
Tana tsaye a barandar shagon cikin shigar shadda me maik’o ruwan makuba riga da zani bata d’aura d’ankwalin shaddar ba sai ta yafa k’aramin mayafi ruwan madara a saman gyararren gashinta data d’aureshi da k’atan ribbon ruwan makuba jaka da takalmanta ruwan madara,fuskarta,ta d’auki kwalliya,ta rungume hannayenta a k’irji tana k’are mishi kallo,yana sanye cikin yadi ruwan madara kanshi ba hula saisayan dayayima gashin kanshi da k’asumbarshi sun mishi kyau,ya fito sharrr dashi k’amshin arabian perfume d’inshi ya mamaye har inda take tsaye.
Yamaida kallanshi cikin littafin amma ya kasa cigaba da abinda yakeyi. A hankali tafara taku d’ai-d’ai har tashiga shagon.Hucin numfashinta kawai yaji a gefen fuskarshi”Dan Sarai barka da hutun k’arshe mako”.
Ke malama na fad’a miki kifita harkata ko ana soyayyah dole ne!?Tamishi fari da idanun ta sannan tafara magana da wani salo irin nata na yanga “Kana ganin ba a soyayyah dole?Tagyad’a kai “To ko ba ayi za a fara hakan akan mu,kaga zamu shiga kund’in tarihin duniya”Julaibib da Kasham”what a perfect match.. Wai kai sai dubu nawa kake so in fad’a maka ina sanka, zanyi sallah koda zan 6ata da kowa nawane sannan za ka yadda dani? Haba Julaibib lokaci fa yayi da zan tunkari iyayena da maganar ka,kabani goyon baya,kaga mun kusa gama karatunmu sai kawai muyi aure hankalin mu zai kwanta”kanwa ta kar tsami k’wannafi ya kwanta.Tayi taku biyu tad’auki ragowar ruwa da yasha,tafara kur6a tana kallan shi danjin abinda zai fad’a,amma har ta shanye baiyi wani motsi ba.
“Jesus christ”!
Tafad’a cikin kad’a kai,miskilancin ka yawane dashi wallahi,wanda bai sanka ba zaiyi zatan kai kurma ne awasu lokutan fa.
Bai kalletaba yace nima sau dubu nawa kike so in fad’a miki bazan iya auren kiba kafin ki yadda dani?!
No No No tad’aga mishi hannu ni ba irin wannan banziyar amsar zaka bani ba.
Musaddiq yashigo da fara’arshi ganinta yasa shi d’aure fuska.Suka gaisa a tak’aice tana tambayarshi ya d’aliban makarantar da yake TP?Ya amsa da lafiya lau a tak’aice.Yamik’ama Julaibib hannu sukayi musafaha. Suka cigaba da maganganun su zuwa can Musaddiq ya kalleymta”Wai lafiya kuwa? Tamishi wani kallo”Kaima ai kasan tatsuniyar gizo bata wuce k’ok’i “Musaddiq ban sanka da irin wannan halin ba.Yadauke kai daga kallan datake mishi “Eh ai kinsan kamawa takeyi a d’aure me d’aurewa,Zama da mad’aukin kanwa kuma shi ke kawo farin kai.
Musadd…yatareta da sauri “A ah kiyi hak’uri kawai matata tace bata yadda magana tadinga shiga tsakanin muba. Matarka?Ta tamabaye da mamaki Eh haka nace matata.Tad’an ta6e baki”to kenan tsoronta kakaji? A ah Ba tsoronta nake ji ba,sai dai bana san 6acin ranta kona sisin k’wabo.Ahaf,tawatsa hannaye “ba cinya ba k’afar baya.tama Julaibib lallausan murmushin ta”ni zan wuce sai mun had’u ranar litini a makaranta”tajuya tayi tafiyarta.
Ranar litini itace da darasin farko a ajinsu Sudaida tana shiga ta tarar dasu a tsaitsaye suna caccar baki.Tabisu da kallo “Lafiya kuka cika ajin da hayagaga bud’ar kan karya?Linda tafara mata bayani “ranar juma’a Sudaida tana cikin yan weekend-sanitation na wancan makon, amma takama hanya tayi tafiyarta ba tare da tayi kome ba,shine yanzu muke fad’a mata wannan juma’ar dole ta tsaya suyi ita da Dinatu,shine tafara masifa wai ba wanda ya isa yasata tayi sai idan taga damar tsayawa tayine kawai zata tsaya,wancan makon ne take da aiki batayi ba kuma ai yariga ya wuce. Kasham tace”baki kyautaba maimakon ki bada hak’uri kome yawuce shine sai ki rufesu da masifa?Sudaida ta turo baki gaba”to ai bani kad’ai bace Dinatu ma tafito indai gaskiyane abun.Tatsareta da manyan idanunta masu maik’o”Idan kuma karya ne fa?Sudaida tad’an motsa kafad’a”shikenan sai tayi zamanta dama idan aka tsaneka ko ruwa ka fad’a sai ace ka ta da k’ura”tafara k’unk’uni.
Kasham tajijjiga kai”ban ta6a dukan kowa ba tunda nazo makarantar nan,amma yau za kisha na jaki,jeki Staff-Room ki jirani.Yan ajin suka zaro idanu, wasu suka d’ora hannayensu aka”Yau Sudaida zata kad’e har ganyanta a wajan malamai.Har ta kusa fita daga ajin sai kuma takirata”Hey come back”Sudaida tadawo tana kumburi”Kneel down here”takai gwiwoyinta k’asa tana k’unk’uni.Kasham tanunata da yatsa ke”If you dare say something again…I will deal with you.
Takira Dinatu tana tambayarta me yasa baki tsaya an gyara ko in dake ba? Cikin rawar murya”Tace bani da lafiya ina kwance a hostel ranarma ban shigo ajiba”. Hakane? Ta tambayi sauran d’aliban suka amsa da eh.sai tadan dafa kafad’rta”Amma yanzu kinji sauk’i?Eh malama naji sauk’i.To jeki zauna ko.Tajuya gaban allo tafara rubutu,tagama rubutawa tajuyo tana fuskantar d’aliban tana musu bayanin sabon darasin da suka shiga.
Sudaida tasake kallan siririn farin agogon fatar dake daure ahannunta na dama,lokacin tama ya kusa k’arewa amma dan wulak’anci ta barta a durk’ushe, gwiwoyinta har sunyi tsami dan rashin tausayi da imani,tabi k’eyarta har zuwan gashin kanta da harara, wannan uban gashin k’aryane ba na ta bane wig ne,ga wani d’inkin rashin mutunci da tayi da atamfar jikinta,koya tayi tasa oho?Taja dogon tsakin dayasa duk yan ajin suka kalleta da mad’aukak’nn mamaki.
Kasham tasake jijjiga kai”ni keki jama tsaki ko?Wallahi yau sai nayi maganin bakin rashin kunya.Tashi kafad’a min abinda yasa kikaki tsayawa ranar juma’a.Taturo baki gaba”to ai Yaya d’ansarai ne yace shi bazai zauna jirana yarasa sallar juma’a ba,ni kuma shine na bishi. Wani lallausan murmushi yasu6uce mata har kyawawan fararan hak’oranta suka bayyana,jin ta ambaci d’ansarai wato dama k’anwarshice wannan? Kawai sai ta rik’o hannunta suka fita.
Ajin yakaure da hayaniya,wasu suna mata ALLAH yak’ara gwamma ayi maganin bakin tsiwan, wasu masu raunin zuciya har idanunsu sun cika da kwalla na tausayin halin da zata tsinci kanta aciki indai tashiga dak’in malamai,musamman kuma da Kasham tayi wannan murmushin sai suke ganin lallai na tanadin wuyane da ALLAH ne kad’ai zai ceci Sudaida.
Sun d’anyi nisa da ajin sannan suka tsaya.Kasham tadafa kafad’arta “Kidaina irin wannan halin bashi dakyau,masoya da mak’iya ba a guzurinsu halinka zai baka su a duk inda kaje”Next time karki sake binshi sai kinyi aikinki kingane ko? Tagyad’a kai.Nima kiyi hak’uri da abinda namiki.Tayi mirmishi “bakome jeki aji ga malamin lissafinku can zai shiga”Always be a good student.
Takoma aji tana wata tafiya irin ta eh yane naci dubu sai ceto.d’aliban suka zaro idanuna suna binta da kallan sama da k’asa alamar”a ah abin mamaki wai Baturiya da suna manga.Dan ba hawaye ba wata alama ta an bata na jaki,amma ba damar tambayarta ya akayi aka haihu a ragaya?Danga Malamin lissafi nan yahad’e girar sama da k’asa,dan shima k’wallan shegene shi yasa ko d’an k’us k’us k’us d’in nan na d’alibai basuyiba sai an tashi tara za a baje kome a fai-fai.Sudaida tamusu fari tana wani lallausan murmushi sannan tazauna awajan zamanta,Suna had’a idanu dashi itama tashiga taitaiyinta.
Suna ciye-ciyensu dasu a’isha a sanda aka buga tara,sauran yan ajin sun zagayesu ana tambayarta an daketa kuwa?Ya akayi tabarta tadawo aji da sauri?Sun dauka har a buga tara basu gama horata ba,bulala nawa aka mata?Tawani hura hanci cikin kuri kamar gaske “tama isa ta dakeni ne?Ai wallahi ko kura ta san gidan me babban sanda.Suka kyalkyale da dariya suna ihu;shegiya yar gidan Ibrahim-Mai Lambu, tad’aga musu hannu”a ah kar wasa yayi wasa a tsikari uwar miji fa.Ni yar sunna ce dan haka kar wacce takuma shegan tani ehemmm.