HALIN GIRMA 23

Birkitota yayi da karfi muryar sa na fita da dan karfi akan dazu yace
“Tell me, me ya faru? Wani abu ya faru? Kin samu wata ko wani da kika zo? Wani ya fad’a miki wani abu ne? Me ya faru!”
Kuka ta samu kanta da fashewa da, ya tashi da sauri yana kunna wutar dakin, ya dawo ya tashe ta zaune suna fuskantar juna, zuwa lokacin ya ji yana neman loosing temper dinshi.
“Kalle ni, look at me! Menene? Me ya faru da ban sanshi ba? Tell me, waye yazo?
” Maimartaba ne yazo.”
” Maimartaba!?” Ya furta da dan karfi cikin yanayin dake nuna tsantsar mamakin sa
“Me yazo yi a part dina? Me yace? Me ya faru? Wani abu ne ya faru while i’m sleeping?”
” Eh.” Ta daga masa kai, tsugunawa yayi a wajen yana tattaro dukkan nutsuwar sa, gabansa na faduwa da abinda zata ce dan yasan ba karamin abu bane zai kawo Bubu part din sa.
” Believe me, bansan komai ba, kamar yadda babu alkalami akan me bacci, na rantse miki bansan me ya faru ba.”
Goge fuskar ta, tayi da hancin ta a jikin sa, ta dago tana kallon kasa tace
” Naga wata Laila a nan.”
Ta nuna wajen da Lailan ta zauna
” Lailah!? ”
“Eh.”
“Ehen, sai me?”
“Tana zaune a wajen tana kuka sosai, daga nan sai Maimartaba ya shigo, sannan ya tafi sai kuma wata mata ta shigo ta daga ta suka fita
Abu ya hadiye me karfi, ya yi kokarin ganin be yi wani abu ba, a hankali yaji kamar ana masa rad’a
_Be calm Moh, be calm.”_
Kamar wanda aka saka abu aka bubbuge ma guiwa haka ya zube a wajen, zai tolerating komai amma banda fushin Bubu, shi za’a wa wannan kazafin? Abinda be taba tunani ko shaawar aikatawa ba, Zina? Shi Muhammad shi aka yiwa wannan sharrin? Saboda yayi kamar be san wani abu yana faruwa ba, shine har aka samu damar yi masa wannan kullin?
Tana ankare da yadda ya shiga kaduwa, tana kuma ganin yadda Adam apple dinsa ke hawa da sauka tsakanin makogwaron sa, idon sa kadai zaka kalla ka tabbatar da ransa yayi masifar baci.
Sai da yayi kusan minti goma be ce komai ba, ba dan bashi da abinda zai ce din ba, sai dan yadda mamakin Iman din ya hanashi komai, be zaci haka daga gareta ba, idan wata ce, ba zata iya daukar abinda ta gani ba, har ta tsaya jiran shi, ya ga kokarin ta sosai kuma ya jinjina mata, hakan ya kara mata matsayi a zuciyar sa.
Girgiza mata kai yayi yana kama hannun ta
“Kin yarda dani?”
” I don’t know.” Tace tsakanin ta da Allah
“Bansan yadda zan dauki abun na ajiye ba, all I know shine I’m hurt, more than yadda nayi tunanin I ll be.”
Folding hannun nata yayi a cikin nasa ya damke.
“I promise to make everything right, koma menene we will over come it, in sha Allah, together we will build tomorrow, I promise you that!”
Shiru sukayi babu wanda ya sake magana, ko be ce ba, ko be ba ita zata gano komai, zata gane kafin ma ya gane, tana da kaifin tunani, sannan tana karantar komai kafin tayi judging din mutum.
Kwanciya tayi ganin suna zaune kowa da abinda yake tunani, ganin ta kwanta sai ya mike ya fita, ya nufi part din Ammi duk da lokacin garin ke karasa yin haske. Ya san tana zaune har lokacin tana azkar kamar yadda ta saba a ko da yaushe.
Yadda ta ganshi ya shigo jikin ta, ya bata babu lafiya, katse abinda take tayi ta mike tana kallon sa har ya karaso
“Lafiya Babana?”
“Ina kwana Ammi?” Ya duk’a k’asa ya gaishe ta, kafin ya amsa mata tambayar ta
“Ba lafiya ba Ammi, yarinyar nan Laila tayi abinda zan nuna mata ko ni waye, ganin kamar ban san me take ba ya bata damar aikata abinda ta aikata wanda zai zame mata dana sani, dama chan Ammi kece kike hanani, saboda zumunci amma not anymore.”
“Me ya faru?!”
“Bubu be sanar dake komai ba?”
“Be ba, me ya faru?”
Iyakar abinda ya sani ya sanar da ita, jikinta yayi sanyi, ta kuma san Bubu zai iya daukar kowanne mataki akan muhammad din, tun da be taba sanin wani abu daya danganci Laila din ba da shi, ita kawai da Muhamamd din ne suka sani sai Kilishi.
“Babu abinda zai faru, kai dai ka rike gaskiya, zatayi halin ta.”
“Shikenan, zanje naga Bubu, zanji me zaice.”
“Allah ya taimaka, zanyi magana dashi nima in sha Allah.”
Fita yayi ita kuma ta zauna a wajen tana hango abinda zai je ya dawo.
Kasancewar safiya ce, shiyasa ya shige kai tsaye wajen Bubun, a lokacin ya fito wajen shashen bayan sallah yana duba wasu littattafan sa. Sai dai yau ya kasa yin komai, tunda aka fito masa da littafan ya kasa taba ko guda daya, balle har ya karanta, abinda ya gani jiya yayi masifar girgiza shi, ya kada shi sosai, har yayi furucin da yake jin idan har Muhammad be wanke kansa a tsawon kwanaki biyar ba, ko da yana da gaskiya ya zama dole ya auri Lailah tun kafin maganar ta fito waje, a jita a ko ina.
Aji ya samu da maganar a lokacin dan ji yayi yana neman faduwa k’asa, sai dai yadda yayi tunanin maganar zata taba Aji sai yaga akasin haka, yana zaune kem fuskar sa bata chanja ba ko kad’an, har sai da Bubun ya kasa daurewa ya tambayi Aji dalilin da be ji abun ba, murmushi yayi yace.
“Ahmadu kenan, da Muhammad da Laila su dukkan su nawa ne, ni na haifi iyayensu na kuma san kowa a cikin su, na san abinda kowa zai aikata da wanda ba zai aikata ba, duk da yanzu ance baa shaidar mutum, amma ni zan shaidi Muhamamd ko aina ne, lallai akwai wani al’amari bayan abinda kai din ka gani.”
“Amma kuma komai ya nuna, a yadda na ganshi naga Lailan, bani da hujjar kare shi ko yarda dashi, idan har nayi haka sai naga kamar banyi wa Yaya adalci ba, mutane zasu ce ko dan babu shi. ”
” Duk abinda zakayi karka tuna mutane dan dama su baa raba su da abin fad’a, kayi gaskiya kawai. ”
” Toh ta yaya zan yarda da Muhamamd be aikata ba? Da wacce hujja zan yarda dashi? ”
” Ka bashi lokaci, ya kare kansa, idan har ya amsa laifin sa shikenan, idan kuma ya kawo hujja gamsasshiya toh.”
” Idan har muhammad ya kasa kawo hujjar bai aikata abinda ni da mahaifiyar Laila muke tunanin ya aikata ba, nayi alkawarin aura masa ita a tsakanin kwanaki hudu! ”
Dawowa yayi daga tunanin yadda suka kwashe da Aji yayi, ya bata rai sosai sanda Moh ya dire a gabansa, cikin girmamawa ya gaishe shi, amma sai yaki amsawa, ya kausasa murya yace
” Ban kiraka nan dan ka gaishe ni na amsa ba, ban kuma kiraka nan dan muyi doguwar magana ba, me ya faru tsakanin ka da Lailah? ”
” Babu komai Bubu. ” Yace kai tsaye dan dama ya riga ya shiryawa tambayar
” Babu komai? ”
” Eh babu, duk abinda ka gani sharri ne, bansan komai akai ba. ”
” Waye shaidar ka? ”
” ALLAH! ”
Ya fad’a kai tsaye, shiru Bubu yayi, ya dauki wani lokaci kafin yace
” Ka dauki alaka ta da kai ta d’a da mahaifi ka ajiye a gefe, ka kalle ni a matsayin alkali da aka kawo min kara ka, na baka nan da kwana hudu ka kawo min kwakkwarar hujja, idan har kwana hudu ya wuce babu komai, nayi maka alkawarin aura maka Laila! ”
” Aure?!!! ”
” Aure, tashi ka bani waje.”
Jikin sa a sanyaye ya tashi, ya fice cikin sauri sauri ya nufi part din Lailan, yana tafiya yana huci, ji yake kamar ya dauko bindiga ya harbe ta, mutanen da suka fara fitowa wanda suka kasance masu aikace aikace a tsakanin parts din suka hau mamakin ganin Moh a irin lokacin shi kadai babu wani tare dashi. Be same ta a bangaren nata ba, tana bangaren Kilishi,juyawa yayi zuwa bangaren Kilishi yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai yi musu.