HALIN GIRMA 2

*HALIN GIRMA!*©️®️Hafsat Rano.
FREE PAGE
(2)
*****
Takalmin Abban su da ta gani a kofar shiga falon yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta bud’e labulen hade da sallama, idonta ya sauka a cikin na Mama da take kallon kofar, tayi
mata wani kallo me cike da ma’anoni da ba kowa ne zai gane ba sai ita kadai da ta san manufar sa.”Abba barka da gida.” Tace tana zamewa k’asa
“Yawwa Uwata, kina ina haka mamanki na ta neman ki kinsan bata so kici abincin da ya huce ko? Ga yanayi na sanyin nan ba komai ne yake rik’e zafin sa ba.”
“Ina wajen Gaji ne.” Tace tana sake yin kasa da kanta.
“Toh dai a dinga kula ana abinda ya kamata kinji? Allah yayi muku albarka.”
“Amin.” Tace tana mikewa ta shige dakin su da dan sauri tana avoiding idon Maman da ta rakata dashi. D’are-d’are ta tarar da Zeenat a saman gadon tana waya, wuceta tayi ta bud’e jakar kayan ta, ta sauya kayan jikin ta da wasu ta ninke Hijab din sannan ta dawo ta saka abun sallah a k’asa ta zauna ta ciro littafin da akayi musu a islamiya ta soma karantawa a hankali.
“Malama kina distracting dina.”
Ta zare wayar daga kunnen ta tayi maganar a chunkushe. Banza tayi mata ta cigaba da karatun ta ba tare da ta daina ba.
“Mtsww!.” Ta ja dogon tsaki
“Baby bari zan kiraka ina zuwa.*
“Owk dear, ina jira.”
Katse kiran tayi ta zuro kafafunta daidai wajen da Iman din take zaune
“Malama duk karatun da kikayi a islamiya be ishe ki ba, sai kinzo kin cika mana kunne mu san kina zuwa makaranta, bayan kowa yasan dalilin da ya saka kika nace da zuwa ko kya samu ya sayyadi ya ce yana so.”
Bata tanka mata ba, hakan ya sake kular da Zeenat din, ta saka hannu zata warce littafin tayi saurin janyewa ta mike tsaye,
“Wallahi sai dai ki hakura da karatun ko kije chan kiyi, naga ma aiki ne gaban ki kin sani tsabar kinibibi so kike sai ya jiyo ki kina karatu. ”
” Kinga duk abinda kike yi bana taba tanka miki, ba wai don ina tsoron ki bane ko wani abu, kawai bana son tashin hankali ne da hayaniya. ”
” Toh ki tanka min ma mana, wallahi yanzu zanje na hado ki da Mama.”
Bata sake magana ba ta fice daga dakin dan ba karamin aikin Maman bane ta hanata zuwa makarantar na wani lokaci, sai kawai ta zarce kitchen ta tarar da kayan wanke-wanke tuli guda, ta nannade hannun ta tasoma wankewa. Abincin da ta gani a tukunya ta san nata ne, yayi mugun sanyi ita kuma a ka’idar ta bata cin abinci me sanyi, ko ruwan sanyi bata sha a rayuwarta balle yanzu da ake zuga sanyi sosai., gudun ta barshi bata ci ba gobe a hanata yasa ta samu leda ta juye a ciki ta wanke tukunyar ta goge gas da k’asan kitchen din ta gyara komai tsaf sannan ta fito da ledar ta zagaya ta kofar baya ta fita zuwa part din Gaji, ta samu me aikinta ta bata sannan ta dawo ta dauko katifar ta a store ta wuce dakin.
Har lokacin Zeenat bata gama wayar ba, toilet ta wuce ta dauro alwala tazo tayi shafa’i da wutri sannan ta kwanta ta rufe kanta gaba daya da dan yalolon zanin gadon da duk ya yayyage ta gefe da gefe ta kudundune da haka bacci ya dauke ta.
Da safe ta tashi kamar kullum tayi ayyukan da suka zama wajibi akanta, kasancewar litinin ce sai ta yi wanka kawai ta wuce shashen Gaji bayan ta tabbatar da fitar Mama tun sassafe, a chan taci abincin ta sannan ta kwanta bacci. Sai da rana ta soma dagawa sannan ta koma ta daura girkin rana,ta gama kafin lokacin tafiya islamiya, ta dauki na Gaji ta kai mata ta sake zama tana jiran lokacin ya cika.
“Yaki takwara ta, zo nan.” Gajin tace tana daga zaune a in da take
“Me yake damun ki?”
“Na’am?”
“Fad’a min idan kina da wata matsala ne, na dade ina lura da yanayin rashin walwalar ki, sai dai na kan dauki hakan a matsayin halitta, amma kuma jiya sai abun yazo kaina, na dinga tunanin ko dai kina da wata damuwa ne? Da kika kasa sanar wa wani kika barta a ranki.”
“Babu komai Gaji, yanayi na ne a haka amma ni babu abinda yake damuna.”
“Kin tabbata.”
Daga mata kai tayi tana jin kamar ta saki kuka, ga dama ta samu amma bata da ikon furta wa, toh tace mene ma wai? Hakan ba shi zai hana Mama ta daina muzguna mata ba, Kai tsaye zata kare kanta da zarar Gajin ta tuhume ta karshe kuma abun ya koma kanta kowa ya cigaba da mata kallon marar kirki ko kuma wadda bata san halacci ba. Shiyasa ta zabi yin shiru kawai dan fadar ba zata sauya komai ba, su duka sun yarda da Maman yarda irin ta ban mamaki.
“Ai nasan bangaren Hajara baki da wata matsala dama, na dai zata ko damuwa ce dai irin ta rashin maman ki kusa dake, duk da bani da haufi akan kulawar da kika samu iyakar abinda zaki samu kenan ko da ita mahaifiyar taki ce.”
“Haka ne.” Tace a kasalance
“Yawwa ki dinga dan daurewa kina shiga cikin yan uwanki kinji? Zaman shirun da kike babu dadi.”
“In sha Allah zan gyara.”
“Yawwa… Haka nake son ji.”
“Ya batun yajin aikin nan kuwa? Kun dauko karatu tiryan tiryan yajin aiki ya tsaidaku da tuni wata maganar ake ba wannan ba.”
“Wallahi shiru ba labari, muna dai ta addu’a Allah ya sa a daidaita.”
“K’asar nan kenan ai, dan karatun ma yanzu nema ake a hana dan talaka yin sa.”
“Wallahi.”
” Allah yayi mana maganin abinda yafi karfin mu.”
” Amin ya Allah!”
” Shiyasa nace duk ku fidda mazaje kawai da zarar wadanchan sun tafi kuma azo ayi naku zaman haka nan ba zai yiwu ba.”
Shiru tayi gabanta ya fadi, bata son taji ana maganar auren su, gashi kuma taga alamar ba za’a dauki lokaci ba za’a ce su fidda mazaje, ya zatayi da ranta? Da ganin suna makaranta yasa maganar ta lafa amma yanzu yajin aikin da aka tafi da ba’a san ranar dawowa ba ya saka iyayen nasu yanke shawarar suma su aurar dasu kawai sai karasa karatun a dakin su.
Tashi tayi tayi ma Gajin sallama ganin lokaci yayi, taje tayi alwala ta saka Hijab dinta ta fito, a falo ta tarar da Mama tayi saurin tsugunnawa ta gaishe ta
” Mama barka da gida.”
” Saura idan an tashi ki tsaya shiririta a hanya ko ki tsaya gidan Gaji karki zo kiyi abinda ya dace, jiya kam kinci darajar babanku yana nan.”
“In sha Allah.” Tace sannan ta mike ta fice Maman ta rakata da harara.
****Sati biyu tsakani aka fara bikin gidan nasu, duk yadda taso gujewa wasu abubuwan amma Maryam bata barta ba, komai idan za’a yi sai ta sakata a ciki, haka kunshi da gyaran kai tare suka je da wata kawar Maryam din.
Alhamis suka fara bikin, a compound din gidan Anty Mabruka sukayi bridal shower iya su da kawayen su, juma’ah akayi kamu asabar aka daura aure hade da yini, lahadi aka kai kowacce gidan ta.
Ranar litinin suka tashi gidan da sauran bakin da basu riga sun tafi ba wanda yawanci dangin Gaji ne, a babban kitchen din gidan suka hadu aka hada breakfast Masa da miyar taushe, har rana tayi sosai basu kammala ba hakan ya sake haifar mata da wata irin gajiya bayan wadda take fama da ita, tasan halin Mama sarai idan ta makale taki fitowa ayi aikin da ita duk da akwai masu yi din amma dolen ta ne ta fito, duk da hakan ba karamin taimaka mata yayi ba wajen gogewa da kalolin girke-girke mabanbanta. Sannan uwa uba girkin mutane da yawa wanda ba kowa bane ya iya.
Da saurin ta, ta karasa dakin su, ta kwanta a gefen gadon saboda wani irin sanyi da take ji alamun zazzabi ne ke neman rafke ta, rawar sanyi ta fara hakoranta suka shiga haduwa waje daya, ta saka hannu da k’yar ta jawo bargon Zeenat din ta lulluba.