BuhariLabarai

Ina Mai Neman Gafarar Ku Kan Matsalar Wahalan Man Fetur

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya nemi gafarar ’yan Najeriya kan yadda karancin man fetur din da aka jima ana fama da shi ya jefa rayuwarsu.

A cikin wata sanarwa da kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Laraba, Buhari ya ce tsawon shekara bakwai ke nan gwamnatinsa na shawo kan matsalar, in ban da a bana da lamarin ke neman ya ci tura.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatinmu na sane da yadda wahalar man nan ta jefa rayuwar ’yan Najeriya da dama cikin kunci, amma tallafi na tafe nan ba da jimawa ba. Ina baku hakuri a kan haka.

“Muna aiki ba dare ba rana wajen shawo kan matsalar. Akwai ma wani yunkuri da muka fara yi a farkon wannan watan don magance ta.

“Muna aiki tare da Kungiyar Manyan Dillalan Mai ta Kasa (MOMAN) da takwararta ta IPMAN, kuma da alama kwalliya na biyan kudin sabulu.

“An fara samun isasshen mai a wasu jihohin, kuma tuni layi ya fara raguwa a gidajen mai. Ku sa ran ganin hakan a dukkan ragowar jihohin nan da ’yan kwanaki masu zuwa,” inji shi.

Shugaban ya kuma ce ya samu bayanin yadda wasu ’yan kasuwar da masu gidajen mai ke kokarin yin zagon kasa ga yunkurin.

Buhari ya ce tuni ya umarci Ma’aikatar Man Fetur ta Kasa da kamfanin NNPC da sauran hukumomi da su dauki tsattsauran mataki a kan duk mai hannu a lamarin.

Game da batun matsalar wutar lantarki kuwa, Shugaban ya ce ita ma saura kiris a shawo kanta.

Daga Aminiya

 

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button