HALIN GIRMA 1

“Iman!” Tsayawa tayi chak, ta kalle su kad’an sannan tace
“Sannun ku.”
Murmushi Bashir din yayi mata sannan yace
“Malamar islamiyya, sannu da zuwa.”
Bata amsa masa ba dan yadda yayi maganar taji akwai alamun rainin wayo
“Ya akayi?” Tace tana kallon Zeenat.
“Babu!” Ta dage kafadar ta.
“Ok!” Tace tana cigaba da tafiyar ta, tana jin sanda suka kwashe da dariya, ta dan ji babu dadi a ranta amma ta danne, ta karasa gidan duk ranta babu dadi. Da gaske ta ji zuciyar ta, ta amince da Bashir farkon magana da yayi mata har tana addu’ar Allah ya tabbatar mata dashi, sai gashi tun ba’a je ko ina ba, ya koma wajen Zeenat wadda ko da ace da wasa yaje wajen Zeenat din toh babu ita babu shi har abadah.
A gate taci karo da Maryam, a kalla ba kamar sauran ba, Maryam ta fuskance ta, shiyasa tasu tazo daya sosai, duk da ba wata doguwar hiraa ce ke hada su ba amma ta kan sake da ita fiye da kowa. Bikin su za’a yi su hudu a gidan. Maryam din sai Bilkisu, Aysha da Amina. Daga su sai ita da Zeenat da yar gidan Abba Musa Rabi’ah sune a layi, duk cikin su babu wanda bashi da me son shi amma banda ita da ta gagara samun wanda ma zai tsaya din.
Bangaren Gajin suka wuce tana mata hira akan shirye shiryen bikin, rabin hankalin ta baya kan Maryam din har suka karasa, suna shiga ana kiran sallar magriba sai kawai suka wuce sukayi alwala.
Bayan sun idar ne Gaji ta kalle su tana kan abun sallah kamar zatayi magana sai kuma ta fasa. Sai da ta gama ta tashi sannan tace
“Maryama daga ina haka ke da alhuda-huda?”
“Daga islamiyya Iman take ni kuma na fito zan taho nan muka hadu.”
“Toh ku tashi ku dubo min ko an gama tuwo dan cikina ya soma kiran chiroma.”
“Wai Gaji wasa wasa fa kina da ci wallahi.”
“Saukin ta ba kowa ke siyan kayan abincin ba ‘yaya na ne, ko zaku hana su bani ne?”
Rik’e baki Iman tayi tana dariya Maryam tace
“Bamu isa ba ai Gaji, aci dadi lafiya lokacin ki ne.”
” Yafi muku sauki dai, kema alhuda-huda kin fara zama su balki ko? Kika biye musu baki da bakin da zaki iya karawa dani atau.”
Shiru tayi bata ce komai ba, suka zagaya kitchen din Gajin da ke baya suka hado mata abincin suka kawo mata sannan suka zauna suka ci tare, lokaci lokaci Maryam na tsokanar ta, ita dai Iman jin su kawai take har aka gama suka tattare kayan sannan Maryam ta tafi ta barta a nan, sai kawai ta zame tayi kwanciyar ta a saman doguwar kujerar ta fad’a kundin tunani kamar yadda ta saba.
“Yaya Iman kizo inji Maama, zamu ci abinci kar ya huce baki ci ba, kiyi sauri.”
Muryar Marwan ta iso daidai kunnenta, da sauri ta tashi zaune, sai kuma ta mike da sauri tana jin sanda Gaji tace
“Hajara ba dai kirki ba, yadda kike kula da yarinyar nan ubangiji Allah ya kula miki da naki yayan.”
Wasu guntayen hawaye ne taji suna neman zubo mata, tayi saurin maidasu ta kara sauri zuwa shashen nasu domin amsa kiran Maama.
_*KASHI NA BIYAR*_
_*KASHI NA BIYAR*_
_*KASHI NA BIYAR*_
_*KASHI NA BIYAR*_
*_KASHI NA BIYAR_*
_*SABUWAR SHEKARA, SABUWAR TAFIYA, SABON SALO*_
????????. ????????. ????????.
_*ZAFAFA BIYAR!! KASHI NA BIYAR!! SINADARIN ZAFAFA5 (BEST TOP 5)*_
_*INA MASOYA KUMA MAKARANTA, MABIYA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR? KU MATSO DOMIN NESA TAZO KUSA, KU SHARE HAWAYEN KU, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE DANNOWA DA TURURUN SU, MASU ZAFAFAN FADAKARWA, NISHADANTARWA HAD’I DA ZAFAFAN KAUNA MARAR GAURAYE.*_
_*YAN BIYAR DIN NAKU KAMAR KO DA YAUSHE SUNE:*_
_*SAFIYYAH HUGUMA*_
_DABI’AR ZUCIYA_
2-_*BILYN ABDULL*_
_TAKUN SAK’A_
_*3- MAMUH GEE*_
_DEEN MARSHALL_
_*4-HAFSAT RANO*_
_HALIN GIRMA_
_*5~NANA HAFSAT (MISS XOXO)*_
_SO DA ZUCIYA❤️_
1
_DAGA TASKAR *SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAYI; DAURIN BOYE, ALKAWARIN ALLAH, ALKIBLA, SIRADIN RAYUWA TA SAKE ZUWA DA WANI RANTSATTSE MAI SUNA:_ *_ƊABI’AR ZUCIYA_*????
2
_DAGA ALKALAMIN *HAFSAT RANO* , MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAZO MUKE A BAYA DA, DAURIN GORO, ABINDA KE CIKIN ZUCIYA, SAUYIN KADDARA, MABUDIN ZUCIYA. WANNAN KARON TAZO DA WANI SABON SALON MAI SUNA:_ *_HALIN GIRMA_*
3
_DAGA SALON TAFIYAR *MAMUH GEE* ,WADDA A LITTATTAFAN TA NA ZAFAFA TAYI; MIN QALB, BURI DAYA, KAUNAR MU, UBAYD MALEEK. WANNAN TAFIYAR TAZO DA WANI DADDA’DA MAI SUNA:_ *_DEEN MARSHALL_*????
4
_DAGA TAFIYAR RUBUTUN *NANA HAFSAT (MISS XOXO)* WADDA A ZAFAFAN BAYA TAYI WASU KAMAR SU: KAI MIN HALACCI, KIBIYAR AJALI, DALAAL, IGIYAR ZATO. WANNAN NEXT LEVEL DIN TAZO DA WANI MAI TAKEN:_ _*SO DA ZUCIYA*❤️_
5
_DAGA SALON RUBUTUN *BILYN ABDULL* MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAYI NA BAYA IRIN SU: WUTSIYAR RAKUMI, SARAN BOYE, MAKAUNIYAR KADDARA, GUDU DA WAIWAYE. WANNAN SABUWAR TAFIYAR TAZO DA WANI MAI SUNA:_ *_TAKUN SAKA????_*
☄️????????✨????
_*KADA KU BARI AYI BABU KU, KUZO A DAMA DAKU A SABUWAR TAFIYA MAI TAKEN SABON SALO, SINADARIN ZAFAFA BEST TOP 5, MASU ZAFAFAN DARUSSA, NA RAYUWA, WANDA DUK WANI MAKARANCI BA ZAI RASA DARUSSAN DAUKA ACIKI BA.*_
_*GUDA DAYA: 300*_
_*BIYU 400*_
_*UKU 500*_
_*HUDU 700*_
*_BIYAR DUBU DAYA (1k)_*
*_YAN TALLAH SAMAN SHAFI NAIRA 300, ‘KASAN SHAFI KUMA 200 NE_*
_*YADDA ZAKU BIYA*_
*_ZAKU TURA KUDINKU ACIKIN WANNAN ASUSUN NA BANKI_*????????????????
*6019473875*
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai katura shedar biyanka ta wannan number*????????????
08184017082
_*IDAN KATIN MTN NE, KO VTU SAI ATURO ZUWA GA*_????????????????
09134848107
_#TEAM ZAFAFA BIYAR_????????
[ad_2]