HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 9

***Zama Mama tayi tana sababi akan tafiyar Khalil din babu sanarwa, sai dai a k’asan zuciyar ta taji dadin hakan domin a kalla hankalin sa zai dauke daga kan Iman din har a gama magana da shi dayan da yazo. Abba ne ya shigo ya sameta tana zaune , ya zauna a gefenta sai tasha jinin jikin ta musamman da ta gama sanin halin sa tsaf.

“Me yasa kika ce min Ibrahim ba da gaske yake akan maganar Ummi ba, sannan shi kuma yaje ya samu Yaya da maganar.”

Yadda ta zabura yaso bawa Abban mamaki.

“Khalil din ne yaje wajen Yaya? Yaushe akayi haka? Me yayan yace masa?”

“Duk ba wannan na tambaye ki ba, baki bani amsa ta ba.”

“Toh toh ai gani nayi shi Khalil ba yanzu zai yi aure ba, su kuma yaran nan yanzu ne muke so mu aurar dasu, bana so Zeenat ta tafi da bar Iman tunda kaga tare suke komai, shiyasa nace gwara wanda ya shirya.”

“Haka ne kuma.” Yace yana mata wani irin kallo da ya sakata tunani sosai 

“Toh hakan yayi ai, Ina fatan dai zeenatu ta sallami yaron nan Bashir ko? Dan ina nan akan bakana ba zan bashi ba.”

“Dan Allah Dr ka bar wannan maganar, tunda tana son shi kayi hakuri kawai ayi tunda an wuce zamanin da za’a yi wa yara auren dole.”

Girgiza mata kai yayi yana dakatar da ita

“Wannan maganar taki shirme ce, musulunci mu ya bawa damar zaba wa yayanmu mazaje na gari, dan haka ban yarda da Bashir ba, idan akwai wani ta kawo shi.”

Ya tashi ya fice ransa na baci da yadda maganar Bashir din taki karewa, sam Hajara bata shirya gane abunda yake hango musu ba, eh hango musu tunda duk in da aka je aka jawo ita uwa sai tafi cutuwa da abinda zai samu yarta.

***Text message biyu ya tura a lokaci daya, address din sa da Abba yace ya tura masa ta message sai kuma message din da yayi wa Abban Iman din, wanda yake ganin shine kadai hanyar da zai bi wajen hana Maman sanin duk wani abu akan Iman din, ya tabbata daga lokacin Abban zai saka ido sosai, ba kuma za’a dau lokaci ba zai gano komai, shi kuma sai yayi amfani da wannan damar ya nemi alfarmar barin komai ya zama sirri a tsakanin su iyaye maza, domin dama su iyaye maza baa sansu da ratatin zance ba, ba kasafai ma suke zama suyi ta magana anyhow ba, ya tabbata idan har hakan ta yiwu toh zai samu abinda yake so, zai kuma tabbatar da Fatiman sa ta samu gatan da bata taba tunani ko hasashen samun sa ba.

***Tunani Abba ya fad’a ganin address din da Muhammad ya turo masa a matsayin in da yake,Emir Palace Kano, Emir Palace Adamawa-Yola, me hakan ke nufi? Kiran Abban su Fatiman yayi yazo ya same shi a part din sa, ya nuna masa message din sannan ya kira sauran yan uwan su Abba Musa suka hau tattaunawa akan abinda ya kamata su yi. Dama chan Abba Musan yana siyasa sosai, sai sukayi shawara akan shi ne zai wuce gaba wajen binciken waye Muhammad din a cikin kwana uku kachal. Haka kuwa akayi, washegari ya same su da maganar da ta yi matukar basu mamaki. A yadda suka sani idan wani daga cikin irin wannan yaga yarinya yana so, kawai aikawa ake iyayenta suzo ayi magana a fadar sarkin, a matsayin shi sarki dama uban kowa ne, sai suga ga banbanci inda Muhammad din yazo kai tsaye ba tare da ya nuna shi din waye ba, ba kuma tare da ya nuna karfin iko na mulki ba, hanyar da ta dace da kowa yake bi wajen neman aure shima ita yabi.

  A cikin su babu wanda be yi amanna da maganar ba, musamman binciken da Abba Musan yayi da irin yabon da Muhammad din ya samu daga wajen mutane da dama musamman mazauna masarautar.

    Shiru Abba yayi bayan kowa ya gama tofa albarkacin bakin sa, aka bashi dama a matsayin sa na mahaifin Iman din, 

“Bakwa ganin idan iyayen yaron nan suka san in da yazo neman aure zasu kyale shi, duba da mu din ba wasu bane akan irin girma da nasabar gidan da ya fito.”

“Idan har a yadda bincike na ya nuna min ne, iyayen sa basu da matsala masu son talakawan su ne, dan haka muyi addua kawai in sha Allah alkhairi ne.”

“Shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi,.”

“Yanzu kayi magana, Amin ya Allah.”

” Ina neman alfarma daya, da mu bar maganar nan a tsakanin mu zuwa muga abinda Allah yayi.”

” Hakan yayi, Allah ya shige mana gaba.” 

Suka hada baki a tare, sai kuma suka shiga wata hirar tunda daman su dan dade basu yi irin wannan zaman ba, anan duk suka ci abinci a tare sannan kowa ya tafi zuwa sabgar sa. Aka bar Yaya a zuwan zai kira Muhammad din da daddare ya sanar dashi ya bashi izinin yazo yaga Fatiman su daidaita, da daddaren bayan ya gama komai ya turawa Muhammad din text message akan ya cigaba da zuwa. Muhammad na zaune shi da Musaddik suna kallon video da ya saka akayi wa Khalil suna kwasar dariya text din ya shigo, tashi yayi ya daka tsalle kafin yace

“Yess!!!

” Ya akayi?”

” Karfe nawa yanzu?”

Yace yana kallon agogon falon

” Opss Ashe dare ya fara, ba dan ba dan ba da yanzu zanje na ganta, amma ba komai kafin na wuce Abuja zan tsaya na fara ganin ta.”

” Me faru wai.”

” Karanta!” Ya mik’a masa wayar

” Ah congratulations angon fatiti, Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”

Rik’e k’ugu yayi yana hararar sa

” Allah ka sake bata mana suna sai na saka frog jump, kaji ma na ratse.”

” Kut! Allah fa ka raina ni Moh, komai sai kace zaka sani frog jump an fad’a ma nima kamar wadanchan dogs din naka ne na bakin gate.”

” Ka dai kula, kana magana ne da Captain Muhammad Ahmad Santuraki, Captain Moh!”

” Whatever, ni dai muhammadu na sani, ba wani bragging da zaka min.”

” Zaka gane ne idan na dauke ka na je na jefa wa mayunwatan zakunan nan na barack, ba zaka sake kiran sunana gatsal ba.”

” An gaya ma kowa irin khalil ne? Lusari!”

Dariya suka saka Muhammad ya shiga gwada yadda Khalil din yake, suka sake tuntsurewa da dariya suka tafa

” Ashe farar kura ce a wajen, sai uban cika baki dan iskan yaro, gobe ma ya sake, naso ka dan saka su sun sassama masa jiki wallahi,.”

” A hakan ma nasan sai sunci zalinsa ai.”

” Wicked soul!” Yace yana dariya

” Naji, bari naje na kira Baby na, naji voice dinta me dadi kafin gobe naje na ganta, dan yanzu ina da license, na matsu na ganmu tare, muna yawo a garin nan cikin mota my hands in to her’s, ga cool music na tashi Malam, wow love in the air.”

” Toh Mr Romeo, Allah ya kaimu dai zamuyi kallo, yadda kake son ta Allah yasa tana maka ko rabin sa ne.”

” I don’t care, as long as munyi aure, zan koya mata yadda zata so ni.”

” We shall see.”

***Ruwan zafi ne a katon bawo, Khalil na zaune a gaban ruwan hajiyar su na danna masa bayansa, gaba daya jikin sa ciwo yake kafarsa kamar zata cire yake ji, babu irin tambayar da batayi masa akan me ya same shi ba amma yaki fad’a mata, haka Mama ta bugu tana fad’an tafiyar Khalil din hajiyar ta fad’a mata a yadda ya dawo, kuma yaki cewa komai. Yana jin su har suka gama ya tashi ya koma dakin sa ya kwanta yana tariyo abinda ya faru cikin tausayin kansa. Shi ya jawo yana takama da shegen bakin sa ya je ya kaishi ya baro, dama an fad’a mutum ya kiyayi harshen sa, akwai hadisi guda da akayi magana akan harshe da kiyayar sa, yaga izina a kansa, gashi bashi da damar fadawa wani abinda ya faru domin yasan shi za’a yi wa dariya, ko da muhammadu a iya soja ya tsaya matsayin da yake kai ya isa ya taka shi son ransa ba kuma wanda ya isa yace dan me? Balle ganowar da yayi waye Muhammad din, anan ya gane bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane, shi din ma ganganci ne da kuruciya. Eh toh kuruciya mana tunda dai yasan a girme Muhammad din zai girma shi dole ya fishi hankali da komai. Abu daya ne zai hana shi walwala, yadda zai yi da tarin soyayyar ta, gashi yayi masa kashedin ko a hanya babu shi babu ita, ya kuma tabbatar idan har ya kuskura yayi wani abu, za’a iya neman shi ma baki daya a rasa, dan masu kudin nan yasan ba wani abu bane a wajen su su batar da mutum bat, har abada a daina jin labarin sa.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button