HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 41-45

” That’s my queen, abinda zaki ce kenan kawai, nasan zaki iya, I trust you.”

” Banda fasa kai.”

” Da gaske nake, nasan zaki iya handling kowanne irin situation.”

Murmushi tayi, sai kuma wani tunani ya fado mata, 

” Shikenan sai ka kara aure?” Ta samu kanta da tambayar shi cikin sanyin murya

” Aure kuma?”

” Eh ba sarakuna basa auren mata daya ba, wasu ma har da kwarkwara suke yi.”

” Eh toh…” Ya mike yana saka links a jikin rigar, 

” Me?”

” Ban dai san nawa zan ba ni ma, amma nasan zan kara uku na cike kinga hudu kenan.”

Gabanta ne yayi mummunar faduwa, ta dinga kokarin karanta gaskiyar sa ta hanyar kallon fuskar sa. He looks serious, sai taji wani kuka na taso mata, tayi kokarin dannewa tana kokarin barin dakin gaba daya, riko ta yayi da sauri ya dawo da ita yana dariya

“Kishi?”

“Zanje k’asa na dauko abu ne.” Tace tana avoiding kallon fuskar sa dan ji take kamar ta fashe da kuka

“I love this new side of you Baby, yayi miki kyau.”

Haushi ne ya sake turnuke ta, wato shi wasa ma ya mayar da abun, fusge jikinta tayi, tayi gaba da sauri ta bar masa dakin, tana fita hawayen da take da rikewa suka zubo, shikenan ace a karaamin shekarun ta zata fara zama da kishiyoyi ba ma kishiya ba, har ga Allah bata da hayaniya da fitinar da zata iya zama dasu, ga hayaniyar gidan sarauta da shegen makirci wanda take tsoro tun farkon fari da ta gano waye ta aura. Tsaye take jikin staircase bata sauka ba, ya fito ya tadda ta a wajen, sai ta waske tana kokarin sauka ya chapko ta.

“Babu in da zaki sai mun karasa maganar mu.”

“Ni fa babu komai, abu zan dauko a k’asa.”

“Ba in da zaki.” Ya juya da ita zuwa ciki, ya zauna ya dora ta a saman cinyarsa.

“Ashe dai ana kishi na haka.”

“Nifa ba kishi nake ba, tambaya kawai nayi kuma ka bani ansa ai.”

“Bari kiji, kinga bamu ne muke da ikon tsarama kanmu rayuwa ba, idan ma ka tsara tsarin Allah daban ne. Bani da sha’awar kara aure amma bansan me gobe zata haifar ba, karki damu let’s pray for the best kinji? Muhammad dinki yana sonki sosai, wannan kawai ya isheki ki mikar da kafarki kamar kin hau jirgin sama mai ya kare.”

Duka ta kai masa suka yi dariya a tare, a kalla dai ya fad’a mata iyakar gaskiyarsa, kuma hakan da yayi ba karamin burge ta yayi ba, taji ta kara son shi fiye da baya. Tare suka karasa shiryawa ya taimaka ya saka mata Alkyabba akan kayan ta, ya gyara mata sosai tayi kyau, ya ciro waya ya yi musu hoto me kyau, sannan suka fito, suka tarar da su Ummimi da sauran yan matan uku sun shirya tsaf suna jiran su, waje kuma fadawa ne suma a shirye an gyara motar. Hannun su sarke da juna suka sakko, duk suka zube suna kwasar gaisuwa, kafin su karasa an bud’e musu motar sai da ya bari ta fara shiga ta zauna sannan shima ya shiga. Sauran motocin su Ummimi suka shiga sai fada.

   Sanda suka isa Takawa be riga ya fito zaman fada ba, sai suka wuce kai tsaye wajen sa, suka sameshi a wajen karatun sa tare da Fulani,a kunyace Iman ta gaishe su amma sai taga kamar basu damu ba, sun sake sosai kamar ba sarki ba, suka dan tsokani juna da muhammad kafin su barsu ita da Fulani zuwa bangaren ta, ba chan waje suka koma ba, wani corridor suka bi har chan din, tasha kallon haduwar wajen a hanyar su ta zuwa har suka dangana da chan sashen.

    Har yamma likis suna gidan, bata sake ganin muhammad ba sai da yazo zasu tafi, ya shigo kamar bashi ba, hatta da takun sa sai data ga ya chanja ya zama irin na saraki masu ji da jini a jika, za’a ga hadadden young Sarki, ga kyau ga aji. 

   Sai da ya zauna fadawan suka fita sannan ya dube ta ya kashe mata ido ba tare da Fulani ta gani ba, murmushi tayi kawai ta saukar da kanta dan Fulani ta fad’a mata yadda tsarin sarautar yake, dole tayi takatsantsan da abubuwa masu yawan gaske, ta kuma ce nan zata dinga zuwa kullum tana ganin yadda abubuwan suke kafin tafiyar su.

   Haka kuwa akayi, kullum sai sun fito da safe sai dare suke komawa kuma bata sake ganin shi wani lokacin ma sai dai su hadu a mota idan zasu tafi.

    

***Maganar Abba da Maman Iman ta 

Rayuwa ta cigaba da garaw

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button