HALIN GIRMA 16

Daya bayan daya aka dinga bud’e kayan, tun mutane na irgawa har kowa ma ya gaji aka zuba ido ana kallon tarin dukiya, dukiya me sunan dukiya, dangin Abba da Mama ta dinga dagawa kai sai suka zama kamar sune kawai a wajen, farin ciki suke dama kowa yaji haushin abinda Maman tayi a dan tsakanin gabatowar bikin, sai kuma yadda ta dinga yada habaici a ranar da za’a kawo kayan wanda suka tabbatar dasu take shiyasa suka ji haushin ta sosai, amma yanzu da haka ta faru sai suka hau murna suka dinga yin abu da gayya dan su kara haukata Maman.
Tashi sukayi bayan an gama ganin kayan, aka damka duk wasu abubuwan da suke da muhimmanci sosai kamar golds da takardun gida da keys a hannun kannen su Abba sannan suka yi musu sallama, abubuwn da aka shirya da sunan Zeenat suka je suka dauko aka saka musu a mota, basu ma so karba ba amma yadda suka dinga insisting yasaka suka karba dan kar suga kamar sun raina musu ne.
Suna gama fita daga gidan masu kawo kayan Zeenat ta shigowa, mata ne kwantsam masu mugun yawa, masu goyo ne, gasu nan harda wanda suka ciko bus suka zo. Ana kokarin daga Mama a maida ta cikin daki sanarwar zuwan su ya katse su, a sanyaye suka dawo suka zauna, suka shigo bayan an matsar da kayan Iman an tura wasu dakin Abba da dakin Maman.
Da kallon bakin ciki Mama take bin su, kamar ta tashi ta hau bugun su haka taji, yaran da suka zo dasu suka dinga ihu na goyen sai da aka sakko su, na hannu kuwa suka hau wasa a falon. Gaisawa akayi suka gabatar da kansu, kafin ma su dire sunan Zeenat din Mama ta ja numfashi da take jin kamar zai fice daga jikin ta.
“Kuyi hakuri asthma ce da ita nema take Kuma ta tashi tun dazu, tashi Yaya mu shiga ciki ki huta.”
Aunty Maimuna kanwar Maman tayi saurin rufawa ta janye Maman dan ta hango matsala babba, kamar ma kokawa take da numfashiin ta. Suna shiga dakin ta kurma ihu, ihun da kowa ya ji shi, da tayi sauri ta saka hannu ta rufe mata baki
“Haba Yaya Hajara, ai sai aji kunya, dan Allah kiyi hakuri.”
“Kutmar uban hakuri, kike ce min nayi hakuri? Bayan kinga abinda ya faru? Kinga yadda Ibrahim ya munafurce ni da yan uwansa? Bayan duk halaccin da nayi musu ? Amma kike cewa nayi hakuri, ke kinsan me nake ji? Innalillah, wayyo Allah na.”
” Ni dai kiyi hakuri, ko ma menene ki bari a gama taron nan, kinga mutane zasu tafi dake a baki.”
” Taro? Ke kina ganin za’a cigaba da taron nan?”
” Toh me za’a yi Yaya?”
” Ba zai yiwu ba, wallahi sai dai a fasa auren, amma ba zan bari bakin ciki ya kashe ni ba a banza.” Sai ta sake fashewa da kuka, kuka irin wiwi din nan da kana gani zaka tabbatar da ba karamin kuka mutum yake ba. Duk yadda Aunty Maimuna taso ta bata baki tayi hakuri ta kasa, sai kawai ta fito ta rufo mata kofar ta dawo wajen bakin, lokacin har an soma bud’e kayan, akwatu na guda hudu sai kit daya, da kayan ta masu kyau daidai da tsarin akwatunan, amma ganin da mutane sukayi wa kayan Iman ya saka zasu ga na Zeenat din kamar bola, a daddage kowa ya kalla, suka dauko dubu ashirin suka ce gashi nan ta kai dinki ba’a samu an dinka ba saboda kurewa lokaci. Daga haka sukayi musu sallama aka je dakin Mama a dauko ragowar kayan da suka rage ta ce idan an basu ko ruwa ba’a za’a basu ba, da k’yar Aunty Maimuna ta bata hakuri aka saka musu ruwa da lemo a bayan mota suka tafi.
Daya bayan daya yan uwan Abba suka zo suka kwashe kayan iman suka maida su bangaren Gaji a cewar su kar bakin ciki da kishi ya saka Mama ta saka wuta ta kona su.
Hauka hauka Maman ta soma da suka shigo, kowa yayi mata banza suka dinga dariya suna yada mata da magana, suka kwashe komai suka yi tafiyar su. Jiki a sanyaye kawayen Mama suka dinga sulalewa suna guduwa kowa burin sa ya isa gida ya bada labarin abinda ya faru.
Zeenat na wajen saloon suna ta waya da Bashir kiran Maman yake ta shigowa tana kin dagawa, da dai taga kiran ya ishe ta sai tace ya bari ta daga wayar Maman, katse nasa kiran tayi ta daga na Maman.
“Kina gidan uban wa wai?”
“Mama kinsan fa ina saloon.”
“Toh ki bar komai kike ki taho gida, kizo yanzu ki same ni.”
“Mama ban gama ba, kuma kinga zamu je mu siyo head din da zan saka da dinner da Bashir daga nan…”
“Bashir din yaci abu ta kaza uban sa, na rantse da Allah kika bari man da awa guda baki dawo gida ba, sai kinga yadda zan miki” tana kaiwa nan ta katse kiran, saroro Zeenat din tayi rik’e da wayar cike da mamakin Maman.
“Me ya faru kuma?” Ta Tambayi kanta cike da mamaki.
Safa da Marwa Mama ta dinga yi a daki tana jiran Zeenat, ko sama da kasa zata hade ba zata yarda ayi auren nan ba, tasan idan ita kanta Zeenat din tazo taga abinda ya faru zata ce ta fasa ne, shege matsiyaci dama munafurtar su yayi kenan.
” Yaya Hajara da kin zauna kin nutsu, tashin hankali ba zai gyara komai ba.”
” Ba zaki gane halin da nake ciki ba, ba zaki gane ba, ina cikin tashin hankali, bayan kunyar da nake ciki.” Ta fad’a tana cigaba da zagayen, idanun ta ya kada yayi jajur taci kuka ta godewa Allah. Jugum sukayi kowa da abinda yake rayawa a ransa. A haka Zeenat ta shigo ta same su, Mama tayi kanta da sauri ta fizgo hannun ta da sauri.
” Kika ce min talaka ne, kayan jikin sa ma a yayyage, daga gani bashi da komai.”
“Waye? Wai Mama menene ya faru?”
” Ubanki, bake ce kika ce min wanda yazo neman auren Iman talaka bane?”
” Eh Mama, dan baki ganshi ba.”
Dundu Mama ta kai mata ta goce cikin bacin rai tace
” Toh dan ubanki dan sarki ne.”
” Sarki!!!” Zeenat ta fad’a da karfi tana zaro ido
*_ZAFAFA BIYAR 2022????_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_1aHALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*????????????
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*????????
09134848107
[ad_2]