NOVELSUncategorized

HUSNA KO HUZNA 2

 2


Wayyo Babana nashiga ukku na lalace wayyo hannuna ,ihu takeyi ba k’ak’k’autawa kamar zata tsaga Gidan , 
Wanda hakan ya kara haifarwa da mama k’ullewar Mara ,ji take kamar mararta zata fashe wannan yasa ta rintse idonta da sauri tana mayar da numfashi sama-sama , 


Ganin haka yasa Abba matsowa wajanta da sauri yana mata sannu, dak’yar ta bude bakinta cikin galabaita  tace Malam Mara ta zata fashe,  Subuhanallahi Hafsee tashe muje asibiti k’ila haihuwa ce , 

Jin hakan yasa Husna fitowa daga d’akin ,tsul sai gata a gabansu cikin tsananin farinciki tace dagaske mama Haihuwa zakiyi ? Yawwa kinga dama na gayamaki ni zakiyiwa Kane ba Huzna ba ,tayi maganar tana wani yamutsa fuska yayinda take ambatar suna Huzna, 

Cikin tsananin ciyo mama ta d’ago ta dubeta cikin tsananin takaici tace ke tashi daga nan tun ba make ki ba, tunzuro bakinta tayi gaba zatayi magana Abba ya tareda da cewa 
         “Karki damu ‘yar Baba wannan ai ke za’ayiwa Kane daman ,yanzu dai abunda nakeso kinga ki sakarma wannan yarinyar Hannunta kinji ko yr Baba , yayi maganar yana kallon wannan budurwar da har yanzu take faman shar’bar kuka duk ta hada yawu da majina, 

Shagwa’be fuska tayi cikin siririyar muryar ta  tace Abba bafa ni bace Allah Huzna ce , 
         Naji ai nasan bake bace taimakawa zakiyi kinji ‘yar albarka 
Turo baki tayi zata k’ara magana ya rigata da cewa ” in fa bata tafi ba Mamanku bazata haihu da wuri ba gara ta tafi kawai kisamu kanen ki yazo da wuri ,

D’an jimm tayi kamun ta juya a fusace tana zuwa kallon hannun kawai tayi sai gashi yarinyar tafara motsa hannun , aikuwa tana ganin hakan ta kwasa aguje tabar Gidan ko Takalmi bata dauka ba , k’wafa kawai tayi bayan tagama bin bayanta da kallo tace zamu had’u ne wallahi bangama dake ba ta wani juya dara-daran idanunta kamun ta dawo kusa da mahaifiyarta dake kwance tana murk’ususu , 

Cikin damuwa tace Sannu Mama , 
Wannan shine banbancinta da ‘yar uwarta tanada tausayi sosai sa’banin Huzna ,

Hafsee ko mutafi asibiti ne ? 
“Aa malam bafa haihuwa bace ko ka manta cikin watanshi takwas yanzu ,kawai dai ciyone irin na masu ciki dakuma hayaniya sam banason hayaniya wallahi ,gashi Allah ya jad’ani da jarababbun yara, ……
        Kul… Karna k’arajin kin kirasu da wannan sunan , kuma ki daina sa damuwarsu a ranki , bakomai ke damunsu ba sai k’urciya in sunyi hankali ai bazasuyi ba , sannan waye bai San k’ofi ba ga ‘yan biyu  mutanen garin nan ne kawai da girmama Abu sai kace akansu aka fara , yayi maganar cike da jin haushi ,

Aa fa malam kaima kasan abun nasu yayi yawa ,nikam ban ta’ba ganin irin wannan tashin hankalinba gaskiya , to kedai kawai ki rinka yimasu addu’a Allah ya yaye masu , shine kawai ,
” to shikenan Malam Allah ya yayesu “amin,

Sunanan a haka sukaji an. Banko kofar Gidan an shigo , Huzna ce ko kallon inda suke batayi ba tayi shigewarta d’aki , girgiza kai kawai Abba yayi tare da furta Allah ya kyauta,


*****


Aguje tashiga Gidan Zane a hannu duk ta firgice , ” ke lafiya mi ya sameki kika shigo haka kamar wadda tayi gamo, cewar inna talatu  ,
Kasa magana tayi sai zama da tayi a k’asa tana mayar da numfashi , 

Oh yau munga ikon Allah wai miyake faruwa daku ne dazu ‘yan uwanki sun shigo aguje kema gashi yanzu kin shigo a firgice sai kace wadan da sukayi gamo ,

Dak’yar ta bude bakinta tace Inna – Inna aljana, Aljanace wallahi Inna, “Aljanaaaa!!!!! Cewar Inna talatu da k’arfi , aikuwa nan take jikinta yafara rawa tuni ta mik’e tsaye ta kwasa aguje ta nufi hanyar d’aki tana ihun sun shiga ukku Aljana,  batayi aune ba tayi Ball da k’waryar dake ajiye a wajan da masara  a cikinta kasancewar bata jima da gama wankin masarar ba zata kai reda ,amma sam bata ko kula kan masarar ba ta shige d’aki ta Sanya sakata jikin ba inda baya rawa kamar mazari, sai faman salati takeyi lokaci d’aya duk ta had’a zufa , 

wannan hayaniyar ce ta tashi Malam Jafaru daga baccin da yakeyi , fitowa yayi daga d’akinshi yana cewa wai Talatu ihun mi kikeyi ne kamar wata sabun kamu, gaba d’aya ihunki ya tasheni daga bacci , yayi maganar cike da masifa kasancewar shi mutum mai zafi ga masifar tsiya ,
Maganar shi ta katse ne lokacin da yayi arba da masarar da ya kawo dazu da nufin ayi Tuwo , wata uwar ashshar ya lailayo ya makawa wannan budurwar mai suna  zaliha yace ke don uwarki waya zubar da masarar nan ,?  Cikin rawar jiki ta bude baki zatayi magana ,kamar daga sama yaji muryar inna talatu tana cewa 
” malam yi ta kanka Aljana , yau munshiga ukku Aljana a Gidan nan , wata juyawa Malam malam jafaru yayi kamar wanda aka jonawa shocking da niyar guduwa amma mi sai gashi k’asa da’bas kasancewar kafafunshi sun kasa daukarshi hakan yasa Babbar rigarahi ta kifar dashi yayi iya yinshi amma yakasa tashi saboda rawar da lafafunshi ke yi ganin da gaske dai bazai iya tashi ba yasa yafara zunduma ihun naiman taimako , ihu yake yana k’arawa duk da zaliha take cikin firgici batasan sanda fara dariya ba , cikin dariyar take cewa baba Bafa wata bace aljanar sai Husna ta Gidan Malam Hassan kawai inna ce bata tsaya ta gama jin abunda ya faru ba tafara ihu, 

Dukkansu tsit sukayi suna sauraron ‘yar tasu.da Saudi Talatu ta balle d’akin ta fito bata tsaya wata-wata ba ta zari icce tayi kan zaliha ,ganin hakan yasa zaliha arcewa a guje tabar Gidan , juyowar da inna talatu zatayi sai ganin Malam Jafaru tayi ya nufota a fusace kasancewar tafi bashi haushi akan zaliha duk tabi ta rud’ashi akan abunda batada tabbas akai, ganin da gaske idan ta tsaya zai iya dukanta kasancewar dama yasaba indai dukan mace ne wannan ba komai bane a wajan shi , wannan yasa tuni ta zari zanenta dake kan igiya tayi waje bata zame ko ina ba sai Gidan maigari , kasancewar malam Jafaru shine babban d’an mai gari,


****


To malam fa yau ba komai a Gidan nan sai dan wannan garin kuma bashida yawa , 
        “Eh nasani Hafsee akwai kudin da nake biyar wani yanzu idan na fita can zan fara ta wajan shi insha Allah nan bada jimawa ba zan aiko maki da kudin sai asan abunda za’ayi , 
       To shikenan malam sai ka dawo , to Allah yasa ,” idan wadan nan rigimammun sun dawo kifara jik’a masu garin su sha kamun na aiko, “to malam adawo lafiya ,

Yana gaf da fita daga Gidan sai wasu sun shigo aguje kamar an korosu , 

Husna tace yawwa Abba dama sauri mukeyi muzo kabamu Biyar-biyar d’inmu tun baka fita ba ko Huzna ,tayi maganar tana kallon Huzna , gyad’a kai kawai Huzna tayi don indai ba masifa take ji ba to miskila ce ta k’arshe ,

Dafe kai Abban yayi cike da zullumin yadda zasu k’are don yasan wadan nan yaran sam basusan babu ba basa d’aga k’afa ko kadan , gashi shi kuma bashida ko sisi dama saurin da yakeyi kenan don ganin ya fita kamun su dawo,


Cikin lallashi yace ” kunga ‘yan Abba kuyi hak’uri har na dawo yau banida kudi amma anjima zan 
aiko maku kunji kuyimun addu’a in samu kudi da yawa zan siyo maku harda kayan wasa, 

Shiru yayi yana kallonsu don gaba d’aya sun had’a fuska Juyawa Husna tayi batare data ce komai Ba tayi cikin Gidan , Huzna ma juyawa tayi har tafara tafiya sannan ta juyo ta ce wallahi Abba yau ko sisi bazakayi ba , tana kaiwa nan tayi shigewarta cikin Gidan ,

Dafe kai kawai yayi kamar zaiyi kuka don ba yau suka saba yimashi irin hakaba kuma abun mamaki hakan ce take faruwa har wuni ya kare bazaiyi ko sisi ba , hakadai ya juya ya fita don bayason ya koma ya dagawa Hafsee hankali , …………..,…..Mmn yusup ce????????
Kuyi hakuri da wannan 
nasan bai tafi a yadda ya dace ba to jikin ne sai a slow

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button