GURBIN IDO 46-50

“Uhnnnn…..u are killing me shaheeda,ko yaushe kayi haquri?kayi haquri,You don’t want to make excuses for yourself?” Daga kai maimunatu da sauri tayi ta dubeshi jin abinda ya fada,sai shima ya maida idanunsa kanta ganin yadda take kallonsa,sai a sannan ya karanci ashe a sarari yayi maganar,saidai can qasan maqoshinsa ne,janye idanuwansa yayi yana dan tsuke fuska kadan,ya akayi maganar ta fito fili?
“Shaheeda” takira sunan a ranta tana son tuno inda tasan sunan,ummin amna?,kwanyarta ta bata…..kafin ta gama tantancewa muryar baba tabawa ta yiwa falon tsinke.
Sai a sannan ya dauke kansa da shanyayyun idanunsa gaba daya daga dubanta ya maida ga baba tabawa,wadda har tayi niyyar juyawa a yanayin data gansu a tsaye,cikin sakanni ta karanci wasu qananun abubuwa a fuskar kowannensu
“Manya,har an fito?” Kai ya jinjina ya kuma ranqwafa yana gaidata,ta amsa cike da kulawa,ya sanya hannunsa a aljihu ya fiddo kudi ya ajjiye mata
“Ah…..ai an kammala karin safe,ka jira a gabatar maka” bata saurari amsarsa ba ta juya ga maimunatu
“Suna kitchen fa” ta fadi mata,kamar wadda ke jiran umarnin barin wajen tayi gaba tana qara hanzari,gaba daya kamar tayi layar zana haka take ji,da so samu ne dakinta ya kamata ta biya ta fafa dauko hijabi,to amma kuma baba tabawan fa?,hakan zai zama kamar wani rashin girmamawa ne a gareta,dole ta wuce zuwa kitchen din.
Sanda ta dawo falon a tsaye ta sameshi yana saita agogon hannunsa,qarin tashin hankalin baba tabawan bata nan a falon,sau daya tak ya daga kai ya kalleta ya maida ga abinda yakeyi,saita wuce dining ta jera komai,kafin tayi magana taga yana takowa zuwa wajen,yaja kujera daya ya zauna a kai,har yanzun bai kuma dubanta ba.
"Me za'a zuba maka?" Tayi tambayar tanason riqe rawar da muryarta keyi,don gaba daya ta gama rudewa,Allah Allah take ta gama serving nasa tabar wajen
“Anything” ya amsata a taqaice,warmers din ta fara qoqarin budewa,saidai duk wadda takama zata bude saita kasa,saboda santsi da kuma yadda jikinta yayi weak,tako ina a jikinta takejin idanunsa na mata wayo,tayi Allah wadaran shigar da kuma yadda ta zauna haka yau din babu ko dan baby hijab din da take amfani dashi ko da yaushe,a nutse yake karantarta,kafin ya kauda idanunsa yana latsa wayarsa,ata qarshe ne ya daga hannu da niyyar karba y bude ganin ta kasa,incidentally hannunsa ya sauka saman nata hannun,abinda ya haifar masa da wani irin shock a jikinsa,yayin da ita kuma tashin farko jikinta ya dauki rawa,ta kuma zame hannun nata da sauri taja baya kadan,yi yayi kamar baisan abinda ya faru ba,a nutse ya dauki bowl da serving spoon ya fara diban farfesun kayan cikin dake cikin warmer din.
Tsoronta gaba daya ta dunqule ta kuma hadiye,saboda tuna warning nata daya taba yi,ta matso a kasalance,ta jawo flask na tea data hada da kanta da wasu hadin kayan shayi na musamman data shekaran jiya tana cikin browsing ta fara zuba masa,wani irin qamshi me dadi ya gauraye wajen,har sai da yaja iskar data kwaso qamshin har cikin hunhunsa,deep inside kuma yawunsa ya fara tsinkewa,ta dauko kwalin suger ta dauki one cube ta saka,ta sake debowa zata qara sanyawa kenan yace
“Enough,ya isa” gaba daya kwalin sugar din ya subuce daga hannunta don dama a tsorace take,suka fara rige rigen afkawa cikin kofin tea din,abinda ya bawa ruwan zafin damar yin fallatsi,ya dawo mata hannayenta,taja baya da sauri tana jin zafin saukar ruwan zafin na ratsata sosai har kwanyarta.
Spoon din hannunsa daya fara diban farfesun ya ajjiye,ya hade yatsunsa waje guda yana kallonta,ta hada gumi tana yarfar da hannun,da alama ruwan ya tabata sosai,har ya dauki spoon din xaici gaba da cin abincinsa sai kuma ya kasa,komai tayi shige yake masa da silly attitude na shaheeda data sha yi masa farkon aurensu
“seat here” yayi maganar yana jan kujerar dake daura dashi,idanunta da suka tara hawaye ta daga ta dubeshi dasu,kamar wadda ke shirin sakin kuka,sai ta tako a hankali kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,ta zauna a darare saman kujerar tana dubansa
“Let me see” ya fada yana miqa mata hannunsa,idanunsa cikin nata yana kallon yadda ta narke gaba daya,gumi kuma ya tsatstsafo saman goshinta.
Sai data maida dubanta ga lallausan tafin hannunsa kamar me tsoron wani abu,sannan ta miqa masa hannun nata a hankali,ya miqa nasa ya riqe yatsun nata.
Qaramar qara ta saki da siririyar muryarta me zaqi wadda ta ratsa dodon kunnensa da kyau,idanuwansa ya rintse sosai sannan ya budesu ya zubesu saman fuskarta wadda tuni hawaye sun fara mata zarya,ya dinke fuskarsa tsaf yana ci gaba da tsare gida
“What is that?,zaki kashemin kunne ne?” Kai ta girgiza,gaba daya hawaye ya wanke mata fuska,ta wani narke cikin wani yanayi daya darsa tausayinta cikin ransa,sai ya janye idanunsa yana qoqarin kawar da wannan ya mayar kan hannun nata.
Da sauri ya janye yatsunsa daga inda ya riqe din,saboda yadda wajen yayi jaa,da alama a wajen ta qone din,kafin yayi wani abu baba tabawa ta iso
“Lafiya dai ko maimunatu?” Tayi tambayar tana dubanta
“Subhanallahi” baba tabawan ta fada sanda taga hannun nata
“Garin yaya?” Ta jefa mata tambayar,rashin sanin amsar da zata bata yasa ta maida dubanta ga ja’afar,dauke kansa yayi kamar baya wajen,kamar bashi take kallo ba,kujerarsa ya sake jawowa gaba kadan,ya zamana dab da ita sosai
“Silly girl” ya fada qasa qasa,sake mele baki tayi zata sake sakin kukan,kamar yasan da haka ya kuma daga shanyayyun idanunta acikin nata,sai tayi hanzarin kulle nata idanun,ita kadai tasan me yake haifar mata idan ya mata irin wannan kallon,yana qara mata razani a kansa da kuma wani irin kwarjini da takeji kamar zai sata narkewa a wajen.
Sannu baba tabawa ta matso tana mata sanda ta duqufa yana mata tofi a hannun nata,ya kwashi kusan minti talatin yana mata tofin babu tsayawa,sannan ya zare hannunsa daga cikin nata
“Sannu maimunatu” baba tabawa ta fada fuskarta na nuna alhini,idanunta akan hannun nata da yayi jaa abinka da farar fata,kanta ta gyada
“Ko za’a kaita asibiti?”
“no need,bazai komai ba….in sha Allah,zanma hisham magana,zai prescribing mata pain killer,sai a kawo,she will be okay”
“To Allah yasa”baba tabawa ta amsashi,duk da bata gane komai da komai da yake fada ba
“Ki cire hijabin kisha iska” baba tabawa tace da ita,sai ta noqe taqi motsawa,ta yaya zata fidda hijabin data saka saboda yiwa jikinta shamaki,ya fuskanci sarai saboda shi din taqi motsawa,sai ya miqe kawai yana kwashe wayoyinsa ya xuba a aljihunsa
“Manya….ai ba abinda kaci” kai ya gyada
“Am okay,thanks” daga haka ya juya yana barin falon,yana kuma sanya hannunsa a aljihunsa yana laluben key din motarsa,don yau a masallacin wuro bokki yakeson yin ssallar juma’a,yanason kuma samun gaba gaba,ya tabbatar abbi ma yana ciki yanzu haka.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 46
Tunda ya dawo gidan baba tabawa tasan ya shigo,ta kuma gayawa maimunatu a fakaice indirectly cewan ya dawo din,ta yita zuba ido taga ta fita yi masa sannu da zuwa ko wani abu makamancin hakan amma bata gani ba,tunda tasan unaisa bata nan,dazun da ta zaga baya tana tsinkar musu lemon tsami taga fitarta,babu kuma alamun ta dawo.
Abun nata cin ran baba tabawa,har zuwa lokacin da suka zauna cin abincin dare,ta dubi maimunatu
“Waiku kam…..haka akewa miji?,ya fita ya wuni fafutukar nema muku abinci,ya dawo amma ko arziqin sannu da zuwa a gaya masa bai samu ba?,sa’annan ace abincin da zaici ma a gidansa ya gagaresa a kasa sammasa?,anya kuwa maimunatu?,ta yaya zaki bata dukka yardar da anni ta baki?,ta dora duk wani fatanta da burinta akanki amma kina neman bata kunya?” Qasa tayi da kanta,tana jin kunya da nauyin suna kamata tun gabanin xancan ma yaje kunnen annin,tabbas tayi kuskure da gaske,to amma kuma shi dinne…..ba irin sauran mutane bane,batasan ta yadda zata fuskanci bahagon mutum irinsa ba,yau inda ace shi din kamar hisham yake to da da sauqi sauqi,amma…..he’s totally different from what they are seeing about him,ba abu bane mai sauqi tunkararsa
“Kiyi haquri baba,baice yana buqata ba”
“Kin taba nuna damuwa ko gwada kaiwar bare ki Fatima hakan?,bari na fito miki a mutum maimunatu” baba tabawa ta fada tana gyara zamanta,abinda ya sanya maimunatu tattara hankalinta waje daya
“Gaba daya na fuskanci inda zaman aurenki ua dosa,bansan na abokiyar zamanki ya yake ba,a gajarce zan gaya miki,ba’a yankewa mutum hukunci ba tare da ka ma’amalanceshi ba,ki sauya,ki zama kamar kowacce mace a gidanta,ki sauke naki hakkin da nauyin,ko meye zai taso a gaba….ko meye zai biyo baya zaki fita a ciki,kiyimin alqawari daga yau zaki canza,inason ganinki kamar kowacce macen auren maimunatu,ina miki sha’awar hakan,na san ja’afar,yana da zuciya me kyau wani abune daban ya canzashi,kuma ina kyautata zaton duk wanda ya aro wani hali da ba nashi ba,rabashi dashi abune me sauqin gaske,zaki canza maimunatu?” Kai ta gyadawa baba tabawa a hankali,tana sake jin nauyi,saboda tana ji a ranta da gasken butulci take son tayi,tana qasan inuwar alfarmarsu,ta samu rayuwa me kyau me cike da gata,sannan ta kasa ciyar da dansu abincin da shine ya siyo shi?,bayan duka duka bata zaman wata biyu ma cikin gidan?.
Da kanta baba tabawa ta shirya abincin cikin wasu sababbin warmers masu kyau
“Dauka maza kikai masa,daga yau babu ruwanki da abokiyar zamanki,duk sanda kika fuskanci yana da buqatar abinci kuma bata nan,bata kuma bashi ba,koda ba ranar girkinki bane dauka ki bashi,ke Allah zai bawa ladan”.
Daki ta koma,ta zabo hijab cikin hijabs dinta ta sanya,ba abinda hijab din keyi sai qamsin turaren wuta na kaya,ya kuma amshi fatarta qwarai,kalar blue black,da kallo baba tabawa ta bita sanda ta fito,kamar tace mata ta canza mayafi a maimakon hijab din,amma sai kuma ta canza shawara ta qyaleta.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya,sannan ya tura hannunsa cikin sumarsa yana yamutsata,hakanan yaji kawai komai baya maaa dadi,sai yakai hannunsa guda daya ya rufe system din dake gabansa ba tare daya damu da yayi shutting down dinta ba,duk da muhimmancin hakan,sai ya koma a hankali ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune,ya kuma hade yatsunsa waje daya yana lumshe idanuwansa.