abincin.

      Hannu ta miqawa amna

“Taho daddy ya samu yaci abinci ko?” Kafada ts maqale tana kallonta

“Ahaf…..wannan ‘yar wulaqancin fa sai wanda ta zaba,wuce ciki abinki” batas anni tafada haka ba,taso zama ne a wajen taci gaba da jin hirarrakinsu,ta kuma morewa kallon ja’afar din,don yau din wani kyau yayi na musamman,kayan sunyi matuqar karbarsa.

Dakin dake opposition da dakin ta shige,ta zare key din dake jikin qofar tana leqensu ta jiki,abun haushin duk yadda ta tsara masa abincin bata wani ga yaci komai ba a ciki,hasalima amna taga ta sanya cokali tana cin abinta,ruwan kawai taga ya dauka yasha,shima ba mai yawa ba.

Ana sallar la’asar daga masallaci gida ya wuce bayan sunyi sallama dasu anni,already dama yayi kiran driver,don haka kafin su idar ma ya iso,ya daukeshi suka wuce,yana mota yana tunanin amnan,duk sanda yazo gidan sai yarinyar tayi attempting din binsa amma tilas take sawa yace mata a’ah,to yau ka harda kukanta,abinda yasa kenan yayi deciding next month ya dauketa su danyi yawo kadan,koda zuwa lagos ne,yasan hakan zai mata dadi,zai kuma debe mata kewa.

Samansa ya wuce direct,ya bude dakin yana kallonsa,gaba daya it’s not in order,komai na dakin bai masa yadda yakeso ba,sai ya koma da baya ya bude daya bedroom din nasa ya sauka a can,kayan jikinsa ya sauya kawai zuwa wata farar jallabiyya ta maza mai sulbi da kuma wide neck,ya hada dukka aikin dake kansa wanda a qa’ida yau zaiyishi a office,amma yau din juma’ar qarshen wata ne,yana basu hutu yawanci duk qarshen wata,musamman idan akwai raguwar aiki sosai a lokacin.

Har zai zauna ya fasa,saboda cikinsa da yaji yana buqatar sanya masa wani abu,sannan kuma yanason jin ya hannun nata,don ya tabbatar a yadda yaji anni na masa magana a kanta yau,tabbas idan wani abu ya faru kai tsaye ma zata iya cewa shine ya qonata.

A nutse yake saukowa daga stairs din,duk inda ya gifta sassanyan qamshinsa yana biye dashi,rigar ta masa kyau ta sake maidashi cikakken mutum mai cikar kamala zati da kuma haiba.

1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button