ALKALI NE Page 1 to 10

Ina mik’a godiya ga dukkanin masoyana. Wannan littafin k’irk’irarre ne, banyishi dan cin zarafin wani ba, ina fatan Allah yasa kowa ya amfana da abinda yake ciki amin.
*LAGOS*
Cike babbar kotun garin Lagos take da jama’a, wasu basu da alak’a da wannan shari’ar, amma yanda ake fad’in yanayin shari’ar da kuma wanda aka maida shari’ar wajensa yasa kowa yake so yaje domin yaji yanda zata kasance.
Kasancewar lauyen da aka maida shari’ar wajensa sabon zuwa ne hakan yasa kowa yake son ya ganshi, domin an sanar cewa wannan zaman shine zama na k’arshe, saboda tsohon lauya ya kasa kawo kwararan shedu hakan yasa shari’ar ta gamsu da shedun abokin karawarsa.
Tsaye mutane suke a bakin kotun suna jiran abasu izinin shiga kafin Alkali ya iso. Wasu Matasa ne da suke gefe guda suke magana akan wannan shari’ar. ‘Daya daga cikinsu yake fad’in abokina ko kasan nima ban gamsu cewar gaskiya ce wannan lauyen yake fad’a ba, taya za’ace bayan mutum ya mutu da wata biyar sannan ace matarsa tana da ciki har na wata ukku, kai da gaji ma kasan rainin hankali ne har sai sunzo wata kotu.
‘Dayen yace kuma wannan shari’ar kotun musulunci yakamata ace an kaita ba wannan kotun ba, gashinan yau zuwa na ukku ne amma an kasa tsaida mafita, da kotun musulunci ce tuni an wuce wajen amma hada wani sake lauya, ai zaizo muji tashi basirar.
Murmushi wanda yake gefensu yayi yana fad’in wallahi kuna bani dariya, kunsan fa ance shari’a sab’anin hankali, abinda wani yayi ya kasa sai kuga wani yayi, koshi Alkalin sai ya kasa gano abinda wani lauyen zai gano, duk da ance sabon lauya ne babu wanda yasan basirar da Allah ya bashi, kuma ba jiya bane ya amshi shari’ar kusan sati guda kenan rabon mu da nan, kunga kuwa acikin sati d’aya zai iya had’a shedu masu kyau idan yana da basira, koda kotun musulunci aka kai wannan shari’ar ai dole sai da shedu, dan haka muyi masu fatan alkhairi shine zaifi, danni wallahi tausayin matar nakeyi, itace k’arama acikin matan Alhajin, kuma itace ta ukku fa, kasan unguwar mu d’aya dasu babu abinda ban sani ba akan irin zaman da sukeyi da abokan zamanta, kasan halin mata, akan kishi babu abinda bazasu iya ba, kuma nasan halin matar, duk da basu dad’e da Alhaji ba amma mutane suna fad’ar kyan halinta, shiyasa jikina be yarda da wancan lauyen ba, domin ina yawan ganinshi a unguwar mu yazo wajen sauran matan.
Jinjina kai sauran sukayi suna fad’in to Allah ya bayyana gaskiya. Yace amin. Tashi sukayi ganin an fara shiga ciki.
Kowa ya sami waje ya zauna ana jiran shigowar Alkali. Wani Matashin yaro ne wanda bazai wuce shekara 32 zuwa da 33 ba yashigo kotun yana sanye da kayan aikinshi, idanuwansa suna b’oye cikin farin gilashi hannunsa d’auke da k’aramar jaka.
Yanayin takunsa yaja hankulan mutanan da suke zaune a kotun, koda ganinshi kowa ya gane shine sabon lauyen da ake magana akanshi. Wasu da yawa suna mamakin ganinshi a haka, sun d’auka zasu ga wani babban mutum sai gashi sunga Matashi mai jini ajika.
Yana k’arasowa wajen da aka tanadar masu domin zama ya fara mik’a hannu ga sauran ‘yan uwansa lauyoyi suna gaisawa. Ko da yazo kan mutum na k’arshe bayan ya bashi hannu sai yaji bai sakeshi ba, d’ago kai yayi yana kallonshi. Babban mutum ne, yasan ya girme mashi a shekaru. Kallon hannunshi ya sakeyi ganin har lokacin bai sakeshi ba kuma murmushi bai b’ace daga fuskar mutumin ba.
Murmushi shima ya sakar mashi yana kauda kai. Sunana *Brr. Nuhu Bajinta*, amma amfi kirana da *Brr. Bajinta*, nine wanda yake jagorantar wannan shari’a, wato abokin karawar ka. Murmushi yayi yana fad’in sunana *Brr. RA’EEZ HAMZA MWD*, nine sabon lauyen daya amshi wannan shari’a.
Jinjina kai Brr. Bajinta yayi yana fad’in muna maka maraba da shigowa wannan babbar kotu mai albarka, Allah ya baka sa’a a wannan aikin namu mai had’ari da wahala. Brr. Ra’eez yace amin nagode.
Zama sukayi suna jiran k’arasowar Alkali. Wanda yake kusa da Brr. Ra’eez ya sake bashi hannu yana fad’in sunana *Brr. JABEER USMAN*, ina aiki a wannan kotun kusan shekara d’aya da farawata kenan, ina maka fatan alkhairi da zuwa wannan kotu. Murmushi Brr. Ra’eez yayi yana fad’in nagode Jabeer Allah ya bamu zaman lafiya. Yace amin.
Shigowar Alkali yasa kowa ya tashi. Bayan ya zauna kowa ya zauna tare da natsuwa. Bayan da Alkali ya gama ‘yan rubuce-rubucensa sannan ya bada izinin acigaba da gabatar da shari’ar.
Tashi magatakarda yayi yana fad’in, a yau sha hud’u ga watan oktoba shekara ta 2019, wannan kotu zata cigaba da sauraron k’arar da akeyi akan iyalan gidan Alhaji Bala wanda matanshi guda biyu suke k’arar amaryarsa Amina akan fitowar ciki a jikinta bayan mutuwar mijinsu wanda suka tabbatar ba nashi bane, wannan shari’ar da ake gabatarwa ta tashi daga hannun lauyen da yake kare wacce ake k’ara ta koma wajen sabon lauya mai suna Brr. Ra’eez Mai Wada wanda aka yimasa canjin aiki zuwa wannan kotu.
Risnawa yayi yana mik’ama Alkali takarda. Bayan daya gama dubawa yace ina sabon lauya kotu tana so ka gabatar da kanka.
Fitowa yayi yana fad’in sunana Brr. Ra’eez Hamza MWD, kuma nine lauyen daya amshi wannan shari’a a wajen abokin aikina. Jinjina kai Alkali yayi yana fad’in lauyen da zai fara bismillah.
Komawa Brr. Ra’eez yayi ya zauna dan beyi niyar farawa ba, yafiso ya zauna yaga kamun Brr.. Bajinta. Fitowa Brr. Bajinta yayi yana fad’in ya mai shari’a, har yanzu Amina bata amsa laifin da ake zarginta ba, haka kuma taki furta sunan wanda yayi mata wannan cikin, duk da matanshi sun tabbatar da Alhaji bai tab’a haihuwa ba a duk zaman da suke dashi, kuma sun dad’e atare dashi bai haihu ba, dalilin rashin haihuwar ne yasa ya k’aro aure, har sukayi zaman kusan shekara Amina bata tab’a b’atan wata ba sai gashi bayan mutuwar Alhaji ciki ya bayyana a jikinta har na wata ukku wanda likita ya tabbatar Alhaji baya haihuwa, kuma kowa ya sheda bayan mutuwar Alhaji sannan cikin ya bayyana wanda Alhaji ya riga cikin barin duniya kafin ya bayyana.
Takowa yayi wajen da Amina take tsaye yana fad’in Malama Amina ya kamata zuwa yanzu ki bud’e baki ki fad’a mana gaskiyar wannan al’amari, be kamata kicigaba da wahalar da kotu ba, agabanki aka gabatar da manyan hujjoji, kowa ya aminta da hujjojin yakamata kema ki bayyana wanda yayi wannan cikin domin ki sauk’ak’a ma kotu wahala.
Tashi Brr. Ra’eez yayi yana fad’in ya mai shari’a, bai kamata lauya yarik’a takura wadda ake zargi ba, Amina tana da ikon ta fad’i gaskiya akan abinda ta sani, bai zaima dole dan kowa ya amince da abinda wani ya fad’a ba ace itama dole ta amince. Nagode ya mai shari’a.
Kallon Brr. Barjinta Alkali yayi yana fad’in ka gyara kalamanka. Risnawa yayi yana fad’in za’a kiyaye ya mai shari’a. Iya kar abinda zan fad’a kenan, ina rokon wannan kotu data yanke wannan hukunci domin magada su san halin da suke ciki. Nagode ya mai shari’a.
Tashi Brr. Ra’eez yayi yana fad’in ya mai shari’a inaso nayima Alhaji Kabir babban aminin marigayi wasu tambayoyi. Da sauri Brr. Bajinta ya kalli Brr. Ra’eez jin wata magana da yazo da ita, shi tunda aka fara shari’a beyi tunanin sako aminin Marigayi ba domin yasan beda wani amfani a shari’ar, sai gashi Ra’eez ya gayyatosa a cikin shari’ar.