GURBIN IDO

GURBIN IDO 46-50

Da tattausar sallama a bakinsa ya shiga falon,baba tabawan ce kadai xaune tana kallo,tana yi kuma tana duba girkinta dake kitchen,duk da abincin ma yau kusan ita daya taci na safen har na ranan,ta rasa wanne irin bacci maimunatun takeyi.

Cikin fara’a ta amsa sallamar tasa ta kuma yi masa maraba,ya tambayeta hannun nata

“Wallahi manya ban sani ba,tunda ta shiga ta kwanta bansan ma bacci take ba sai daga baya” baice komai ba ya miqe,hannunsa cikin aljihun rigarsa,ya nufa dakin nata.

A hankali ya tura qofar ya sanya jikinsa,kamar ko yaushe dakin gauraye da madaidaiciyar iska dake cakude da qamshi iri iri wanda ya bada wani scent na musamman,kasancewar yamma tayi dakin ya rage hasken dake akwai,yaci gaba da takawa zuwa inda yake hangenta a cure waje daya,saidai hasken wayar daketa aiki ta haske fuskarta sosai.

Gab da kanta amma ta bayanta,idanunsa suka sauka tun daga dogayen qafafunta dake harde waje guda,saidai kuma taba motsasu a hankali duk bayan wasu sakanni,da alama mafarki takeyi,don haka take dan motsa hannayenta ma,yawo yaci gaba dayi da idanunsa,yadda take kwancen sai yakega.kamar kwanciyar tata batai dai dai ba,sosai qugunta ya fita ta cikin rigar,sai ya dauke idanunsa da sauri ya saukesu kan screen din wayar.

Minti daya kacal ya tuna film din,one of the best dramas nashi,ya akayi ta nemoshi take kuma kalla?,hannunsa ya sanya ya zare earpiece din dake kunnenta ya maida a nashi kunnen idanunsa still suna kan wayar,lallausan murmushi ya qwace masa,abinda ya qarawa fuskarsa wani mugun kyau,abinda ba kasafai yake faruwa dashi ba kenan,ya tuna scene din,ya tuna wajen,murmushin yaqi daukewa daga fuskarsa,,ya tayar masa da wani tsohon memory da kuma wani sweet moment,sai yaji yana da sha’awan sake kallon drama din,ya duqa a hankali ta saman kanta da zummar dauko wayar ya kashe mata,abinda yasa yayi mata kamad rumfa a saman kanta.

Juyi tayi cikin hanzari tana sakin wata qaramar qara,abinda yasa ta bugeshi,ya kuma fada saman kanta saboda unexpected ta bugeshin,baiyi tsammanin zata motsa ha a sannan,qamqam ta riqeshi,tana tsamamnin cikin mafarkinta ne,saboda shine cikin mafarkin,ta kuma sake gasgata mafarkin takeyi jinsa a jikinta qamshinsa yana shiga qofofin hancinta.

A nutse ya zube idanunsa saman sleepy face dinta,karon farko da sukayi kusanci mai zurfi a tsakaninsu irin haka,har suna musayar numfashi,wanda yake fita da tare da qamshin jikkunansu,yayi gab da ita qwarai,kamar me shirin kissing lips dinta,sosai shagwababbiyar fuskarta ke shiga idanuwansa har yana ganin qananun gashin dake qasan hancinta wadanda suka sanya wajen danyi duhu kadan,cikakkiyar girarta da ta kusa hadewa da ‘yaruwarta,siraran labbanta da suke dauke da wasu irin Pink lips masu daukan hankali.

Wani abu ne ya motsa zuciyarsa,har sai daya saki wasu irin tagwayen numfashi guda biyu a jejjere kamar mai sheshsheqar kuka,yanason zame kansa data zagaye hannayenta dashi saidai ya fuskanci mafarki take,kamar ma kuka kuka,saboda yadda shagwababiyar fuskartan nan ta narke gaba daya,ci gaba yayi da kallonta,a hankali murmushi ya soma maye gurbin yanayin kukanta,ya zubawa dan qaramin bakinta daya soma motsawa idanu

“Kayi haquri…….”
“Yaa hisham” sunan ya fita can qasa,shi kansa motsi da dan qaramin fitar sautinta yabi ya fahimci me take cewa,mamaki ya cikashi,hisham?,hisham kuma take kira cikin mafarkinta?,for what reason?,fuskarta yaci gaba da kalla nasa yanayin na sauyawa ba tare daya sani ba,a hankali fuskarta ta koma normal mode na masu bacci,da alama ta gama mafarkin da takeyi kenan,sai ya zame hannunta daya nutse a qeyarsa cikin lallausar sumarsa,ya miqe tsaye yana ci gaba da kallonta bayan ya goye hannunsa a qirjinsa,kiran sunan hisham da tayi ya dawo masa,yadan rufe idanunsa sannan ya sake budewa,wani abu yaji yadan taba ransa,sai ya miqa hannu ya jawo hannunta dake boye a gefanta,zugi ya ratsa tsakiyar baccinta,abinda ya sanyata farkawa kenan.

       Sai data bude ta kuma rufe idanunta sau uku don son tabbatar da cewa yanzun ma mafarki ne ko ido biyu,yaji alamun ta farka amma kuma baiko daga kansa ga dubeta,yana dai nazarin hannun nata ne,sai daya tabbatar batayi ko alamin tashi ba sannan ya sake mata hannun,a hankali kuma ya aza mata idanunsa masu nauyi da suka tilastata janye nata,ya basar ya kuma motsa kaman zai fita sai kuma ya dakata

“Karki qara kwanciya bakiyi addu’a ba,that’s why kuke rubbing mafarkai” yana kaiwa nan ya taka sannu a hankali ya fice.

       Idanunta ta waro waje tana bin hanyar daya wuce da kallo bayan ta tabbatar da fitarsa,kada dai yana tsaye ta gama mafarkin da tayi yanzu,saita cusa kanta tsakiyar pillow tana son tuna me da meye ya faru cikin mafarkin,tsahon minti kusan biyar kafin ta sake daga kanta da sauri ta kalli agogo

“Kai” ta fada da sauri tana wantsalowa daga gadon,ganin lokacin salla ya qwace mata sarai.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 47

Washegari tare suka hada breakfast da baba tabawan,suna aikin suna taba hira,sanye take da wasu kayan bacci masu taushi sosai,saidai basu da wani kauri me yawa midnight blue da torches na olive color,wandon iyakarsa saman idon sahunta,rigar kuwa tsahonta iya cinya ne,short sleeve ce,don iyaka dantsenta hannun yatsaya,daga gaba rigar ta dan lafe mata,har tana fidda shade na brazier dinta,bata damu ba sosai,tunda tasan babu kowa a sashen daga ita sai baba tabawa,hakanan babu me shigo musu,kalar kayan ta fidda hasken fatarta sosai,kanta qaramin dankwali ne mai santsi data masa Vshape ta daure sassalkan gashinta,wanda santsinsa dana dankwalin suka hadu waje daya suka sanya dankwalin qin zama sosai a kanta,duk bayan minti biyu saita janyo dankwalin ta rufe gaban kanta dake da wani irin kwantaccen suma mai santsi data zagaya har qeyarta,duk da safiya ce,amma jikinta qamshin turaren women maze alharamain yakeyi,qamshin dake cakude dana body mist datake amfani dashi.

Hira suke sosai,baba tabawan tana bata labarai wadanda maimunatun take jinsu daban,saboda sun saɓa da tata rayuwar,saidai hirar tana nishadantar da ita sosai,saboda ko a saman fuskarta ya nuna hakan,kyawawan jerarrun fararen haqoranta sun bayyana.

Knocking suka jiyo,maimunatu ta tsame hannunta daga ruwan da take dauraye kwanukan da suka gama amfani dasu,ta goge jikin towel na kitchen din,sannan ta fito da niyyar budewa ba tare da tunanin komai ba.

A hankali ta kama handle din ta bude,abu na farko daya fara marabtarta qamshin jikinsa ne,wanda acn da aka balbalawa babban falon ke tunkudo qamshin da gaske zuwa nata falon.

Saman kanta idanunsa suka fara sauka,wanda dankwalin kanta ya zame xuwa rabin kanta,abinda ya bawa gashinta damar bayyana sosai,sai ya zame idanun nasa ya janyesu gefe,tasa dukka hannayenta biyu tana dafe dankwalin dake shirin faduwa daga kanta gaba daya,ta kuma janye qafafunta da taji suna sarqewa zuwa gefe ta bashi hanyar shigowa,a sace idanunta na binsa da kallo,cike da mamakin shigarsa ta yau ta zallar bahaushe,cikin wani lallausan farin yadi me shara shara,wanda hatta fara qal din singlet din dake jikinsa sai data bayyana,ya giftata ya bar mata qamshinsa wanda batasan me yasa take samun wata nutsuwa ta musamman ba duk sanda zata shaqeshi.

Kamar wata mara gaskiya ta rabe a bayansa

“Ina kwana?” Ta fadi a matuqar ta kure,nadamar yadda ta fito haka gaba gadi ba tare da tambaya ko sanin waye ba tana shigarta.

     Gaba daya ya waiwayo zuwa inda take tsayen,hannayensa dunqule cikin aljihun rigarsa,ya zube idanunta da sukayi wani irin laushi saman qirjinta dake bayyana shatin baqar brazier dinta,yadda yake qoqarin janye idanunsa daga wajen haka zuciya da idanunsa ke ingizashi zuwa ga ci gaba da kallonta,yana jin kamar wani mayen qarfe aka dasa ma idanun nasa a wajen,yayin da wani abu me kama da tsarguwa ya saukarwa maimunatu jin shuru bai amsa ba,cike da jarumta da son tsira da mutunci ya raba idanunsa daga wajen yana lumshesu

“Karki sake irin wannan gangancin,kinsan waye da kk bude qofa batare da kin tambaya ba?” Yayi maganar yana sake qarewa shigarta kallo,hatta sambala sambalan qafafunta sun fito sosai saboda rashin tsahon wandon,yana kallonta ‘yar qarama a gabansa,yanayin da ya tuna masa da zamanin amarcinsa da shaheeda, she’s always like this……under eighteen,sannan taci gaba da zama da dabi’antuwa kamar yadda yakeso ta kasance masa,ta ina ta kuma yaya zai maida GURBINTA?.

“kayi haquri” kalaman suka sauka a kunnensa dai dai da irin yadda shaheeda take fada masa,bata kuma taba canza kalamanta da haka ba,koda shi ya bata mata,yakance

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button