GURBIN IDO 6

“Me kike nema kuma?” Ya fada yana hade rai,kai ta girgixa
“Babu komai” amsarta tasa ya saki fuska
“Na sani,kinfi kowa hankali cikin ‘yammatan rugar nan,nasan babu wanda zaki kula,ungo wannan” yayi maganar yana miqa mata wata leda.
Babu batun ma tace ba zata karba ba,don kuwa bata baki ne,don haka ta saka hannu ta karba tana cewa
“Na gode”
“Yauwa,medillu,dan men waratam?(zan tafi,yaushe zanzo?” Mummunan faduwa gabanta yayi,kada dai xancan da innar laulo ke gaya mata ya tabbata,buderi….. Buderi ne zai fara zuwa tadi wajenta?
“Ban sani ba” sandarsa ya wulwula sama ya caketa a qasa
“Shikenan,ni xan saka rana da kaina” sai ya juya abinsa ya fara tafiya,dama can shi din ba mutum ne da ya iya yin sallama ba,da ya gama abinda ya kawoshi xai saka kai ya wuce abinsa,har ya dan bata rata sai taga ya dawo da tsaya a gabanta
“Baki taba cewa kina so ba maimunatu,ate ayyam?,ayid’iyam?(zaki aureni?,kina sona?)” Banbarakwai taji maganar tasa,ta kuma rasa amsar da zata bashi,tana matuqar tsiron buderi,batajin xai kasa maketa a wajen idan tace bata sonshi,amma kuma idan tace tana sonsa din tayi masa qarya,sannan yaudara ta shigo ciki.
Dariya ya bangare da ita
“Ja’ira,kunyar gayamin kikeji kenan…..shikenan,idan nazo saiki gayamin tunda zuwan dare ne,bana ganinki sosai” daga haka ya juya abinsa yana waqar tauri.irin ta matasan fulani yana cilla sandarsa.
Baya taja a hankali ta jingina bayanta da bishiyar dake wajen,ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana lumshe idanunt,sannan ta saki ledar hannunta a hankali ta sulale zuwa qasa.
A matakin rayuwarta gaba daya ba zata iya dorar da komai ba,ba zata iya fadin meye ainihin rayuwa ba,kamar yadda ba zata iya fadin me rayuwa ta qunsa ba,meye manufar tata rayuwar?,me ta cimma?,me takeso ta cimma?,tabbas a karan kanta tasan cewa akwai abubuwa da dama da takeso ta cimma,tana da mafarkai da burika masu yawa irin na kowanne dan adam,saidai ita kanta batasan wadanne ne burikanta ba,me takeso ta cimma din,dukka bata sani ba,rayuwata qwaqwalwarta dama komai nata na tattare ne a waje daya,a yanzun kumma innar laulo ta dauko hanyar da zara qara ruguzata zuwa pieces gaba dayanta,aure da buderi?,me hakan yake nufi?,wanne buri ne a ran innar da takeso ta cimma?.
Ta jima a haka kafin ta iya bude idanuwanta,dukka wani fata da take dashi na ganin ibrahim ya fara zagwanyewa daga zuciyarta gaba daya,ganin yadda lokacin da ya dace tabar wajen zuwa gida ya gabato,jiki a mace ta miqe daga jikin bishiyar,saidai tana taku biyu takalminta ya katse
“Innalillahi” ta fada gabanta yana faduwa,ta duqa a hankali da zummar daukoshi,sai tayi arba da ledar da buderi ya kawo mata wadda ta jima da faduwa a wajen,ta sanya hannunta a nutse ta budeta,sai tayi arba da gasashen naman daji,cikin tashin zuciya ta dauki ledar gaba daya tayi wurgi da ita can cikin daji,sannan ta dauki takalminta ta duba da kyau,ya gama moruwa,bataga laifinsa ba,saboda yayi mata iyakar qoqari,bata da wata sauran dabara data rage mata,abu dayane a yanzu yayi mata saura shine ta cire dayan ta dauresu a qugunta,sannan taci gaba da tafiya da zallar tafin qafarta tana fara hade kan dabbobin,tanayi tana takatsantsan kada ta taka qaya.
[