HUSNA KO HUZNA 3
P3
“Lafiya kuka shigomun haka sai kace an maku mutuwa ? Mama ba Abba ne ya ki bamu biyar ba kuma ni awara nakeso na siya ,cewar Husna tana magana cike da shagwa’ba ,wani dogon tsaki Mama taja don har ga Allah yaran Haushi suke bata saboda muguwar muguntarsu da tsabar rashin jin su kawai dai tana hakuri ne tare da yi masu addu’a Allah ya yaye masu wannan abun , don tasani na
d’an lokaci ne idan sunfara girma doli abun kai karye , tunaninta ya katsene lokacin da taji muryar Husna tana cewa tunda ya hanamu Ai Huzna ta gayamashi ko sisi bazaiyi ba yau,
Da sauri Mama ta d’ago kanta ta kafesu da ido cikin tsananin ‘bacin rai , tsabar haushi ma yasa ta kasa cewa komai ,
Lokaci d’aya duk suka sha jinin jikinsu don duk abunda sukeyi to suna shakkar mama don tanada zafi sosai kuma ita duk abunda sukeyi baya hana ta dakesu son ranta sai dai in tagama sukuma su samu muguntar da sukayi mata, don ansha rik’e mata hannu ko k’afa sai Abbansu ya lalla’basu sannan suke rabuwa da ita,
Yanzu Abban naku kukayiwa haka duk k’ok’arin da yake maku bakwa gani ko ? To shikenan in bai samo kudin ba sai naga uban da zai Baku kud’in ,tayi maganar tare da dungurewa Huzna kai ,
A zuciye Huzna ta tashi tana k’unk’uni tayi hanyar waje tana cewa wallahi ko babu kud’i sai naci awarar nan ,
Kwala mata kira mama ta dinga yi amma ina ko juyowa batayi ba , Ganin haka yasa Husna ma ta mik’e tana cewa bari nima naje in tasamu ta sammin wallahi da gani zatayi dad’i in munci ai sai Abba ya biyata in ta kawo k’ara ko Mama tayi maganar cike da yarinta,
Dafe kai kawai Mama tayi amma tama kasa magana sai addu’a takeyi a cikin zuciyarta don tasan ko ta ce karta je sai taje ko Sama da kasa zasu had’e ,haka tanaji tana gani itama ta fice daga Gidan aguje,
Assalamu Alaikum ,”Wa’alaikussam Malam Musa barka da Safiya ,Barka dai Malam Hassan yagida da yaran ? “To Alhamdulillah ,
Sun d’an ta’ba fira kad’an sannan Abba yayi mashi maganar kudin da yake binshi Wanda sukayi a yau zaizo. Ya kar’ba , duk da yana cike da zullumin abunda zaije yazo saboda yasani sarai Huzna ta wuce inda yake zato abun nata kamar mai aiki da aljanu ,
To wlh malam Hassan sai hak’uri don wallahi ba kudin yanzu a hannuna don Allah kayimun lamuni har zuwa gobe insha Allah zan baka wlh yarona ne muka tashi dashi ba lafiya shine nayi amfani da kudin na siya mashi magani yanzu gaba d’aya naira ashirin ce kawai ta ragemun ,
Shiru Abba yayi cike da rashin jin dadi ,furzo da iska yayi daga bakinshi kamun yace to shikenan Allah yabawa yaron lafiya Allah ya kaimu goben amma in ba damuwa ka bani naira ashirin d’in akwai abunda zanyi da ita don ba ko sisi a hannuna ,
Ah ba komai wallahi bari nabaka , haka ya dauko naira 20 din daga aljihunshi ya bashi ,amsa yayi sannan yamashi sallama ya tafi , ko wajan sana’arshi bai jeba ya juyo gida da nufin kawowa ‘yan biyunshi naira ashirin din don su rabu lafiya , yasani komai zai iya faruwa in bai basu kudin ba don ga alama yafara gani,
Tunda ya shigo kwanar tasu yake tsinkan dandazon yara a wajan Larai mai awara ,bai kawo komai Ba saida yakusa zuwa dai-dai wajan sannan hankalinshi yakai kan su Huzna dake tsaye sai faman huci sukeyi ga hannuwansu duk awara ga wata kuma a bakinsu sunaci wata na zuba saboda yadda suka cika bakinsu da ita yaran dake wajan kuwa sai tafi suke masu hade da kirari
Dafe kai Abba yayi cike da k’unar rai yasani ko ba’a fad’a. Mashi ba suneyadda basuda gaskiya Allah yayi masu shegen fada da tsokanar tsiya,
Kai kai mi yake faruwa ke Huzna mi kukeyi a nan , jin muryar mahaifinsu yasa suka juyo da sauri, ganin kuwa da gaske shine yasa suka kwasa aguje suka nufi gida suna tintsira dariya ,
Kallonshi ya kai ga Larai mai Awara ganinta yayi jage-jage da hawaye da majina tana rik’e da hannunta sai jijjuyashi takeyi , yace lafiya mi yake faruwa , shiru bata bashi amsa ba don gaba d’aya in ranta yayi dubu to ya ‘baci, saboda ba karamun cin mutunci aljanun yaran nan suka mata ba a bainar jama’a da girmanta da komai , kasancewar Larai zata haifesu ma don zawarace harda yaranta biyu saidai basuyi sa’an su Husna ba ,
Akwai k’anwarta da take tayata sayar da Awaran duk Wanda yazo siya ita take zuba mashi , itace tayi caraf tace ” Muna zaman mu sukazo sukace abasu awara ,shine nace su bada kud’i sukace bazasu bayar ba don basuda kudi , shine Anty ta koresu tace su tafi su bata waje , shine fa sukak’i tafiya sukace su sai sunci awara , nan muka k’yalesu mukaci gaba da harkan mu , ganin haka sai suka juya suka tafi , basu jimaba sai gasu sun dawo suna zuwa suka jefama Anty gawan k’adangare ajiki ita kuma dama tsoron kadangare take shine fa batasan sanda ta kwasa aguje ba shinefa zanenta ya fadi daga ita sai fant bata Ankara ba saida takusa fita daga kwanar na rink’a Binta da zanen sukuma suka Tara yara suka rinka kwasar awara sunaci suna shek’a dariya ,da kyar nasamu Anty ta dawo shine koda mukazo duk sun yashe awarar , hakan yasa Anty tayi Kansu zata dakesu sai kuma hannunta ya lak’e yanzu haka anyi-anyi amma takasa motsa hannun shine take kuka,
Dafe kanshi yayi cike da damuwa tare da mamakin wannan surutun na yarinyar sai kace aku tunda tafara magana ba bata tsayaba ,tsaki yayi a cikin ranshi yana tunanin yau kila sai yakusa karya yaran nan don sunfara kaishi bango yara sai kace aljanu duk sunbi sun addabi mutane ,
Hakuri sosai ya bawa larai tareda yimata alkawarin zai biyata Kudin kayanta , sannan yanzu zaije yayi masu magana su sakar mata hannu, kai kawai ta iya daga mashi don tabbas yau yran nan sunci mutuncinta kuma sosai ta tsorata da al’amarinsu bare tace zata yi masu wani abun doli haka zata hakura amma tabbas bazata yafe masu ta barsu da Allah????????
Aguje suka shiga idan kowace baki nashe-nashe da mai ,kallonsu kawai mama tayi ta girgiza kai tana jiran abunda zai biyo baya don tasan tunda ta gansu a guje to biyosu akayi , tasan sun tafka wata ta’asar ne ganin yadda bakinsu yayi nashe-nashe ,
Waje suka samu suka zauna kamar wasu na Allah sai muzurai sukeyi ,don duk hakurin Abbansu wani lokacin jibgar kwarai yake masu in suka kaishi bango,
Ganin shiru baishigo ba yasa Husna tashi tsaye tafara ‘yan raye-rayenta kasancewarta ma’abuciyar rawa haka tace kullum a cikin rawa ko da kid’a ko babu ,
Juyowar da Husna zatayi sai arba tayi da shi ya zuba mata ido yana kallon yadda take wani lank’wasa sai kace macijiya wannan Abu ba k’aramun tsunduma shi yayi a zargi ba Anya yaran nan su kadai suke kuwa?? abubuwan da sukeyi yafi karfin shekarunsu gaskiya , wannan abun ya sanyaya mashi jiki akan yadda ya shigo da zafi da nufin dukansu ,
Malam yanaga ka dawo. Da wuri kuma ,ko har ka amso kudin ne ?
Shiru yayi nadan wani lokaci kamun ya shaida mata duk abunda ya faru Wanda yasa ya dawo har abunda yaran sukama Larai mai Awara,
Hawaye ne suka taru a idonta ,kallonta yayi da kyau yace mi nake gani Hafsee hawaye Hafsee kuma akan yarana !! Wallahi ko kusa karki yarda kiyi wannan gangancin , sam ko alama karki yarda kiyiwa yaran nan hawaye , Gaba Hafsee sai kace bakisan illan zubar hawayen uwaye ga ‘ya’ya ba ,
Kayi hakuri malam ni kaina bansan da zuwansu ba amma zan kiyaye insha Allah zan ci gaba da addu’a har Allah ya yaye masu wannan halin ,
“Yawwa ko kefa addu’a itace kawai zamu yi masu komai mai wucewa ne amma ni tabbas zanyi wani Abu akai don dawuya in yaran nan basuda aljanu abun masu yayi yawa , hakane malam nima ina wannan tunanin to koma dai minene Allah ya yaye masu sukace amin , duk wannan firan da sukeyi ‘yan biyu kyautar Allah suna waje sai tik’ar rawa sukeyi abunsu ba abunda ya damesu????????
******
ABUJA
Akan mi zaka daketa ina ruwanka da duk abunda zatayi ko akan ka take zaune ,to wallahi bazan dauka ba kar Wanda ya kara takurawa ‘yata ehe tayi maganar tana Harar shi ,
Umma wai….
” kaga Jamil zoka wuce narasa wane irin kunnen k’ashine da kai so nawa zance maka duk abunda k’afa Nasma nayi ka sanya mata ido tunda uwarta bataso ana mata magana amma kaki ji, cewar Hajiyar Aliya wadda yaran ke cewa Mamy ,
Insha Allah Mamy daga yau duk abunda zatayi bazan sake kulata ba Ai dai Yaya yakusa dawowa shine zai saitaki Marar kunyar yarinya kawai ,
“Kaine dai Marar kunya kuma ko mu’azzam din yazo bai isa ya takuramata ba ,cewar Hajiyar Na’ima wadda yaran ke kira sa umma Jan hannuna Nasma tayi sukabar wajan tana ta surfa masifa ,
Harara shi Mamy tayi tace to zoka wuce tunda kasamu abunda kake so kafison kullum ka rinka janyomun magana ina zamana ,ai shikenan Mamy daga yau bazan sake kulas ba insha Allah ,
Allah yasa tace kamun ta nufi Sama zuwa bedroom dinta ,yayinda shi kuma Jamil ya juya yabar part din ,
Gidan Alhaji Husaini kenan dan’uwa ga Mahaifin Husna da Huzna ,
Alhaji Husaini shahararren mai kudi ne Dan boko kuma Dan kasuwa yana da Mayan aure ukku , gidane da ake zama irin na kishi kullum a cikin fad’a suke daga iyayen harma da yaran baki d’aya ,
Matarshi ta farko Hajiya Lauratu wadda suke kira da Mamah macece mafadaciya sai dai akan gaskiyar ta take fada kuma bata shiga shirgin da bai shafeta ba ta iya takunta sosai kuma taja girmanta , Bafulatanar Asalice fara tass uwa uba kyau kamar ita tayi kanta tanada Yara Hudu , Na farko Ibrahim (Mu’azzam) ta biyu Fatima wadda yanzu haka taba aure anan cikin garin na Abuja sai yan biyunta mace da namiji Hasan da husaina
Hajiya Ni’ima itace ta biyu macece mai matukar kyashi da hangen na wani ga shiga malamai burinta shine ta mallake kowa a Gidan sai abunda tace kuma tayi nasara don sam Alhaji Husaini baya tsallake maganar ta duk abunda tace ya zauna , saidai abun a iya kanshi ne kawai don takasa mallake kishiyoyinta kamar yadda taso,
Kuma ita ta shiga ta Fita ta rabashi da d’anuwanshi malam Hassan mahaifin su Husna kasancewar taga a duniya ba abunda yake kaina Sama da Dan uwanshi Hassan , gashi itakuma ta tsani kowa ya ra’be mijinta wannan yasa ta shiga ta Fita tasa aka raba tsakaninsu ,shiyasa ba Wanda yake Neman wani acikinsu,
Yarinya
Ukku duk mata , Harira itace babba sai Saudat sai kuma Nasma, dukkansu suna Gidan zaune ba wadda take da niyar fitar da mijin aure dukkansu sha-shanci sukasa a gaba da yawon bin kawaye
Hajiya Aliya kuwa tanada yara hudu Aliyu Jamil da safiyya sai aura Surayya,
Hajiya Aliya mace ce mai matukar son kai daga ita sai ‘ya’yanta sam bata hada ‘ya’yanta da kowa ba shiyasa a kullum Gidan yace cikin fad’ace-fadace Wanda ko Abee kamar yadda suke Kiran Alhaji Husain baya iya tsawatar masu sai fa idan Yayamsu Mu’azzam yana nan wannan kam ko motsi mai k’arfi yaran basu isa suyi ba tsabar yadda suke tsoronshi don sam baya masu da kyau duk Wanda ya fada komarshi to tabbas sai. Ya hadu da hukunci mai tsanani ,sam bayason raini kuma shi ba ruwanshi da kabilanci dukkansu d’aya ya daukesu shiyasa yake tsaye a Kansu don ganin sum samu tarbiya mai kyau…………………..kai wallahi magaji sai kuma gobe????????????
Karku manta comment nakeso in naga babu comment nasani book din bai samu karbuwa ba sai na ajiye shi kawai na maku wani tunda farincikiku shine namu????????