HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 7

“Maraba da Yarima!”

“Sarkin dogarai…”

Muryar sa ta saka takawa d’agowa, ya gyara daga gishingid’ar da yayi, ya fad’ad’a fara’ar fuskar sa da tayi ma Moh iso har gaban kakan nasa. Russunawa yayi cikin girmamawa ya kai gaisuwa, hannu ya mik’a masa ya matso kusa dashi sosai, ya shafi saman kansa

” Sai yau kaga damar leko ni ko Muhammadu?”

” Tuba nake Takawa, ayyukan ne suka yi min yawa.”

” Toh madallah, naji kace kana son gani na, toh gani ya akayi?”

” Dama magana ce akan abinda Bubu yayi maka magana.”

” Auren ka? Jairi toh sai akayi yaya?”

Dariya ya saka sosai

” Toh kunce sai nayi aure yanzu kuma nazo da maganar kuma, sai na fasa auren ma gaba daya.”

” Fasa mana, waya yayi asara? Kaji dan nema.”

Dariya suka saka a tare, kafin Takawa yace

” Toh sai ka fadi a inda yarinyar take ko? Idan yaso sai a nemi iyayenta.”

” A ah ni dai Takawa, ayi min aikin gafara a bari a samu wasu suje su nema min auren ta.”

” Wasu?” Yace yana kallon sa

” Eh a dangi haka ba, ba manya sosai ba, Ina nufin ba cikin manyan masarauta ba, yan chan kasa kasan dai.”

” A wanne dalili?”

” Kawai ni bana so suji tsoro su ga kamar mun fi karfin su.”

Girgiza kai Takawa yayi

” A neman aure babu boye boye Muhammadu, a sak dinka zaka je, kai ne fa jika na farko a gidan nan, sannan a wajen mahaifin ka, wanne irin tunani ne haka ya shiga kanka?”

Sosa kai Moh yayi yana marairaice fuska

“Ni dai dan Allah takawa, a bar wasu suje.”

“Sam sam kaima kasan hakan ba mai yiwuwa bane, dole ne su san kai din daga gidan da ka fito.”

Shiru yayi yana jin kamar ya daure kansa da ya budewa Takawa zuciyar sa, yasan shi sarai da tsayawa akan ra’ayin farko, amma yayi tunani zai fuskance shi duba da irin son da yake masa, dama Musaddik ya gaya masa, babu me yarda da shirmen sa kamar yadda yake jaddada masa a kullum, babu me biye masa ko bashi goyon baya. Tun daga lokacin yasan sarai babu me tsayawa ya saurare shi, balle ya yarda da tsarin sa. Ammin sa ce kadai itama bata ja da maganar Takawa, ballantana Bubu da baya iya aiwatar da komai sai abinda Takawa din yace.

   

“Kana jina Muhammadu, maganar da kazo da ita bata kamawa bace. A tsari na gidan nan ma zamu iya aika musu suzo nan din domin muna da damar bada diyar tasu, sai dai ba zamuyi haka ba, zamu basu girman su da darajar su in Sha Allah, za kuma musu duk abinda Muhammad yake so amma banda shiririta.”

Ya karashe yana murmushi, murnushin shima yayi kawai ba tare da yace komai ba. Suka cigaba da hira irin wadda suka saba har be san iya adadin awoyin da ya bata ba, sai da suka ci abinci da Takawar sannan ya lallaba ya shiga gidan ya gaida matan gidan ya kare a dakin kakarsa ya tarar da yan matan family din sunzo suna da wani get-together da suka shirya sannan suyi maganar tsari bikin Abidah guda daga cikin jikokin gidan. 

   A kaidar sa baya sakar musu fuska ko kad’an domin suna da rainin hankali sosai, duk da shi basa yi masa neman ma ya kula su suke amma shi sam baya tsayawa shirmen su, da gaske suka shakkar shiga shirgin sa hakan yasa yana shigowa shashen suka dinga yayewa da d’aya d’aya.

  Dan tsiririn tsaki yaja sanda suka gama ficewa ya zauna yana muzurai a dole baya son raini shi. Mutane da yawa na fad’a masa yadda yake abubuwan sa kadai ya tabbatar da shi din jini ne na sarauta amma shi sam be san ma yana yi ba ma. 

   Ya dan jima a wajen nata kafin ya tafi yana jin zai dan dade kafin ya sake waiwayo su duba da tafiyar dake gaban sa akan aikin sa.

***Yana zaune a gate din gidan yana dakon shigowar Abba Babban, a kan idon sa ya dawo ya tashi da sauri ya tare shi ya bud’e masa kofar mota.

“Sannu da zuwa Abba.”

“Yawwa Ibrahim, kaine yau a gate din kenan.”

” Wallahi kuwa Abba, sannu da dawowa, ya aiki?”

” Alhamdulillah mun gode Allah, ya naka aikin?”

” Alhamdulillah.” Yace yana tuna abinda ya faru dashi.

” Allah ya taimaka ya bada sa’a.”

” Amin Abba.” Yace yana bin sa rik’e da jakar sa a baya. 

” Mika jakar ciki bari na fara gano Gaji.”

Yace yana bin hanyar da zata kaishi bangaren Gajin, da sauri Khalil din ya kai masa jakar ya dawo ya zauna yana jiran ya fito. Ya dan jima a wajen Gajin kafin ya fito sai dai ganin Khalil ya saka shi mamaki, abunka da Babba nan da nan ya gane akwai wani abu.

” Ya akayi Khalil? Kana son gani na ne?”

” Eh Abba.” Yace yana sosa kansa 

” Haba ko da naji, toh zan turo a kiraka kaji?”

” Toh Abba Nagode.” Girgiza kai Abban yayi ya wuce bangaren sa. Maimakon ya koma gida sai yayi zaman sa anan yana jiran kiran Abban. Yana zaune kuwa yaga fitowar Sadik ya tashi da sauri ya tare shi 

“Yawwa wai kazo in ji Abba.”

Rik’e hannun sa yayi suka koma yana jin wani iri a ransa, bakin sa dauke da addu’a ya shiga falon ya tarar Abban ya chanja kaya yana zaune da alama abinci ya gama ci. A chan gefe ya zauna yana jin kunya.

“Yawwa ina jin ka Ibrahim, ya akayi?”

Shiru yayi yana tsara yadda ya kamata ya ce, sai da ya dau sakanni yana hado maganar kafin yace

“Dama Abba akan maganar Fatima ne.”

“Uhum ina jinka. Ya akayi?”

“Dama… Dama so nake dama a bani dama kamar yadda tsarin gidan nan yake.”

Murmushi Abba yayi cikin jin dadi yace

“Masha ALLAH naji dadin wannan abu matuka, Allah ya tabbatar mana da alkhairi kaji? Allah yayi muku albarka.”

” Amin Abba.” Yace a ciki-ciki farin ciki na kamashi, 

” Kaje ku daidaita idan Allah yayi mu haka muke so, an riga an zama daya ai in sha Allah babu wata matsala.”

” Nagode Sosai Abba, Allah ya kara girma.”

” Amin.” Yace yana chanja tasha a tv, shiru Khalil din yayi kafin ya mike

” A huta lafiya Abba.”

” Yawwa Ibrahim.”

Yana fita ya daka tsalle a wajen yace

“Yes!!”

Da sauri ya bar wajen yana jin kamar ya same ta ya gama ne, zai nuna wa fakirin saurayin ta cewa dan gida yafi bare.

***Sabon yadi ne me saukin kudi sosai, dinkin ma irin dan 1500 din nan ne, a rayuwar sa be taba hasashen saka ire-iren kayan da yake sakawa a yanzu ba, wani kallo Musaddik yake masa yana jin kamar ya kamashi yayi ta bugu.

“Yanzu Moh irin kayan da zaka saka kenan zaka ganin sirikin ka?”

“Wait and see.” Yace yana kawo wata leda a kusa dashi, ya wurga masa yana cigaba da kallon kansa a mudubi

“Ka chanja mu tafi idan yaso muyi sallar magriba a hanya sai mu karasa.”

“Na saka me?” Musaddik yace da sauri yana bud’e ledar.

“Wait what! Kana nufin ni zan saka wannan kayan.”

“Mu nawa ne a dakin nan?”

“You must be kidding me, haba haba an fad’a ma kowa ma irin ka ne.”

“Allah su zaka saka mu tafi, kayi sauri karka batan lokaci I’m dying to see my love.”

“Aiko sai dai ka tafi kai kadai wannan karyar ba dani ba.”

“Da wa toh? Wa nake dashi bayan kai? Kasan da ace ban samu kanta ba dole kaima ka tattaro ka dawo sabon shagon nan dana zauna mu zauna tare. Allah dai ya taimake ka wallahi.”

” Ai wallahi babu yarinyar da ta isa nayi mata irin wannan son, the whole you, Captain Muhammad Ahmad Santuraki, dan ga sarki jikin sarki sannan kuma babban soja, ko da yake fa dama ance ku sojoji baku iya soyayya ba, musamman idan allurar ku ta motsa.”

Daina abinda yake yayi ya matso kusa dashi

” Idan bansa an saka min kai frog jump ba, kace ba suna na Muhammad ba.”

Dariya maganar ta bawa Musaddik,

” Ni zaka saka frog jump?”

” Sosai, ka cigaba da batan lokaci kaga.”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button