BABU SO HAUSA NOVELGURBIN IDO

GURBIN IDO 6

     Murmushi yuuma ta sake tana kada kai,tana matuqar sha'awar yadda suke kula da anni,tana jin cewa dama ace itama tana da arziqin da zata ramawa anni koda dan kadanne cikin irin alkhairanta gareta

“Tunda ya fada ai hakanne anni” kashingida tayi kan lallausan katifa da bargo da yuuma tayi mata shimfida da ita

“Ke rabu da shi ramatu,bokon tasu ma ta wannan qarnin tafi qarfin hankalinka,ke bakya ce sunyi muhammadiyya ba” anni ta fada tana fadawa wani tunani can,wanda har sai da yuuma ta ankara

“Yanzu anni har yau baki bar sana’a ba?” Idanunta ta bude sosai tana kallon yuuma

“Ramatu,kome arziqin mijinki jikoki da ‘ya’ya kada ki kuskura kice zaki rabu da sana’a,duk tsiya naka naka ne,koda ba’a rageka da komai ba,amma naka yana da dadi” kai yuuma ta jinjina tana gamsuwa da zancan anni,tun tale tale anni bata saba da zaman banza ba,har kawo yau da babu abinda ta nema ta rasa,ko rai tace tana so idan ana siyar dashi za’a siya mata,amma bata daina nema ba,tana da makeken gidan gona,wanda tafi ji dashi fiye da komai nata.

Tun suna hira sama sama har bacci yayi awon gaba da anni,sai a sannan yuuma ta gyara nata wajen ta kwanta itama.

*_WASHEGARI_*

K’arfe takwas na safe yuuma ke dosar dakin daada dauke da turamen atamfa gudu hudu a hannunta da shadda ta maza yadi goma,sai takalmi na maza me kyau wanda ta tabbatar zaiwa ibrahim.

Da sallama ta daga labulen dakin daadar,safiya dake zaune tana shan kunu ta amsa mata tana gaidata,dai dai lokacin daada ta fito daga uwar dakinta tana daura zani,kafadarta saqale da hijabi.

Gaisawa suka fara yi da yuuma sannan ta’ajjiye mata kayan

“Gashi inji anni”

“Too…..anni bata gajiya,to Allah ya amfana ya qara arziqi” daadan ta fada cikin farinciki,mutum ce dake matuqar son ka yiwa ‘ya’yanta alkhairi,safiya dake shan kunu tataso itama tana daga atamfofin tare da fadin

“Bara na zaba tawa kafin zubaidata iso ta dauke wadda tafi kyau……gaskiya anni nada kirki,bata gajiya” murmushi yuuma tayi ta miqe,har takusa da qofa ta juyo

“Af…..niko daada nace ba,ko ibrahim ya gaya miki inda yaje ne?,tun jiya anni keta tambayarsa,kuma kamar banga shigowarsa gidan nan ba tun shekaran jiya,abincinsa ma sai da safen nan na hada a dumame” tana shirin saka hijabinta ta amsa mata

“Eh…..na turashi gidan sukaina”
“Sukaina?” Yuuma ta maimaita a ranta cike da mamaki,saidai ba kasafai take magana akan wasu abubuwan da daada ke yankewa kan yaranta ba

“Ayyah…to Allah yasa zasu hadu,don jibi annin zata koma”

“Ba lallai gaskiya,inajin sati zaiyi acan kafin ya dawo”

“To ba laifi” yuuma ta fada tana ficewa,kanta ya daure tamau,sukainan yayar furera ce,bata da kirki ko kadan,masifaffiya ce ta bugawa a jarida,tana aure ne a wani qauye dake maqotaka da rugarsu,ta yaya za’a tura saurayi kamar himu gidan yayi kusan sati?,duk da itama tana da samarin yara kamarshi,amma kuma tafiyar ai ba ta radin kansa bane,kamar wani qaramin yaro?,da wannan tunanin yuuma ta koma dakinta,inda tabar anni da kuma laila wadda ke jira a kawo mata qosai da yuuma ta bayar a siyo mata,tace shi take sha’awa,tunda suka tashi da safen take jiyo qamshinsa.

          Suna tsaka da hira daada ta shigo a shiryenta tsaf,suka gaisa da anni sannan tayi mata godiya daga bisani tace

“Zanje na dawo yuuma,ba dadewa zanyi ba” kallonta yuuma tayi cike da mamaki,ina zata da safen nan,uwa uba kuma ma kusan dokar bappa ce,basa fita unguwa a gidan matuqar ya tafi kudu irin haka sai ya dawo,kamar anni tasan tunanin da yuuman take sai tace

“Labaran ya sassauta tsaurin nasa kenan?” Tayi maganar tana dariya.

     Kai daada ta kada fuskarta na nuna zallar damuwa

“Ko daya anni,dole ta kama na fita ne,zanje na yiwa wata yarinya data nacewa himu gargadi,waye zaiso hada iri da irin tsiya irin jaraba”,laila dake dan sauraron voice note na watsapp ta earpiece din dake kunnenta sai ta zareshi,ta miqe ta zauna sosai tana kallon daada,saboda yadda taji maganar banbarakwai,ita kanta anni dake rayuwa cikin tsakiyar birni,cikin ahali da muhallin da wayewa da kuma boko suka yiwa katutu sai data ji maganar bawai

“Tooo….ikon Allah,to….abi a sannu dai,Allah ya maganta mana”

“Ameen ameen,sai na dawo”

“Allah ya kiyaye” yuuma ta amsa mata.

Shuru yuuma tayi tana juya batun cikin ranta,me yasa daada take haka?,akan yaranta gaba daya idanunta suje rufewa?,yanzu Allah ne kadai yasan idan taje me zasu aiwatarwa da yarinyar,tunda ta riga data sani,innar laulo qawace kuma aminiya a wajenta,ita kanta banda ubangiji ya riga da ya qaddara tafi qarfinsu,da ba qaramar wuya zata bata ba ta hannun daadan.

“Wai….nace ba” laila ta fada tana duban yuuma,sai ta maida hankalinta ga laila

“Wai daada kuwa cikakkiyar bafulatana ce yuuma?” Murmushi yuuma tayi,tasan me lailan ke rayawa cikin ranta

“Gaba da baya,har gwara ni innata itama ruwa biyu ce,amma ita babu sirki”

Tun gabanin lokacin tafiyarta kiwo yayi yau din ta shirya,da wurwuri tayi wanka don kada innar laulo ta farga ta hanata yi,ta gyara jikinta sosai,ta kama jelar gashinta ta nannadesu tayi musu wata lanqwasa me qawanya me kyau,hatta da duwatsun kwalliya na kanta da hannunta sai data qara wasu,ta sake fita bufalatana zam.

Can qasan ranta takejin cewa tana yin wannan kwalliyar ne duka saboda ibrahimu,tana ji a jikinta zaiyi wuya ace yau din baizo inda take ba,saboda yaune kwanaki uku suka cika bata ganshi ba,bata saurari wani abincin safe ba,tunda ba ita zatayi ba yau,ta cika gorarta da nono wanda ta tatsa ta barwa innar laulo xatayi aikinsa za’a fiddashi kasuwar qauyen dake maqotansu wadda take ci yau.

Tun kafin innar ta tashi ta kada dabbobin kiwo,yau fes takejin zuciyarta,da wani nishadi na daban,ba kuma lallai ka fahimci haka ba,amma idan ka kalli fuskarta da kyau xakaga akwai banbancin yanayi a tattare da ita.

Wajen daya zame musu gurin zama ita da ibrahim din ta koma ta zauna bayan ta gama duk abinda ya kamata tayin,lokaci bayan lokaci tana daga kanta zuwa sama,ta wurga kallonta hagu da dama,tana ji kamar ibrahim din yana hanya,kamar yana tahowa inda take.

“Kin fara son ibrahim ne?,me yasa zuciyarki ke canzawa?” Ta yiwa kanta wannan tambayar karo kusan na uku kenan,sai ta girgiza kanta a hankali,har yanzu batace ga dalili ba,amma rashin zuwan ibrahim din a kwana uku rak sai takejin kamar tans komawa izuwa wata duhuwa ne data fita ta bari.

Duk da yadda lokaci ke qara jaa amma bata saare ba,bata rasa qwarin gwiwarta ba,taci gaba da dube dube,har daga bisani ta miqe daga wajen,ta fara kewaye cikin dabbobin,wai ko hakan zai sanya lokaci yayi gudu,ya kusantata da zuwansa wajen.

“Maimunatu na!” Kakkaurar muryar mai cike da kaushi ta doki kunnenta,ta kuma zama musaya ko ince madadi ga muryar ibrahim da take ta dako da fatan ji.

Buɗeri ne,ba shakka shine,saboda shi daya yake mata wannan kiran mafarautan,kiran dake sanya zuciyarta luguden bugu,ta sauke sandarta a hankali tana nufin juyawa zuwa gareshi,saidai kafin ta waiwaya din har ya iskota ya sha gabanta,taja baya da sauri saboda yadda kusancin dake tsakaninsu yayi qanqanta da yawa.

Fuska ya hade yana kallonta

“Meye na ja da bayan?,kin manta ke din tawa ce?” Ya fada yana nunata da yatsa,kau da kanta tayi,idanunta suka sauka ga qafarsa dake cikin huffaje,saidai shi kansa huffajen yayi daqal daqal dashi,kamar yadda sutturar jikinsa take cidin cidin,sau tari tana mamakin uban tulin qazanta irin naa buderi,abune me matuqar wuya ka sameshi fes cikin tsafta

“Amma kinyi kyau maimunatuna……ina fata babu wanda ya kallemin ke” yayi maganar yana washe baki,kanta ta daga a hankali tana duban gefe da gefanta,tana fatan kada Allah ya kawo Ibrahim a yanzu har sai buderi ya wuce,tasha jin alwashi daga bakin buderin na cewa,duk randa yaga wani ya rabi maimunatunsa,wala shakka sai ya sha jininss,tana kyautata zaton wannan na daya daga cikin dalilan daya sanya babu wanda yake mu’amala da ita

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button