GURBIN IDO

GURBIN IDO 5

LAST FREE PAGE 05

AREWA BOOKS::HUGUMA

Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya kusan rabi da rabi na dawowar maimuntu daga kiwon ibrahim ne,wasu lokutan yakanyi gaba wani lokaci kuma tana biye dashi a baya,har sukai gida,ya tayata daure na daurewa ko sharar wajen idan bata samu tayi ba,sudan taba hira sannan ya wuce zuwa gida. Duk da cewa fiye da rabin hirar shi kadai yake abarsa,na maimunatun baya wuce eh ko a’ah. Haka kawai fa tsinci kanta da jin dadin tarayyarsu ita dashi,sai takejin wani canji na zuwa ma zuciya da rayuwarta,gaba daya wannan kadaicin babu shi,tana jin kamar ta samu wani bango da zata raba ko ta jingina dashi ko yaya yake,sabanin daa da bata da wanda zai magana da ita,magana da ake kirame dadi,idan taji magana daga bakin wani to fada ne,idan taji hira akanta to ta tsangwama ce,wani lokaci takan jima kwance duk sanda taje bacci,tana tuno irin hirarrkinsu da ibrahim,wani abun takan saki murmushi ne ta kuma juya ta gyara kwanciyarta.

Ta bangaren ibrahim din wani matsayi na musamman yakeji maimunatu na sake damu cikin ruhi da zuciyarsa,a dan zamansu ya fahimci abubuwa masu tarin yawa tattare da ita,ta banbanta qwarai da duka yaran rugar tasu,tana da wata irin nutsuwa da fasahar magana wadda ya jima baiga irinta jikin wata ‘ya mace ba,komai nata na hankali ne da sanin ya kamata,yakan zauna yana kallon yadd take iya controlling dabbobinta da baki kawai ta hanyar basu umarni,lokaci dai daiku ne takanyi amfani da sandarta wanda xaiyi wuya ma kaga hakan.

Yadda take tausayin dabbobin kamar ‘yan adam,bayan dukka alamu sun nuna sun fita samun gata da kulawa,duk da har yanzu bata taba bude baki tayi masa wata magana data shafi gidansu ba,yadda take communicating dasu kawai abun burgewa ne,duk da shima cikakken bafullace ne amma ba kasafai yake ganin hakan ba,lokuta da dama idan ya tsokanetan saidai tayi murmushi kawai,wanda kusan wannan din dabi’arta ne.

Ko sau daya himu baiyi nufin zuwa ga gaje ba kamar yadda daada ta buqata,wani lokaci ma sai ya rako maimunatu yake tunawa da batun,saidai yana ganin ba abu bane mai yiwuwa,yana da tabbacin komai zai daidaita da zarar bappansa ya dawo,wanda ya qara kwanaki kan wadanda yace zai dawo,saboda jiran haduwar kudadensa dake hannun mutane.

Yammacine lis,wanda yake busa wata ni’imtacciyar iska me dadi,yanayi ne da ya yiwa halittu da dama dadi,bawai ga dan adam kawai ba,hatta da sauran tsirrai da kuma dabbobin daketa kai kawo suna kiwo a farfajiyar wajen da ya zame musu wajen yini.

Daga can qasan bishiyar idan kakai kallonka wajen,bafullatana maimunatu ce cikin baqin saqinta,zaune saman koren hiramin da himu ya shimfida mata,shi kuma yana zaune daga gefanta saman wani dan mulmulallen dutse da bai cika girma ba.

Murmushine ke fita daga saman fuskarta,murmushin da kana kallonsa kasan kunyace cike dashi,ko a iya zamanta idan ka.kalla da kyau kasan a takure take,hannayenta sarqafe cikin juna tana kallonsu,yayin da shi kuma ibrahim ya zuba mata dukka idanunsa yana jiran amsar tambayar daya jefa mata.

Wani irin nauyi ibrahim din ke aza mata duk lokacin da ya zaunar da ita irin haka yana karanta mata kalaman soyayya……daga qarshe kuma a yau din ya tirketa kan lallai sai ta furta masa da bakinta tana sonshi,saboda bai taba jin hakan daga bakinta ba.

Wani abune kuma ita din da bata jin zata iya gaya masan,kalma ce data ji ta girmi kanta matuqa,koda baya kallonta ba zata iya fada ba,bare yadda yake zaune yana kallonta.

,sirara kuma jajayen labbanta ta motsa a hankali

“midelli…yamma tayi” dauke idanunsa yayi daga kanta yana murmushi,duk da yasan yau din sun gota lokacin komawarsun,amma tayi hakanne don ta kaucewa tambayarsa,yana mamakin kunya irin tata kawaici da kuma kamewa,sai ya miqe kawai ya dauki sandarta da a yanzun shike amfani da ita idan zasu koma gida.

     Kamar ko yaushe ya tayata suka kammala komai,yayi tsaye daga jikin wata rusashiyar bukka dake daura da wajen yana dubanta cikin murmushi

“Shikenan,tunda ba zaki bani amsa ba maimunatu zan tafi,sai jaaango?” A kunyace tayi murmushi tana kauda kanta gefe daya,ya sauke qafarsa da ya harde waje daya ya fara takawa a hankali yana barin wajen

“Ka gaida gida” ta fada cikin siririyar muryarta da ba kasafai ya fiya jinta ba,sai daya waiwayo cikin jin dadi ya kalleta yana jinjina kai sannan yaci gaba da takawa,hakanan taji kunya ta kamata,abinda yasa ta juya da sauri da nufin shigewa zuwa shiyyar da dakunansu suke. Saidai kuma cak ta tsaya,saboda ganin inna tsaye daura da ita,da alama taji komai ta kuma ga komai.

    Kallon da innar kawai ta tsareta dashi ya sanyaya mata gwiwa ya kuma sanya mata fargaba me tarin yawa,gabanta ya fara faduwa da wani mugun qarfi,duk da haka ta ari dakiya taci gaba da nufar inda innar ke tsaye tana ci gaba da kallonta

“Immoi’onni?(waye wancan?)”innar ta fada a tsawace cike da tuhuma da kuma zargi,yanayin yadda tayi mata maganar ya jefa tsoro a zuciyar maimunatun,ta qanqame jikinta waje guda,tana jiran jin saukae duka daga wajen innar,don wannan din ba sabon abu bane a wajenta

“Tambayarki nakeyi waye wancan din?”

“Sunansa ibrahim…..ya tayani qaraso da dabbobi gida ne”

“Meye hadinki dashi?” Inna ta sake tsareta da tambaya,saboda zargin da ya shiga ranta,taso taha fuskarsa amma kuma haqarta bata cimma ruwa ba,saidai batajin wanda take tunani dinne,don bata da shakka akan alqawari da yarjejeniyar dake tsakaninsu

“Babu komai” ta amsawa innar kanta a qasa,tana matse hannayenta waje guda,tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa fat fat

“Yauwa…..gwara ki rufawa kanki asiri,ke ta buɗeri ce,shi daya zai iya rufa miki asiri ya aureki,don haka kada ma ki batawa kanki lokaci ki yaudari kanki kice zaki saurari wani,kaf fadin karkarar nan bana jin akwai wanda zai iya daukarki idan bashi ba,koda an samu to yayi miki qarya,saboda haka ki kiyaye” daga haka tayi gaba zuwa garken dabbobin,tabi tana dubasu daya bayan daya tana kuma irgasu kamar yadda ta saba duk sanda maimunatun ta dawo,kai zaka zaci tana duba kaya data bawa qasurgumin barawo ajiya ne.

“Wuwuɗandu(ki share wajen)” ta bata umarni tana fita daga garken tayi gaba abinta,duk yadda takai ga gajiya hakanan dole babu yadda zatayi haka ta laluba kayan sharar ta fara gyaran wajen,duk da cewa a dazun kafin su tafi ta gyara wajen,batasan me ya bata wajen hakan ba,duk da tasan ko ba yaro idan innar taso bata wahala,zata qirqiro mata aikin ko kuma wanda yayi kama dashi,duk dai don kada ta huta,bata qaunar ganinta a zaune ko da na minti daya ne.

°°°°°°°°°°°°°°

A nutse yayi sallama cikin rumfar innar yana yafe da koren hiraminsa,dawowarsa kenan daga sallah sadam yace masa innar tana kiransa.

     Abinda ya bashi mamaki shine ganinta da yayi a tsaye tana kai kawo daga wancan bangon zuwa wannan,idanunta dake cike da fushi ta daga ta dubeshi,ba tare data amsa sallamarsa ba kai tsaye tace dashi

“Joɗa(zauna)” kasa zaman yayi,sai ya duqa daga gefe kawai yana kallonta,ta tako gabansa a hankali tana dubansa

“Inaso naji bayan ni wace mahaifiyar kake da ita?” Sosai tambayar ta bashi mamaki,har ya tada kai yana dubanta sosai kafin ya kauda kansa ganin itama shi take kallo,yaro ne shi mai tsananin biyaya,don haka bazai iya hada idanu da daadan ba

“Babu daada….amma wani abune ya faru?” Sake baci ranta yayi

“Ni kake tambaya wani abune ya faru himu?,ashe ni ba uwarka bace?,ashe ban isa na gaya maka magana kaji ba?,tun a waccar ranar ban rabaka da maimunatu ba?,ban gaya maka babu kai babu ita ba?,shine kasa qafarka kayi wancankali da maganata akan diya mace saboda bani da wani muhimmanci a wajenka?”

“Ba haka bane inna…”
“To yaya ne?” Shuru ya gifta wanda bai gaza qasa da second hudu ba

“…….ko kuwa maganar yuuma ce ta shiga kunnenka fiye da tawa ni mahaifiyarka?” Girgiza kansa yayi da sauri

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button